Ticker

6/recent/ticker-posts

Alhaji Nuhu Ouagadougou

Alhaji Nuhu Ouagadougou

Allahu Akbar!!! Allah SWT ya yi wa wannan Bawan Allah, Alhaji Nuhu Ouagadougou, Jamhuriyar Burkina Faso rasuwa ranar Lahadi 10/09/2023 sanadiyar rashin lafiya. Mai shekaru kimanin 87, Alhaji Nuhu Attajiri ne da asalin iyayen sa mutanen Jihar Kano ne da fatauci ya kaisu Ƙasar Burkina Faso fiye da shekaru 150 da suka wuce, Allah ya yi zaman su a can har suka haife shi a Ƙasar. Mai aikin Tawali'u da Jink'ai ne, shi ne ya gina wani katafaren Masallacin Juma'a a Birnin na Ouagadougou a shekarar 1979 ya miƙa shi zuwa ga Al'ummar Hausawa da sauran Ƙabilu Musulmai dake zaune a Ƙasar a matsayin tasa gudunmuwa wajen ɗaukaka Addinin Musulunci. Ya zuwa yanzu wannan Masallacin ne suke amfani dashi. Ga hoton Masallacin anan ƙasa 👇👇👇. Allah jiƙan sa da rahama, amin. 🤲🏾🤲🏾🤲🏾

Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
Ɗanmadamin Birnin Magaji
Imel: birninbagaji4040@gmail.com
Lambar Waya: 08149388452, 08027484815 


Post a Comment

0 Comments