Ticker

6/recent/ticker-posts

Bushewa Gaba Yayin Saduwa

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamualaikum malam muna maka fatan alkhairi Dan Allah Malam meye yakesa mace bushewa a lokacin da take mu'amala da mijinta bayan lokacin da suka fara ba haka bane sannan malam me yake saurin kara ruwan maniyyi  kuma malam Ina fitar da iska yayin saduwa malam a taimaka yadda ka saba taimako Allah ya kara girma ngd.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatu

To abin da yake sa bushewa idan ana saduwa rashin wadatacciya ni'ima ne indai ana tsaka da saduwa ne kike Bushewa, Amma indai kafin saduwa ne toh matsalar sanyi ne ko rashin wasa na motsa sha'awa, amma wasu kuma jumawa ana gurzarsune yake sawa ruwan yake qafewa musamman idan namijin gwarzo ne, amma ba matsala bane, abin da zakiyi shine kisamu magani masu kyau na qara ni'ima, sai yawan shan kayan marmari da kayan ganye sune wanda zasu taimaka miki sosai wajen tabbata ciyar ni'ima.

Sanann kidinga samu kankana ki ferayeta kamar kabewa sai ki yayyyanka ki sata a blender ki markadeta sai ki saka garin kaninfari kamar cokali 1 bayan kin markada sai qara zuba madararki gwangwani 1 kamar peak, luna ko wacce kike da Iko, sai ki qara markadawa su hade gaba ɗaya, Sai ki samu mazubi mai kyau ki juya ki ajjiye a firji kidinga sha wanan zai sakar miki ni'ima kamar fanfo sai kin gaji da zuba.

Sanan abin da zai qara yawan ruwan maniyyi shine ki samu yayan kabewa ki dake kidinga shansa da zuma ko ki markada dabino da madara kina sha duk suna bada wadattacen ruwan maniyyi ga mata da maza

Matsalar fitan iska yayin ya danganta da yanayin kwanciya da kukeyi musanmam ana samun fitar iska wajen saduwa ta baya domin iska na samin shiga da fita , wani lokacin kuma budewa ga mace na saka fitar iska ta gabanta yayin saduwa, wani lokacin kuma gaskiya ba matsala bane domin indai ana saduwa a wajen da akwai iskar fanka takan sa iska na shiga da fita wajen zurawa da cirewa sai adinga jin iska na fita wannan ba matsala, amma ga magani a jarrrraba in Shã Allah Zaki dace.

Zaki nemi kayan hadi kamar haka;

Ganyen magarya sassaqen danya,Yayan hulba ,Gishiri. waɗannan kayan hadin sai ki haɗesu guri guda ki tafasa  bayan kin sauke ki zuba gishiri kina zama a cikin ruwa na tsawon minti goma Kuma ya zama ruwan da kike tsarki da shi Amma ko yaushe ya zama da dumi.

Allah ta'ala yasa mudace

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Fc3hX6HoDt65aKhhKOiDpX

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments