𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum. Dan Allah ina son in san hukunci
game da shafa a kan huffi ko safa, idan mutum ya yi alwala kuma ya saka safa to
idan har fitsari ya kama shi, shin idan ya je ya yi, shin idan har zai yi
alwala sai ya sake cire safar ko kuma zai yi shafa a kanta? Na gode.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Shafa a kan khuffi ko safa sunnah ce ba farilla
ba. Ya halasta idan mutum ya saka khuffinsa ko safarsa a lokacin da yake da
tsarki, yayin da ya zo yin alwala ba sai ya cire khuffin ko safar ba, kawai sai
ya yi shafa a kansu.
Haka nan idan alwalar mutum ta karye akwai khuffi
ko safa a ƙafarsa,
idan ya yi nufin sake yin alwala ba dole sai ya cire su ba, kawai sai ya yi
shafa a kansu, dalilai da yawa sun zo a kan haka a hadisan Annabi ﷺ ingantattu, daga ciki akwai hadisin da
Sahabin Annabi ﷺ
Almugeeratu ɗan
Shu'uba Allah ya ƙara
masa yarda ya ruwaito, a inda yake cewa:
“Na kasance tare da
Annabi ﷺ a
halin tafiya, sai na yi nufin in cire masa khuffinsa, sai Annabi ﷺ ya ce mini "KA BAR SU, DOMIN NI NA
SA SU SUNA DA TSARKI", Annabi ﷺ da ya gama alwala sai ya yi shafa a kansu”.
Bukhari 203, Muslim 274.
Baya ga wannan akwai hadisai da dama da Sahabbai
suka ruwaito cewa Annabi ﷺ idan
ya saka khuffi a halin tsarki, yayin da zai sake yin alwala ba ya cire su don
wanke ƙafa,
barin su kawai yake yi, sai ya yi shafa a kansu.
A'immatul fuƙaha'i sun haɗu a kan halascin yin shafa a kan khuffi ko safa a
lokacin alwala matuƙar
lokacin da aka sa su an sa su ne a halin tsarki. Inda kawai suka yi saɓani shi ne adadin kwanakin da mutum zai
iya yi yana shafa a kan khuffi ko safar.
Allah S.W.T ne mafi sani.
Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/Du5LNx31U9hDi6RƘbbrzgW
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.