"Kashi ɗaya, Audu Kila
Sadauki Audu Kila
Mai jin maganar Usaini
Ya ji tsoron Audu Kila
In ya ƙi ya kwan ƙiyama.
Da ganin Kila a jeji
Kai za ka tsaya ya hau ka
In dai ba tsautsayi ba?"
–Sarki Usaini ɗan Mai kotso
Wannan shi ne tsohon ɗan damben ɓangaren Kudu, Audu Kila (wanda ya ba kyamara baya) tare da abokin karawarsa Marigayi Mamman ɗan Sanyinna (Rabagardama). Allah ya gafarta musu baki ɗaya.
Daga:
Zauren Makaɗa da Mawaƙa
0 Comments
Post your comment or ask a question.