Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Bayyana Ko Ɓoye Karatu A Sallolin Nafila

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Shin nafilar bayan sallar magariba bayyana karatu ake, domin naga wadansu suna bayyana karatu wadansu kuma sunayi a ɓoye, wanne yafi inganci acikinsu.?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

الحمد لله

Abun da yake asali shi ne bayyana karatu a sallolin nafilfilin da akeyinsu da dare, da kuma ɓoye karatu acikin waɗanda akeyinsu da rana.

Imamun nawawy Rahimahullah ya ce: sallar idi data rokon ruwa da sallar tarawihi da sallar kisfewar wata sunnah ne bayyana karatu acikinsu babu saɓani.

Nafilfilin rana sunnah shi ne ɓoye karatu acikinsu babu saɓani.

Nafilolin dare wanda ba sallar tarawihi ba ana bayyana karatu acikinsu, Alqazy da mai littafin attahzeeb ya ce: Mutum zaiyi tsaka tsakiya acikinsu wataran ya ɓoye karatun wataran kuma ya bayyana.

Amma sunnoni jerarru da'ake yinsu bayan sallolin farillah ko kafinsu a mazhabarmu shi ne dukkansu za a ɓoye karatunsu ne, alqazi ya nakalto acikin sharhi muslim daka wasu cikin salaf cewa ana bayyana karatun nafilar sallar asubah raka'atanul fajar kenan, daka jamhur ɗin malamai shi ne ɓoye karatunsu kamar mazhabarmu. sai imamun nawawi ya ambaci hadisan da sukazo a kan haka Almajmu'u (3/357).

Yazo acikin kasshaful qina'a (1/441) Makaruhi ne mai sallah ya bayyana karatu acikin nafilar rana inba asallar kisfewar rana ba ko ta rokon ruwa ba, acikin sallar nafilar dare kuma ya kiyaye wanda suke tare da shi ko yake kusa dashi, ko wanda zai cutu da bayyana karatunsa sai ya ɓoye, idan kuma akwai wanda zai amfana da bayyanawarsa sai ya bayyana.

Rana ana nufin daka hudowar rana ba daka hudowar alfijir ba, dare ana nufin daka faduwarta harzuwa sake hudowarta.

Babu saɓani sunnah shi ne ɓoye karatu asallolin rana,

Idan mai sallah ya bayyana karatu a sallar rana saboda hakan zaifi sashi tsoran Allah da kuma tunatar dashi, babu laifi akansa, tare dacewa sunnah dakuma abun da yafi shi ne ɓõyewa.

Shaik bin baz Rahimahullah ya ce: " Idan mutum yana sallah shi kaɗai an shar'anta masa yayi abun da yafi masa ransa na bayyana karatu ko ɓõyewa cikin  dare idan  asallar nafila ne, idan  bayyana karatunsa ba zai cutar da kowa ba, idan akwai wani akusa da shi wanda zai cutu da bayyanawar ko mai bacci ko wasu masu sallar daban ko masu karatu an shar'anta masa ɓoye da sautinsa.

Amma sallar nafilar rana kamar sallar duha,  da nafilolin da'ake akowacce sallah da sallar azahar da la'asar sunnah shi ne ɓoye karatu.

Ya halatta wani lokacin liman yabayyana wasu ayoyi a sallar azahar da la'asar saboda hadisin Abu qatada ya ce manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam yakasance yana jiyar damu wasu ayoyi asallar azahar da la'asar.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/BSA30hdZD7V3WSJF8WVwUj

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments