Ticker

6/recent/ticker-posts

Nayi Mafarki Hakora Na Suna Zubewa

TAMBAYA (18)

Assalam Alaikum Warahmatullah. Fatan malam yana lpy. Dan Allah tambayane nake da shi akan fassaran mafarki. 1-yawan mafarkin da mutum zaiyi hakoransan suna zuba haka kawai. 2-mafarkin ruwa

AMSA:

Shahararren malamin fassarar mafarkinnan Imam Muhammad Ibn Sireen (Tabi'i kuma dalibin Imam Malik) yayi bayani daki-daki a cikin littafinsa mai suna "Qamus din fassarar mafarki" (Dictionary of Dreams) ya ce: Mafarkin zubewar haqora haka kawai yana nufin biyan bashi, idan haqori daya ne ya fita hakan na nufin mutum daya yana binki bashi, idan dayawane kuma gwargwadon yawansu a zubewa gwargwadon adadin mutanen da suke binki bashi

Idan haqoran mutum na gaba suka zube ba tareda yaji zafi ba ko kuma jini ya fita ba hakan na nufin mutum zai rasa kadara ko kuma wani abu a cikin abin da ya mallaka

Tattaro haqoran da suka zube a mafarki yana nufin mutum yana cikin danasanin aikata wani abu, idan mutum mai addini ya rasa haqoransa a mafarki hakan yana nufin yana sakaci da addininsa sai ya dage da ibada kamar yawaita nafilifili, anso ya fara da azumin litinin da alhamis, azumin 13,14 da 15 ko kuma ya sha yau ya azumci gobe

Zubewar haqora a kasa cin abinci a mafarki na nufin talauci, idan mutum yayi mafarki haqoransa sun zube akan cinyarsa, hakan na nufin zai samu yalwatuwar iyali dayawa sannan kuma idan yayi mafarkin matarsa tana dauke da ciki sai ya cire haqorinsa batareda yaji wahala ko kuma zafi ba hakan na nufin matarsa zata samu karuwar da namiji

Sai kuma mafarki na biyu, wato mafarkin ruwa, fassararsa tanada matuqar tsayi amman a taqaice ga wasu daga ciki:

Ganin ruwa a mafarki na nufin, farin cikin rayuwa, kudi, daukaka, yalwar kasuwanci, samun ribar kasuwa, ko kuma aure. Idan mutum yaga ruwa garai-garai a mafarki hakan na nufin raguwar farashin kayan masarufi, idan mutum yayi mafarki yana tauna ruwa hakan na nufin wahala a cikin harkar kasuwanci, shan ruwa da yawa a mafarki sabanin yanda mutum ya saba sha a farke na nufin tsawon rai. Idan glass daya na ruwa bai kosar da mutum ba a mafarki hakan na nufin rashin samun jituwa tsakanin mata da miji

SHARHI:

Na farkodai, idan na fahimta mafarkinki yanada alaqa da (maybe ke yar kasuwace ko kuma wani dan kasuwa yana binki bashi) don haka a shawarce sai ki biya wannan bashin da yake a kanki sannan kuma kada ki manta da rubuta wasiyya saboda halin rayuwa

Idan mutum yaci bashi da niyyar biya to in sha Allahu, Allah zai bashi ikon ya biya idan ma mutun ya rasu bai biyaba to Allah yakan aika Mala'ika Siddiqun (AS) yayiwa yan uwan wanda ake bi bashin bayanin halin da mamacin yake ciki silar rashin biyan bashin wanda a karshe idan aka bincika za a gano tabbas fa wane yana bin mamacin kudi kafin ya rasu wani lokacinma har adadin kudin

Idan kuma mutum yana cin bashi batareda niyyar biya ba to wannan ko saidai abin da ya gani a rayuwar barzahu (kabari) domin kuwa Allah baya yafe hakkin dake tsakanin bawa da bawa sannan kuma a ranar lahira za a biya da wanda yake binsa bashin bawai da kudi ba a'a da sallah ko azumi ko hajji ko zakkarsa

Don haka a shawarce, yake yar uwa, ki daure ki sauke nauyin da yake kanki sannan kuma ki dinga rubuta wasiyya ki sanarda iyalanki ta yanda zasu biya miki da kansu batareda ansha wata wahala ba

A karshe kuma kada a manta tasirin addu'a domin kuwa tana canza kaddara kamar yanda sahihin hadisi ya tabbatar

An karbo daga Abdullahi Ibn amr Ibn al-As (RA), Annabi SAW ya ce: "Babu abin da yake canza kaddara sai addu'a"

(Sahihul Bukhari babin Addu'a hadisi mai lambata 3439)

Don haka ko da Allah ya kaddara wata musiba zata fado gareki silar wadancan mafarkan to saiki tarbi wannan musiba da addu'a, in sha Allahu sai kiga Allah cikin ikonSa ya kareki da kariyarSa

Wallahu ta'ala a'alam

MAI TAMBAYA: Masha Allahu ngd sosai. Allah saka da alkhairi

Amma Malam bana kasuwanci hasalima ni dalibace. Dan ganeda zubewar hakuri kuma a mafarkin ba zabi ba komai kuma wlh Malam ni bana karban bashi hasalima tsoronta nakeji Sai de akwai wani lokacin da najeyin katin shaidan dan kasa muka sayi abu aka hada mu canji hamsin zan basu naira talatin sbd ba canji to wlh bansan lokacinda suka tafiba kuma har yau abin yana raina na rasa yadda zanyi wlh Bayaga wannan to wlh bazance ga wanda yake bina bashiba a duniyar nan wlh idan nasan banida kudima bana fara daukan kayan mutane

Kawai zanyi mafarkin hakorina suna zuwa ba zafi ba jini ba komai

USMANNOOR: Fassarar dai ta fito karara. Shi wancan bashinda ake binki na N30 ai haqqinsu ne tunda baki biyasu ba. La'akarida kin nemesu kin rasa to kamata yayi kiyi musu sadaka da N30 din tareda roqon Allah ya saka a mizaninsu. Wannan shine fassarar mafarkin kam. Ya fito sosai tunda ai kina iya tuno cewar akwai hakkin wasu akanki domin kuwa wannan N30 saita iya hanaki jin dadin rayuwar kabari. Kuma ki godewa Allah da yazamana bai saka miki sha'awar karbar bashin mutane ba, kina yin sadakar N30 din tasu ga mabuqaci zakiji wata nutsuwa ta sauka akanki silar sauke nauyin hakkin can

Allah ya bada ikon aiwatarwa

Amsawa:

Usman D. Mato (Usmannoor_As-salafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments