Ticker

6/recent/ticker-posts

Tasirin Musulunci a kan auren Hausawa

Takarda da aka gabatar a taron ƙara wa juna ilimi na Ɗalibai masu karatun Digiri na Uku (PhD) a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato, Satumba  04-09, 2023

Daga

Haruna Umar Maikwari

+2347031280554

Tsakure

Rarrabe tsakanin al’adun aure da addinin Musulunci ba abu ne mai sauƙi ba. Idan aka lura da irin tasirin da addinin Musulunci ya yi a kusan dukkan ɓangarorin rayuwa, za a ga cewa wasu abubuwa da suka shafi aure sun sauya daga abinda al’ada ta zo da shi ya zuwa ga abinda addinin Musulunci ya zo da shi. Musulunci ya zo da dukkan tsare-tsare, kuma rashin bin wannan tsari na Musulunci, kan iya barazana ga auren ma’aurata da kuma rayuwarsu ta gaba ɗaya. Wannan jinga na da manufar: bayyana auren Hausawa, fito da tasirin Musulunci a kan auren Hausawa da haskaka alfanun Musuluncin a cikin auren Hausawa.hanyar da aka bi wajen aiwatar da wannan bincike ta haɗa da hira da wasu mutane da karance-karancen littattafai da kundayen binjcike. An ɗora wannan jingar a kan ra’in Sauyin al’adu. Ingar ta fito da irin tasirin da Musulunci ya yi a wasu al’adun Hausawa na aure, tun daga kore wasu, sauya wasu, da kuma samar da wasu al’adun.

1.0 Gabatarwa

Al’ada aba ce da ta shafi dukkan ɓangarorin rayuwar al’umma. Wannan ne ya sa kalmar ‘al’ada’ ta daɗe tana jan ra’ayin masana da manazarta da dama. Asalin kalmar al’ada ba Bahaushiya ba ce aro ta aka yi. Kuma an are ta daga harshen Larabci. Tana nufin abin da aka saba yi a Larabce. Duk da cewa akwai kininta a harshen Hausa.[1] Akwai rubuce-rubucen ilimi da bincike-bincike da aka gudanar a matakan ilimi daban-daban game da al’adun Hausawa. Masana da manazarta sun yi ƙoƙarin ba da maanar wannan kalma. A cewar Ibrahim (1982:iii) “al’ada” tana nufin: “abubuwan da mutum ya saba yi a cikin rayuwarsa ta duniya”. Ɗangambo, (1984:5) cewa ya yi: “Al’ada ita ce sababbiyar hanyar gudanar da rayuwa, wadda akasarin jama’a na cikin al’umma suka amince da ita.” Bunza, (2006:7) na da irin wannan ra’ayi inda yake cewa: “Al’ada tana nufin dukkanin rayuwar ɗan Adam ce tun daga haihuwarsa har zuwa kabarinsa.” Idan aka duba waɗannan ma’anoni da ma wasu da dama makamantansu, za a tarar da cewa, al’ada dai na nufin hanyar rayuwar al’umma ta gaba ɗaya. Wannan kuwa ya haɗa da dukkan matakan rayuwa da zamantakewa da tattalin arziki da kiyon lafiya da dukkannin abin da ya shafi rayuwar al’umma.

A ɓangare guda kuwa, aure na nufin zaman tare tsakanin mata da miji bisa yardar juna da amincewar junansu. Aure na daga cikin manyan matakan rayuwar wanda yake ƙunshe da aladu baya ga shi kansa. Al’adu su ne suke yin jagorancin tafiyar da shi a zamani dauri.

Musulunci kuwa, addini ne na Allah (SWA). Musulunci hanya ce ta gudanar da rayuwa cikin tsari da Allah ya tsara, annabi Muhammadu (SAW) ya koyar ga al’ummar duniya. Dun irin tanadin da al’ada ta yi wa al’umma, addini ya zo da kwatankwacinsa. Kuma tsarin addinin ya fi sauƙi da daɗin bi. Wannan ya sa al’ummu daban daban da kira da shiriya suka iskar suka karɓe shi hannu biyu-biyu. Karɓan Musulunicin ya taimaka wajen tasirin da Musulunci ya yi ga al’adun da aka gada kaka da kakanni. Wannan jinga na da manufar: bayyana auren Hausawa, fito da tasirin Musulunci a kan auren Hausawa da haskaka alfanun Musuluncin a cikin auren Hausawa.

1.2 Hanyar Gudanar da Bincike (Jinga)  

Wannan jiga za ta bi hanyoyin tattaunawa da wasu masana a kan al’adun Hausawa. Haka kuma za a bi hanyar karance-karancen litattafan da suka yi magana a kan aure da addinin musulunci domin ganin irin tasirin da addinin Musulunci ya yi ga auren Hausawa. Haka kuma an bi hanyar karance-karancen mujallu da maƙalu da kundaye domin samun wani abin dogaro da za a kafa hujja da shi dangane da wannan jinga.

1.3 Ra’in Bincike (Jinga)

Jingar ta yi amfani da ra’in “Mazhabar Sauyin Al’adu”. Gusau(2015, p. 51) ya bayyana wannan Mazhaba da cewa; “tana kokawa ne da yadda tasirin baƙin aladu na zamananci ko birnanci yake ƙoƙarin mamaye aladun gida na gargajiya masu asali.” Abin nufi dai a nan shi ne al’ada ta yi tsari ga rayuwar al’umma. Addinin Musulunci ya zo da nasa tsarin yadda rayuwa take tafiya cikin tsari. Dukkan Hausawan da suka karɓi Musulunci, sun ɗauki wannan tsari na Musulunci. Don haka a wasu al’adu an samu sauyi a madadin kore al’adun. Wasu kuma korewa aka yi. yayin da wasu kuma aka mamaye su.

1.4 Bitar Ma’anar Aure Daga Masana

Aure alaƙa ce ta halaccin zama tsakanin miji da mata, ana yin sa ne domin shi aure sunna ce ta Annabi Muhammada Rasulullahi (S.A.W) domin tsarkaka zuri’a. Aure muhimmin abu ne ga al’umma saboda haka akwai hanyoyi da matakai na tabbatar da shi. Mataki na farko shi ne neman aure. Haka kuma akwai wasu matakai na wali, da dukiyar aure da sauransu.

Rambo, (2013), ya ruwaito, Burgress da Locke, (1953) na cewa “Aure zamantakewa ce ta amincewar mutum ɗaya ko fiye da ɗaya ko mace ɗaya ko fiye da ɗaya mai dangantakar mata da miji”. Rauf, (1977:78) ya bayyana aure da: “Ƙulla  yarjejeniya da za ta haifar da halaccin saduwa da mace da samun zuri’a. Kuma wani ɓangare ne na mu’amala da ibada”.

“Auren gargajiya na Hausawa ya danganci zaman tare a tsakanin namiji da mace a bisa yardar juna ko amincewar dangi ta hanyar wasu ƙa’idoji na al’ada ko na addini.” Ibrahim, (1985:i). Aure muhimmin al’amari ne ba kawai a wurin al’ummar Hausawa, har ga sauran al’ummomin duniya gaba ɗaya.[2]

Alhassan, da Wasu (1982:8), Suna ganin “ Aure a matsayin alaƘa ta halaccin zama tare tsakanin namiji da mace. Ana kuma yin sa ne saboda abin da aka haifa ya sami alsali da mutunci, da kiwon iyaye. Haka nan aure shi ne maganin zina da ‘ya’ya marasa iyaye, kuma mafi yawanci yaro yakan fara neman aure ne, idan ya kai shekarun balaga.” Ibrahim, (1982:22-23) na cwa, “ Aure shi ne zaman tare tsakanin mace da namiji a bisa yardar juna da amincewar dangi ta hanyar wasu ƙaidojin aladu ko addini. Saulawa (1986:1) cewa ya yi, “ Aure wani abu ne wanda ake yi tsakanin mace da namiji bisa ga amincewar junansu a haɗa su tare ta hanyar ƙulla dangantaka a tsakaninsu da niyyar zaman tare na mata da miji, domin yaɗa al’umma da kuma yawaita zuri’a.” A Ƙamusun Hausa na CNHN, (2006:22) ya kawo bayanin aure kamar haka, “Dangantaka tsakanin namiji da mace ta hanyar shari’a.”

A gudummuwa irin wannan za a iya cewa: “Aure na nufin haɗuwa ko ratsawar wani abu a cikin wani abu, mutum ko dabba ko tsiri da makamantansu. Domin samun albarkar da ke tattare da abubuwan da suka haɗu ko suka ratsa juna”.

Idan kuma aka kalli ma’anar a addinance za a iya cewa, “Aure wata hanya ce ta baiwa namiji da macce damar zama tare da saduwa ta hanyar jin daɗi da mutunta junansu. Ita wannan hanya ko yarjejeniya ana gabatar da ita ne a gaban shaidu tare da yanka sadaki, kuma yadda addinin musulunci ya ƙayyade a kuma zartar da shi ta hanyar da sunnar Manzon Allah (SAW) ta tanada.

Haka kuma Allah Maɗaukakin Sarki ya ambaci aure a cikin littafinSa Mai Tsarki wato Alƙur’ani cewa, (Ku auri abin da ya fi maku daɗi daga mata biyu-biyu ko uku-uku ko huɗu-huɗu, amma idan ba za ku iya adalci ba ku auri ɗaya)[3]. Sannan kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce, (Mafi yawancin aure mai albarka shi ne, auren da yake da ƙarancin sadaki kuma babu riya a cikinsa.)[4]

Shi kuwa Bergery, (1934) da Roxana, (1997) da Abraham, (1962) dukkansu ba su bayar da ma’ana wadda za a gane aure ba. Sai dai sun yi maimaicin kalmar sun saka a cikin jimla wasu kuma sun yi fassara daga Hausa zuwa Ingilishi. A ƙamusun Jami’ar Bayero kuwa, an bayyana cewa, “Aure dangantaka ce tsakanin namiji da mace ta hanyar shari’a, ko mace da namijin tattabara, ko haɗa wani tsiro da wani don samun ingantaccen iri”. CNHN, (2006:22). “Aure wani tsari ne wanda Allah ya shirya wa mutum musulmi, wanda ya ba shi damar ya nemi matar da ta dace domin su zauna tare a matsayin miji da mata bisa wasu sharuɗɗa da Allah ya shimfiɗa masa”. Auta, (2017:279). 

Daga ma’anonin da suka gabata za a iya cewa: “Aure hanya ce ta haɗa ko ƙulla dangantaka tsakanin mace da namiji waɗanda za su zauna tare kuma a wuri guda a matsayin mata da miji, wadda kowace irin al’ada ta duniya ta amince da ita a kan dangantaka ta din-din-din domin yawaitar al’umma da kuma ci gabanta.”

1.5 Bitar Ma’ana Aure Musulunci

Musulunci itace rayuwa da ALLAH ya shar'antawa bayinSa ta harshen Annabi Muhammadu (SAW), shi kuma ya ɗauko ta zuwa gare mu. Duk wanda ya bi ta cikin dukkan alamuransa na ibada da muamalansa to shi ne musulmi, kuma shi ne wanda ya riƙi ALLAH a matsayin Ubangijinsa kuma majiɓincin al'amuransa.[5]

Musulunci shi ne yarda da saƙon da Allah Ya aiko Annabi Muhammadu (SAW) da shi, da kuma aikata abin da saƙon ya ƙunsa daidai da karantarwar Annabi Muhamadu (SAW)[6]. Musulunci shi ne addinin gaskiya wanda babu wannan addini in ba shi ba.[7] Musulunci shi ne tsarin tafiyar da rayuwa da bautar Allah Maɗaukakin Sarki.[8] Musulunci shi ne zaman lafiya, kuɓuta daga aibubbuka.[9] Musulunci shi ne sanin ƙaidojin sharia wanda annabi Muhammadu ya zo da shi daga wajen Allah.[10] Musulunci shi ne miƙa wuya ga Allah da jawuwa gare Shi, da yi maSa ɗa’a, da tsalkake Shi da barin yi masa shirka.[11]Duk wanda ya riƙi wani addini wanda ba Musulunci ba, Allah ba zay amsa masa ba, ranar Lahira suna cikin masu hasara.[12] Haƙiƙa addini a wurin Allah shi ne Musulunci.[13] Musulunci shi ne sanin dokokin shari’a waɗanda annabi ya zo da shi tare da sharuɗɗa keɓantattu da suka danganci Sallah, Azumi Hajji, Zakka.[14]

1.6 Tasirin Musulunci a Kan Auren Hausawa

Addinin Musulunci ya yi tasiri kusan dukkan al’amurran rayuwar Hausawa waɗanda suka karɓe shi. A fannin aure Hausawa kuwa Musulunci ya yi tasiri tun daga nema, zuwa zance, baiko, shiga lalle, hidimomin buki, tarewa, da zaman aure. Akwai wasu abubuwa da yawa da ake yi waɗanda idan ba ilmi ke ga mutum ba, zai yi wuya ya iya rarrabe su. Ra’in sauyin al’ada da aka zaɓa don ɗora wannan aiki, ya tabbatar muna da cewa ana samu tasirin wasu baƙin aladu su mamaye ko su sauya wasu ko ma su kore su al’adun. Addinin Musulunci ya yi irin wannan tasiri ga al’adun Hausawa na aure. Yayin da ya sauya wasu, ya mamaye wasu ya kuma kore wasu al’adun.

1.6.1 Tasirin Musulunci a Kan Al’adun Daɓe

Daɓe dai shi ne aikin daddale ƙasan ɗaki da ma wajensa domin gusar da turɗa. Ana yin daɓe da ƙasar ɓurji da ruwa da makuba da sauran kayan haɗi.[15] Kafin zuwan Musulunci wannan lalura ta daɓe ta ta’allaƙa ne a kan amarya. Iyakar miji ya gida ɗaki, su kuma dangin amarya su ke da alhakin yin daɓe da balgen ciki da wajen ɗaki[16]. Da Musulunci ya zo sai ya zo da tsarin tanadin muhalli da gyaransa duk sun ta’allaƙa a kan miji. Yanzu da Hausawa suka karɓi Musulunci sau-da-ƙafa sai waccan aladar ta daɓe da ta ta’allaƙa a kan mata (amarya da danginta) ta koma a muhallinta na asali. Miji ne zai gyara komai, ita mata zuwa ta shiga ɗai an nata.

Akwai tattaro da ‘yan uwa da abokan arziki daga dangin amarya tare da dafe-dafen abinci, da gayyato masu aikin daɓen su zo daɓe suna yin waƙoƙinsu na arashi da batsa da sauran abubuwan da suke son su faɗa ko isar duk a wannan daɓe, duk zuwan Musulunci ya sauya waɗannan al’adun. Yanzu ma da tsarin ginin zamani ake yi, sai a ƙare komai na gyaran gida amarya da dangi ba su ma san an yi ba. Sai dai kuma idan an gama ko an tanada akan kai su su gani domin su san irin kayan ƙawar da za su saka. Muhallin shahid dai yanzu Musulunci ya dakatar da daɓe da shagulgulan da ake yi cikin yinsa.

1.6.2 Tasirin Musulunci Kan Neman Aure

Addinin Musulunci ya tsara yadda ake neman aure. Idan namiji ya ga wadda yake so da aure, yakan nemi iyayen yarinyar a ba shi dama ya nemi so ga yarinyar. Idan ya samu dama sai a tsayar da magana. Za a tanadi wali (wakili) sannan kuma za a dakatar da duk wanda ke neman yarinyar bayan shi kaɗai. Idan zai zo hira (zance) kuma, yarinyar takan zo masa tare da ‘yar rakiya. Ba za a bari su keɓanta su kaɗai ba a wani waje ɓoyayye. Musulunci ya hana zuwa tsarance kuma ya hana cire. A wancan lokaci al’ada ta yadda da zuwa tsarance domin kuwa babu wani abu na lalata a cikinsa. Zuwan Musulunci ya hana wannan al’adar duk kuwa da cewa babu wani abu mai kama da lalata a cikin wannan tarancen.

Musulunci ya tsara yadda komai ya dace ya tafi a cikin sha’anin neman aure. A yau, bin wasu al’adun ya zama wani abin ƙyama. Da wuya a iske mai neman mata ya je tsarance. Amma yana iya keɓancewa wannan kuma ba ya nuna wani abu. Kawaci da ke ga Hausawa na nuna yarda da mutum ya sa ake barin wanda ya je zance keɓancewa da wadda yake nema kar ya zargi ba a yarda da shi ba.

1.6.3 Tasirin Musulunci Cikin Shiga Shagalin Aure  

A dauri al’ada ta yadda da kafin shiga shagalin aure, a sa yarinya ta ɓoye sai a nemo tsohuwa mai sa amarya lalle. Ana kiran wannan tsohuwar da arwanka. A dauri idan za a sa amarya lalle, akan nemi ta je ta ɓoye a wani gida daban. Sai a nemi arwanka ta shiga nemanta. Ita dai arwanka, takan nemi run tulun matar da ta tsufa ba ta taɓa yin yaji (tashi) ba. Sai wannan arwankar ta ɗebi wannan ruwan a gyanɗama (gora) sai ta riƙa yawon gari unguwa-unguwa, gida-gida tana neman wannan amaryar. Kuma tana da damar shiga koina na gida idan ta shiga. Tana iya shiga har ban ɗaki ta kuma duba har cikin ɗaki har bayan gambu da ƙarƙashin gado. Ba wanda zai hana ta. Idan ba ta gani ba sai ta yi sallama da masu gidan ta fita zuwa wani gidan daban da ake tsammanin yarinyar ta je. Daman amaryar za ta iya zuwa gidan da ba a tsammanin ganinta. Wannan neman amaryar don sa mata ruwa ta shiga lalle yana iya ɗaukar makonni biyu ko fiye. Ya danganta da lokacin da aka gane amaryar. Daga ta gane ta za ta zuba mata wannan ruwan a kai ko fuska ta ce mata ga ruwan aurenki nan. Sai amaryar ta fashe da kuka, ita kuma da mutanen gidan da aka gane ta sai su ɗauki guɗa. Daga nan a kama amaryar zuwa gidan ubanta domin shiga shagulgulan aure.

Daga an je gida kuma sai arwankar ta shiga hidimar yi wa amarya wanka. Akan yi wannan wankan a tsirara, kuma a saman turmi a tsakar gida a gaban mutane dangin amarya da na mijin. Bayan wankan kuma akwai al’adar ɗaurin laɗe da ake yi wa amarya wanda abokanta ke yi. Akan yi kaɗe-kaɗe da luguden turame da kiɗan ƙwarya da shantu da dai makamantan wannan.

Wannan al’adar Musulunci ya sauya ta. Ya dakatar da wannan ɓoyon, ya kuma hana yin wankan lalle tsirara a saman turmi da kuma ɗaurin laɗe da aka saba. Haka kuma, ya zo da saka rana da gayyata da gyaran jiki ba tare da an fita cikin bainar jama’a ba. Haka kuma Musulunci ya dakatar da cuɗa ga shi kansa ango da yi wa angon ko amaryar wata al’ada da za ta bayyanar da tsiraicin wani daga cikinsu.  

1.6.4 Tasirin Musulunci Wajen Ɗaurin Auren Hausawa

Tun kafin zuwan Musulunci Hausawa na yin aure. Akan saka rana a tara mutane musamman a ranar kasuwa ko a cikin kasuwa sai a ɗaura aure. A lokacin Maguzanci, lokacin da Hausawa ba su karɓi addinin Musulunci ba. Idan za a yi ɗaurin aure, aka nemi wani tsoho ya ɗaura aure. A wajen wannan aure dai tsohon kan tara ƙasa ya ɗauki ɓota ya tara ƙasa a gaban mutane ya bugi (doki) wannan tarin ƙasar ya furta cewa Ya ɗaura auren wane da wance ya ga ɗan kaza-kazar uban da ya isa ya kwance.[17] Haka kuma wannan auren ana iya ɗaura shi a cikin kasuwa ko ƙofar gidan uban yarinya.

Da Hausawa suka karɓi Musulunci sai wannan lafazi ya sauya daga na ashar zuwa na abinda Musulunci ya zo da shi (addu’a). Haka kuma a madadin a nemi tsoho ya ɗaura sai abin ya koma sai limamai ke daura aure da malaman addinin Musulunci. Har ila yau, a madadin a ɗaura a kasuwa, sai abin ya sauya zuwa ɗaurawa a cikin masallacin dai ba ƙofar wani ba ko uban yarinya.

1.6.5 Tasirin Musulunci Ya Haifar da Walima a Shagalin Bukin Aure

A lokacin Maguzanci, idan aka yi aure akan yi shagali a ci a sha a yi kaɗe-kaɗe.[18] Da Musulunci ya bayyana ga al’ummar Hausawa, sai wannan ya sauya daga abin da aka sani a Maguzanci zuwa walima. A duk lokacin da aka yi hidamar aure, akan keɓe rana ta musamman domin yin walima. A wannan lokaci aka saka wannan walima daga jerin tsare-tsaren da ake yi na shagalin buki. Walimar aure dai ta danganta daga masu yinta. Wasu sukan gayyato malaman addini maza kuma fitattu. Wasu kuma sukan gayyato malaman wannan amaryar na Islamiyya. Wasu kuma malamai mata da suke da ilimin addinin Musulunci suke gayyata. Idan suka zo, sukan yi wa’azi da jan kunne a muhallin da aka tanada. Wasu sukan tanadi wata makaranta ta Islamiyya wasu kuma gidansu ko na danginsu.

Galibi a wannan rana ta walima, kayan da amarya ke sakawa dole akwai alkyabba. Wannan alkyabba ta samo asali ne daga suturar Larabawa. Su kuma Larabawa Bahaushe ɗaukar yake dukkansu Musulmai ne. Duk abin da Larabawa suka zo da shi Bahaushe ɗauka yake addini ne. Yanzu wannan walima ta zama wajibi cikin sha’anin auren yau. Ko da ba za a yi komai ba, akan fitar da rana da ake yin walima. Kuma galibi wannan ranar takan zama ko dai Alhamis idan za a ɗaura ranar Juma’a. Ko kuma ranar Juma’a idan za a yi auren ranar Asabar.

1.6.6 TasiriM Musulunci Wajen Ɗaukar Aure Ibada ba Sharholiya ba

Kafin zuwa Musulunci a ƙasar Hausa aure alada ce ta zama da mace ko mata a matsayin matan aure. Ana yinsa don kamala da ribar aure da makamantansu. Da addinin Musulunci ya samu ga Hausawa sai kuma aure ya tashi daga alada zuwa ibada. Tsarin Musulunci ake bi wajen aiwatar da shi. Idan aka samu matsala, matsarin Musulunci ake bi, wajen gyaransa. Tsarin Musulunci ake bi idan aka samu saɓani aka yi saki. idan za a koma, abin da Musulunci ya tsara ake amfani da shi wajen yin kome.

1.6.7 Tasirin Musulunci Cikin Kai Amarya

A rayuwar baya ta Maguzanci, akan kai amarya ta kaɗe-kaɗe da bushe-bushe da waƙe-waƙe. A kan hanyar zuwa akwai zabaya ita ke shiga gaba ta rera waƙa su kuma yan rakiya suna amsawa har a isa. Yanzu kuma da Musulunci ya zo sai aka bar gayyatar zabaya, sai dai a zo da abin hawa a ɗauki amarya a kama hanya zuwa kai ta gidan ango. Idan Musuluncin ya ƙara tasiri ma a yau shi ne wasu iyaye su ke kai yarsu da kansu. Maana uba kan ɗauki ‘yarsa ya kai ta gidan miji domin yin koyi da Sabin nan da ya kai ‘yarsa. An bayyana cewa sunna ce uba ya kai ‘yarsa gidan miji ya yi mata huɗu ba[19]. An kuma samu wasu da dama suna ɗabbaƙa wannan sunna.

1.6.8 Musulunci ya yi Tasiri Wajen Ƙayyade Yawan Mata da Za a Aura

Kafin zuwan Musulunci Bahaushe na iya auren mata fiye da huɗu. domin kuwa a wancan lokaci, wanda yake da yawan ‘ya’ya shi ne mai arziki. Domin kuwa da ‘ya’yan ne ake zuwa gona wajen aiki. Su ne ke tara abinci. Yawan ‘ya’ya kuma yana samuwa ne idan akwai mata da yawa a gida. Kenan kowace za ta haihu, kuma abin da aka haifa yakan zama jarin gida. Da musulunci ya samu a ƙasar Hausa, sai aka samu sharaɗin ƙayyade mata. Musulunci ya ƙayyade cewa dukkan Musulmi kar ya wuce mata huɗu. Musulmi kan iya auren mata biyu, uku, ko huɗu. Idan kuma ba za su iya adalci ba suna iya tsayawa ga auren guda.[20] Wannan karantarwa ta addinin Musulunci, ita ce ta sa Bahaushe yanzu ba ya auren matan da suka wuce wannan ƙaida ta mata huɗu da aka shata.

1.6.9 Tasirin Musulunci Cikin Ƙayyade Ƙarancin Sadaki

A lokacin Maguzanci, babu ƙayyade ƙarancin sadaki. Kenan komai mutum ya bayar a matsayin dukiyar aure za a amsa. Da Musulunci ya samu karɓuwa, sai ya zo da mizani (ma’auni) cewa mafi ƙarancin sadaki rubu’in dinari (rub’u Dinar) wato kwatankwacin naira dubu arba’in da takwas da ɗari tara da tamanin da biyar a yanzu. (N48,985.00).[21] Yanzu idan za a yi sadaki sai an tabbatar da cewa ya kai wannan adadi kar a saɓa wa umarnin Musulunci. Haka kuma Musuluncin ne ya zo da a rage kuɗin sadaki, sai dai kar ya kasa wannan ƙaida da aka shata.

1.6.10 Tasirin Musulunci Cikin Zamantakewar Aure

Kafin zuwan Musulunci, Hausawa al’adu suke bi sau da ƙafa. Matan Hausawa a wancan lokaci suna suna zuwa gona, sukan yi ayyukan ƙarfi domin riƙon gida. Da Musulunci ya zo sai ya zo da tsarin yadda zamantakewar aure take a shariance. Musulunci ne ya zo da yi wa mace gata cikin sha’anin aure[22]. Musulunci ya yi umarni ga maza su ciyar da matansu da suka aura. Kuma wannan ciyarwa ma tana daga cikin ginshiƙan aure.[23] Musulunci ne ya samar da gado ga mace koda tana a wani gida tana aure idan mahaifinta ya mutu tana iya gadonsa. Haka kuma idan maigidanta ya mutu, tana iya gadonsa. Idan ma ɗanta ne ya mutu, tana iya gadonsa.[24] Ko shakka babu Musulunci ya tsara duk yadda ya dace zamantakewa tsakanin ma’aurata ta kasance.

1.7 Kammalawa

Tasirin Musulunci a kan al’adun Hausawa ba bau ne da za a iya ƙayyadewa ba. Rabe tsakanin aladu da umarnin addinin Musulunci ba abu ne mai sauƙi ba. Idan mutum ba ya da ilimin addini zai yi wuya ya iya rarrabewa. Akwai auren sadaka da aka sani ana yi domin Musulunci. Yadda ake yinsa, kuma ake ɗauka Musulunci ne idan ba ilimin addinin Musulunci ke ga matum ba, sai tunaninsa ya tafi kan cewa Musulunci ne. Ciyarwa da ba da wajen kwana haƙƙi ne da ya rataya a kan namiji, amma yanzu wasu gani suke kamar alada ne. Dafa abinci da mata ke yi ganinsa ake tamkar haka addini ya tanadar. Musulunci ya yi tasiri kusan dukkan ɓangarorin rukunnan aure.

Manazarta

Abraham, R. C. (1962). Dictionary of the Hausa Language. London: Hodder Sydney.

Alhassan da Wasu (1982) Zaman Hausawa. Institute of  Education ABU, Zaria.

Argungu A.I da Sanyinnawal. (2022) “Kutsen Zamani Kan Suturar Hausawa”. Takardar da Aka Gabatar A Taron ƙara Wa Juna Sani A Tsangayar Nazarin Harsuna Ta Kwalejin Ilmi Ta Adamu Augie, Argungu.

Auta, A. L. (2017). Faɗakarwa A Rubutattun Waƙoƙin Hausa. Kano: BUK Press.

Bargery, G.P (1934). A Hausa English Dictionary & Hausa Vocabulary, London: Oxford University Press.

Burgress, and Locke, (1953). The Family, 2nd (ed): New York. American Book. Co.

Bunza, A. M. (2006) Godon Feɗe Al’ada, Lagos Tiwal Nigerian Ltd.

CNHN (2006) Ƙamusun Hausa Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya Kano: Jami’ar Bayaro.

Ɗangambo, A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa. Kano: Triumph’, Gidan Sa’adu Zungur.

Dogondaji N.B (2021) Takarda Mai Taken Farin Kan Da Musulunci Ya Sanya Wa Aure. Takardar Da Aka Gabatar a Ajin Masu Neman Digiri Na Uku a Darasin HAU: 933

Ibrahim M.S (1982) Auren Hausawa: Gargajiya da Musulunci. Publications Center.

Gusau, G. U. (2012), Bukukwan Hausawa. Gusau: Ol-Faith Publishers.

Gusau, S. M. (2015). Mazhabobin Ra’i da Turke a Adabi da Al’ada na Hausa. Kano: Century Research and Publishing Limited.

Muhammad Siddiqal Minshawi (1134AH) Karantar da Ma’amala tsakain ma’aurata. Madina: Darul fadilati Wat Tazayyin. Shafi na 16.

Rambo, R. A. (2013), “Gwagwarmayar Kamancen Neman auren Hausawa Da Na Dakarkari”. Takardar da aka gabatar a taron ƙarawa juna Sani a Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya. Jamiar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.

Rauf, M. A. (1977). Islamic View On Women and Family: New York: Cambrige Press.

Roxana, (1997) Dictionary of the Hausa Language. London: Cambrich

Saulawa I.A (1986) Yanayi da Tasirin Al’adun Aure a Ƙasar Katsina. Kundin Digiri Na Farko, Jami’ar Usmanu Danfodiyo , Sakkwato.[1] A duba Bunza (2006) Gadon Feɗe Al’ada, a shafi na XXV

[2] Ahmad Magaji ya bayyana Aure a matsayin wata yarjejeniya ce a tsakanin namiji da mace da kuma bin wasu }a’idoji da dokoki da wannan al’umma ta tanada domin samun zuri’a ta gari.

[3] Suratul Nisa’I. aya ta 4. A cikin Al}ur’ani mai girma

[4] Hadisi na 22, a cikin Zadul Muslimat. Haka kuma akwai shi a Buguyatul Muslimin, da kuma Bulugul Maram Min Adillatul ahkam.

[5] An samu a shafin ZAUREN SUNNAH DA TAMBAYOYI. Kuma an yi wannan ɗab’i a ranar 17 ga Febrairun 2016 a shafin Internet.

[6] An samu wannan bayani daga shafin Internet na Sayyada Suhaila. Ta kuma buga shi a ranar 13 ga Mayu, 2020.

[7] Tattaunawa da Malam Aminu Ibrahim Mailemu a gidansa da ke Gusau, unguwar Samaru Phese II, a ranar 15 ga Ogusta 2023 da misalin ƙarfe biyar na yamma (5:00)

[8] Hira da Malam Sanusi Mai Almajirai a gidansa da ke Samaru Bayan S.S, a ranar 15 ga Ogusta, 2023 da misalin ƙarfe 6:00 na yamma.

[9] Tattaunawa daga Dr. Abbas Abubakar Bunza. Dean School of Languages, HOD Arabic Department. A ziyarar da na kai masa a ranar 16 ga Ogusta, 2023 da misalin ƙarfe 4:30 na yamma.

[10] A cikin Durusil Awwaliyya Babul Ƙawa’idul Islam.

[11] Bayanin Imamu Nawawi a cikin Usulus Salasa.

[12] Aƙur’ani Maitsarki. A cikin suratul Ali Imran.

[13] Alƙur’ani Suratul Baƙra.

[14] Hadisin Durusul Awwaliyya, Babin ƙawa’idul Islam.

[15] Hira da Malam Ɗahiru Sankalawa, malami a Kwalejin Ilmi da ƙere-ƙere ta gwamnatin Tarayya da ke Gusau, a ofishinsa ranar 16 ga Ogusta 2023 da ƙarfe 12:00 na rana.

[16] Hira da Malama Hauwa’u a gidanta da ke Gusau Unguwar Saminaka a ranar 17 ga Ogusta 2023 da misalin ƙarfe 5:00 na yamma.

[17] Laccar ALH 308 Thougth and Believe. 2011.

[18] Laccar ALH 308 Thougth and Believe. 2011

[19] A zamanin Manzon Allah (SAW) an samu Sahabi  Sa’id Bn Musayyid ya kai ‘yarsa gidan miji domin ya kauce wa taron nan  na bidi’a da ake yi wajen kai amarya.

[20] Alƙur’ani: Suratul Nisa’i

[21] Wata sanarwa da Sarkin Musulmi Muhammadu Sa’ad ya fitar a watan Juli da ya gabata 30 ga Juli, 2023.

[22] Hadisin Durusul Awwaliyya, Babin ƙawa’idul Islam

[23] Hadisi ya zo a littafin Riyadus Salihin kan maza su riƙa ciyar da matansu, kuma alhakin ciyarwa a kan mazan yake.

[24] Allah (SWA) ya faɗa a cikin Alƙur’ani Mai Tsarki cewa mata suna gadon iyayensu da mazansu da kuma ‘ya’yansu idan sun riga su mutuwa.

Post a Comment

0 Comments