Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Matar Da Ta Zubar Da Ciki Za tayi Kaffara Kamar Wanda Yayi Kisan Kai?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum malam jinjina, fatan alkhairi da kuma addu'ar cikawa da imani su tabbata agareka tare da iyalanka, iyaye, malumanka da kuma daliban wannan zaure mai albarka. Malam tambayoyi nake dasu kamar haka. Menene hukuncin matar da tazubda ciki (juna biyu) kuma shin zatayi kaffara kamar wanda yayi kisan kai? Kuma idan mijinta yasani kokuma sun hada kai tare wajen zubda cikin shima zaiyi kaffara?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumus salam wa rahmatullah wa barakatuh.

Zubar da ciki don tsoron talauci yana daga cikin manyan zunubai domin shima kisan kai ne. In dai cikin yakai wata huɗu zuwa sama. Idan cikin yakai wata huɗu to sannan an riga an busa masa rai. Idan mace ta zubar dashi da gangan, sai ta biya diyyah zuwa ga Waliyyan jaririn (wato dangin Ubansa).

Diyyar jariri shi ne kwatankwacin Rakuma guda biyar. Wato Ushurin diyyar Mace kenan. Kuma bayan haka zata 'yantar da Kuyanga guda, idan battta da kuyangar sai tayi azumi Sittin amatsayin kaffara. Mijinta da duk wanda suke da hannu cikin kashe jaririn duk zasu hadu su biya diyyar. Kuma kowannensu sai ya 'Yanta Kunyanga ko kuma yayi azumi Sittin. Hujjah anan ita ce Hadisin nan na 6910 acikin Sahihul Bukhariy, kuma na 1681 acikin Sahihu Muslim. Duk sun ruwaito Hukuncin da Manzon Allah ya yanke ma matar data kwada ma wata Mai juna biyu dutse wanda yayi sanadiyyar mutuwarta da kuma jaririnta.

Amma idan cikin bai kai wata huɗu da samuwa ba, To babu diyya ko kaffara amma duk da haka dai Zunubi ne mai girma. Don Ƙarin bayani aduba cikin MATALIBU ULIN NUHAA (juzu'i na 6 shafi na 50).

Allah ne mafi sani

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/CfDLSdXaGD00Wpxdfy2ofp

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments