Ticker

6/recent/ticker-posts

Ya Sake Ta Saki-Uku Alhalin Tana Haila

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Miji ne ya saki matarsa alhali tana haila har saki uku, ba laifin-tsaye ba na-zaune. To yanzu idan ta gama wanka za a sanya shi cikin idda ne, ko sai ta ƙara uku?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh

Saki uku cikin kalma guda ko a mazauni guda malamai sun sha bamban a kan hukuncinsa. A lokacin da waɗansu suke ganin cewa bai auku ba, waɗansu kuma suna ganin cewa ya auku ne a matsayin saki uku, wanda kuma babu daman yin kome har sai ta auri wani mijin da ba shi ba. Amma maganar da muka amince da ita saboda ingancinta ta fuskar dalilai ita ce: Saki uku a cikin kalma guda yana aukuwa a matsayin saki guda ne kawai, wanda kuma yana iya yin kome kafin ta gama idda.

Sannan kodayake saki a cikin haila sakin bidi’a ne a wurin malamai, sai dai duk da haka ya auku, a maganar da ta fi ƙarfi a wurin malamai. Amma yadda gyaran ya ke shi ne: Ya dawo da ita, ta gama wannan hailar da take yi, ta sake yin wata. Idan ta gama, watau ta yi tsarki daga haila ta biyu, sai ya sake ta tun kafin ya kusance ta in ya so, a matsayin saki na biyu, ko kuma ya cigaba da zama da ita da sauran igiyar aure biyu. Haka ya zo a cikin mashahuriyar ƙissar Ibn Umar (Radiyal Laahu Anhumaa).

Watau, ba za ta fara maganar idda ba sai a bayan ya yi mata saki na Sunnah.

 WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaahi Assalafiy

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/EbkKRXdFzNu4F8aƘZbZ1Vx

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments