Hukuncin Janabar Wanda Ta Yi Inzali Ta Hanyar Haram

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum warahmatullah. Malam barka da warhaka, Malam ina da tambaya kamar haka: WAI DOLE NE IDAN AKA SAMU MATSALA NAMIJI WANDA BA MUHARRAMIN MACE BA YA TAƁA TA SAI TA YI WANKA KOKO?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumus Salamu wa Rahmatullah. Irin wannan aiki haramun ne, mu ji tsoron Allah a cikin dukkan al'amuranmu, kuma mu guji duk wani yanayi da zai sa mu ƙaɗaita da wanda ba muharramunmu ba, saboda hadisin da Bukhariy ya ruwaito daga Abdullahi ɗan Abbas, Annabi ya ce: "Kada wani mutum ya keɓanta da wata mace face sai da muharraminta". Bukhariy 5233.

    Ƴar uwa lallai babu bambanci a tsakanin mace ko namijin da suka yi inzali (fitar da maniyyi) ta hanyar haram ta fuskar wajabcin yin wankan janaba. Inda suka bambanta shi ne, mutumin da ya fitar da maniyyi ta hanyar halas, ana sa ran zai sami ladar yin wankan janaba, amma wanda ya yi wanka ta dalilin janaba ta hanyar haram, wannan ya dai yi tsarki kawai, saboda ba ta hanyar halas janabar ta same shi ba, kuma wajibi ne ya yi wannan tsarkin saboda samun damar ci gaba da ibada.

    Allah ne mafi sani.

    Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

    Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/FBuwMyVjc2sGOEGLm0W7ed

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.