Wai Ba Ruwansa Da Aƙeedah Ko Fiƙhu!

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu Alaikum. Ina hukuncin wanda ya ce shi babu ruwansa da Littaffan Fiƙhu, sai dai Alƙur’ani da Hadisi kawai? Da kuma wanda ya ce, shi kowa zai bi shi sallah, ba ruwan shi da tantance aƙeeda?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh

    Maganar wai mutum ya ce ba ruwansa da Fiƙhu sai dai Alƙur’ani da Hadisi, a gaskiya wannan maganar ba ta yi kama da maganar malamai ba, ta fi kama da maganar jahilai kawai. Domin abu ne sananne cewa, yawancin maganganun da suke cikin Alƙur’ani da Hadisai ba a gane su da tsabagen ƙwarewa da fahimta a cikin Harshen Larabci kaɗai, watau irin Larabcin da ake koyar da shi kuma ake fahimtarsa a yau. Dole ana buƙatar zurfafa bincike a cikin waɗansu fannonin ilimi, kamar na ULUUMUL-ƘUR’AAN da USUULUL-HADEETH da USUULUL-FIƘH da ƘAWAA’IDUL FIƘHIYYAH, baya ga fahimtar fannin AL-ADABUL-ARABIY don gane yadda Larabawan Farko da Alƙur’ani ya sauka da Harshensu suke magana.

    Daga nan muke gane cewa ba zai yiwu mutum ya samu sahihiyar fahimta a cikin addini ba tare da fahimtar fannin Fiƙhu da fahimtar ƙaidojinsa ba. Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:

    مَنْ يُرِدِ اللهُ بِهِ خَيْراً يُفَقِّهْهُ فِي الدِّينِ

    Duk wanda Allaah ke nufinsa da alkhairi sai ya ba shi Fiƙhu (fahimta) a cikin addini.

    Wannan ya nuna akwai alkhairi mai yawa a cikin Fiƙhu da dukkan nau’ukansa biyu: FIƘHUL-AKBAR da ya shafi mas’alolin aƙeeda, da FIƘHUL-ASGAR da ya shafi mas’alolin furu’a.

    Na’am, za ka iya cewa ba ka yarda da Fiƙhun da na yarda da shi ba, amma dai ba za ka ce ba ka yarda da dukkan Fiƙhu ba. Domin tun da sashen Fiƙhu fahimta ce, ba lallai abin da ni ko malamina ya fahimta ya dace da abin da kai ko malaminka ya fahimta ba. Shi ya sa ma da yawa ake samun saɓani a cikin mas’alolin Fiƙhu, hatta a tsakanin mabiya mazhaba guda ɗaya ma!

    Abin lura dai: Matuƙar abin da aka gina Fiƙhun a kansa ginshiƙi ne ƙwaƙƙwara, ba a bi son-zuciya ko shaawar rai ba, ba za a ce wanda ya bi shi ya aikata munkari ba.

    Amma dayake malami yana gina yawancin mas’alolin Fiƙhunsa a kan Ƙiyasi ne saboda rashin bayyanar dalili ingantacce kuma sarihi a fili daga Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) a wurinsa, a kan mas’alar tun da farko, sai ya zama wannan bai hana a yi nasiha ga wanda ya riƙe wannan maganar mara ƙarfi ba a yau, bayan an samu gamsassun dalilai ingantattu a kan masalar. Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) da ya ce:

    الدِّينُ النَّصِيحَةُ ... للهِ ، وَلِكِتَابِهِ ، وَلِرَسُولِهِ ، وَلِأَئِمَّةِ الْمُسْلِمِينَ ، وَعَامَّتِهِمْ

    Addini nasiha ne… ga Allaah da Littafinsa da Manzonsa da Shugabannin Musulmi da sauran Jama’ar Musulmi

    Maƙalewa da nacewa da nuna raayin riƙau ga wata magana daga cikin maganganun manyan malaman Fiƙhu, bayan kuma an fahimci ta saɓa, ko ta ci karo da hukuncin Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ba alkhairi ba ne, kuma ba ɗabi’ar mutanen kirki ba ce. Allaah Maɗaukakin Sarki ya ce:

    وَمَا كَانَ لِمُؤْمِنٍ وَلَا مُؤْمِنَةٍ إَذَا قَضَى اللهُ وَرَسُولُهُ أَمْراً أَن يَّكُونَ لَهُمُ الْخِيَرَةُ مِنْ أَمْرِهِمْ وَمَن يَّعْصِ اللهَ وَرَسُولَهُ فَقَدْ ضَلَّ ضَلَالاً مُبِيناً

    Bai kamaci wani mumini ko wata mumina ba, idan Allaah da Manzonsa suka yanke wani al’amari ya zama suna da wani zaɓi na su na-daban a cikin al’amarinsu.

    Kuma duk wanda ya saɓa wa Allaah da Manzonsa to, tabbas ya ɓace ɓacewa bayananniya daga hanya.

    Sannan kuma Allaah Mabuwayi Mai Girma ya ce:

    يَآ أَيُّهَا الَّذِينَ ءَامَنُوا لَا تُقَدِّمُوا بَيْنَ يَدَيِ اللهِ وَرَسُولِهِ

    Ya ku waɗanda suka yi imani! Kar ku gabatar da komai a gaban Allaah da Manzonsa.

    Malamai suka ce: Ma’anarta: Kar ku gabatar da wata aƙeeda ko wani aiki ko wani ra’ayi ko wata fahimta a gaban Allaah da Manzonsa. Ku dai ku zama mabiya masu biyayya, ba masu ƙirƙirar bidia ba.

    Allaah ya datar da mu gaba ɗaya ga abin da yake so kuma yake yarda da shi.

    Maganar bin kowane limami sallah kuwa, ƙaidar da Malamai suka sanya kuma suke gudana a kanta ita ce:

    مَنْ صَحَّتْ صَلَاتُهُ لِنَفْسِهِ صَحَّتْ صَلَاتُهُ لِغَيْرِهِ

    Duk wanda sallarsa shi kaɗai ta inganta, to sallarsa ga waninsa ma ta inganta.

    Ma’anar wannan maganar a wurin malamai ita ce: Ya halatta a bi duk limamin da aka tabbatar da cewa idan ya yi sallah shi kaɗai sallar ta yi, ko da kuwa yana yin waɗansu kura-kurai ko laifuffuka a cikinta, saboda Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:

    يُصَلُّونَ لَكُمْ ، فَإِنْ أَصَابُوا فَلَكُمْ وَلَهُمْ ، وَإِنْ أَخْطَأُوا فَلَكُمْ وَعَلَيْهِمْ

    Suna yi muku limancin sallah, to idan suka dace ku da su duk kun haye, idan kuma suka yi kuskure to, ku kun dace su kuma suna da laifi.

    Amma idan mutum yana da iko to daidai ne ya nemi masallacin da limaminsa ya zama ƙwararre wurin bin Sunnah daidai a cikin ayyukan sallarsa. Ko shakka babu, wannan ya fi wanda ba shi ba.

    Haka idan yana da ikon sanya limamin da ya fi sani da iyawa, to wajibinsa ne ya yi hakan. Kuma haram ne ya bar limamin da bai iya ba, wanda yake yin kura-kurai a cikin sallarsa!

    WALLAHU A'ALAM

    Sheikh Muhammad Abdullah Assalafiy

    Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.