Gabatarwa (Ta Mai Asalin Waka) - Daga Tahamisin Wakakken Ka’idojin Rubutun Hausa

    Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

    About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

    Gabatarwa (Ta Mai Asalin Waƙa) 

    Godiya da kyawawan yabo su dawwama ga Allah Buwayayyen Sarki. Tsira da aminci na har abada su tabbata ga amintaccen amininSa yardajjen manzonSa Muhammadu ɗan Abdullahi (S.A.W.) da iyalan gidansa da sahabbansa da masu koyi da su.

    Ginuwa da ci gaban kowane harshe ya dogara ga tsarin sarrafa sautukansa a rubutu. Duk harshen da ba ya da tabbataccen ƙa’idojin rubutu rarrafe yake yi bai tashi tsaye ba balle ya zauna da gindinsa. Masana da ɗalibai da masu sha’awa da kishin harshen Hausa sun yi abin a zo a gani wajen raya ƙa’idojin rubutun Hausa. Ayyukansu sun taimaka ainun wajen ci gaban harshen Hausa da adabin Hausa da al’adun Hausawa. Irin gudummuwar da suka bayar ta burge ni sosai, har na ga ya dace in ci gaba da raya ta, ta yadda ɗaliban Hausa za su kiyaye ta su iya koyar da ita ga ɗalibansu. Ba don Hausawa sun ce, aikin Magaji ba ya hana na Magajiya ba da na ce, ayyukkan da suka yi sun isa a ci gaba da bitar su ana koyar da su.

    Hangen irin muhimmancin da ke ga ƙa’idojin rubutu ga harshe mai tasowa da farin jini irin Hausa ya sa na rubuta wani littafi mai suna: Hausa A Sauƙaƙe Don Makarantun Firamare (Littafi na 1 zuwa 6) wallafar Kamfanin Hudahuda, Zariya a shekarar 1990. Bayan littafin ya bazu ya kuma samu karɓuwa musamman da yake yana tafiya da waƙa a kowane babinsa, sai na ga ya kyautu in ɗan ƙara ɗaga darajarsa zuwa littafin malamai da ɗalibai duka, don haka sai na rubuta Nahawun Rubutu Jagoran Ƙa’idojin Rubutun Hausa, a shekarar 1991, wanda Tarayyar Malaman Harsunan Nijeriya suka wallafa. Gyare-gyare da shawarorin da na samu daga masana, da malamai, da ɗalibai da marubuta, ta sa na sake bitar sa na faɗaɗa shi na wallafa shi a shekarar 2002 da sunan Rubutun Hausa (Yadda Yake da Yadda Ake Yin Sa, Don Masu Koyo da Koyarwa) wallafar Maɗaba’ar IBRASH, IKKO. Tattare da irin maraba da lale da ya samu daga ɗalibai da abokan aiki, wasu shawarori suka sake biyowa baya na sake kyautata shi da gyara tuntuɓen alƙalami da kuren ɗab’i da haskaka abin da ya shige duhu. Don haka na sake fitowa da dokokin da ƙa’idojin rubutun Hausa a waƙe, domin taƙaitawa da sauƙin harda ga ɗalibai da malamai don haka na yi masa suna: Waƙƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Ba ina nufin wannan aiki ya soke ayyukan da na yi a baya ba; abin nufi a nan shi ne, wannan ya fi su taƙaituwa da tsari mai saurin kai ga muradin mabuƙaci.

    Tilas in miƙa godiya ta musamman ga malamaina da abokan aikina da ɗalibaina da masu sha’awar karance-karancen ayyukan Hausa da ke ba mu ƙarfin guiwan ci gaba da yi wa harshen Hausa aiki. Na zaɓi in yi aiki a waƙe saboda dalilai da dama kamar haka:

    i.              Waƙa ta fi taƙaita bayani da zurfafa tunanin mai koyo da nazari.

    ii.            Waƙa ta fi sauƙin kiyayewa da hardacewa ga mai koyo.

    iii.          Waƙa ita ce hanya mafi sauƙi ga koyon nahawu musamman ma Larabci da Hausa.

    iv.          Ƙungiyar Manazarta da Marubuta Waƙoƙin Hausa ta Nijeriya, ta taɓa kira ga sha’irai da su fara tunanin waƙe nahawun Hausa ta hanya mafi sauƙi. Wannan yunƙurin karɓa kiranta ne a matsayina na sha’iri.

    v.            Darusan koyon Hausa na farko da waƙe aka fara koyar da su har Hausa ta kawo a wannan lokaci na tudun-mun-tsira. A nan, zan girgiza wa Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari shugban Nijeriya Jamhuriyya ta biyu, da ya fara koyar da darusan Hausa cikin waƙa.

    vi.          Haka kuma ganin irin namijin ƙoƙarin da Farfesa Mu’azu Sani Zariya ya yi na waƙe nahawun Hausa a cikin Alfiyyarsa ya burge ni. Ashe masu cewa, ba a iya koyar da wasu darusan harshe na Hausa cikin Hausa, Hausar ce ba su fahimta ba, domin ga Shaihin Masani Mu’azu Sani ya fito a waƙe yana musanta su. Don haka, wannan yunƙurin tukuici ne ga aikin shaihin masani Mu’azu.

    vii.        Hanya mafi sauƙi ta koyar da yaro ya tsaya ya fahimci abin da ake son ya fahimta cikin sauƙi ita ce waƙa. Da fatar Allah ya yi mana jagora. Amin!

     

    Ina roƙon Allah ya sanya wannan aikin ya zama mai amfani ga harshen Hausa da masu koyar da Hausa tun daga makarantunmu na Firamare har ya zuwa Jami’o’inmu. Zan yi farin ciki idan na samu wanda zai yi wa wannan waƙa tahamisi, domin ƙara faɗaɗa bayani.

    Na gode.

    Farfesa Aliyu Muhammad Bunza, 2004
    B.A., M.A., Ph. D., Dip. Arb., Dip. Lw., Cert. Frch.,
    (Bunza, (2004: X)

             

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.