Ticker

6/recent/ticker-posts

Tsarin Ɗan Waƙa

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

Tsarin Ɗan Waƙa

A tsarin ɗiyan waƙar bara ba a samun sauka kamar yadda yake a wasu waƙoƙi. Wato kowane ɗan waƙar bara hawa kawai ake samu(furucin jagora) sai kuma amshi ya biyo. Misali:

Jagora: Lansika, inna lansika.

 Amshi: Kulle.

 Jagora: Mata dangin Fatima.

 Amshi: Kulle.

 Jagora : Ku taru ku bamu na Annabi.

 Amshi: Kulle.

 Jagora: Ku taru ku bamu na.

 Amshi: Kulle.

 Ja gora: Kowab ba mu na Annabi.

 Amshi: Kulle.

 Ja gora: Alla na gode mashi.

 Amshi: Kulle.

(Mata Dangin Fatsima)

Idan aka lura da tsarin ɗiyan waƙar da suka gabata sai a ga kowane ɗa ja gora ne kawai ke furta shi sai Amshi su furta amshin waƙar ba tare da ƙara wani furuci ba face amshin. Wannan shi ya nuna waƙoƙin bara ba su da sauka wajen rera su, hawa kawai ake samu.


Post a Comment

0 Comments