Ticker

6/recent/ticker-posts

Waƙoƙin Almajirai maras Amshi

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

Waƙoƙin Almajirai maras Amshi

Waɗannan waƙoƙin almajiri ɗaya ne yake rerawa, ko da suna tare da wasu sai dai su zama ‘yan rakiyarsa, babu wani abu da suke cewa saboda wannan nau’in waƙoƙin basu da amshi, sai dai in an sami sadaka su taru su amfana. Suna amfani da ire-iren waɗannan waƙoƙin a wajen baransu ko a gidajen jama’a, ko kuma wajen taruwar jama’a don su sami sadaka, musamman ta abinci ko kuɗi. Akan sami sauran mabaratan da ba almajirai ba su yi amfani da wasu waƙoƙin domin nasu baran. Almajiri yakan maimaita waƙar ne har ya tashi baransa, ko kuma idan ya gaji sai wani abokinsa ya canje shi.


Post a Comment

0 Comments