Wanda Ya Fara Ƙaryata Tatsuniyar Cewa Bayajidda Ne Asalin Hausawa

Marigayi Farfesa Hambali Muhammad Jinju ke nan. Mutum na farko da ya fara ƙaryata tatsuniyar cewa Bayajidda ne asalin Hausawa a 1985. Gogaggen masanin harsuna, falsafa da tarihi haifaffen ƙasar Nijar, wanda ya koyar a jami'o'in Lagos da ABU da BUK da Danfodiyo University Sokoto. Maras tsoron fadar abin da bincike ya tabbatar, Farfesa Ibrahim Makwashi yace a gabansa ya taɓa faɗa wa Sarkin Daura Bashar ido da ido cewa su daina jingina tarihin Hausawa da Bayajidda.

Daga:

Zauren Hikima