Ticker

6/recent/ticker-posts

Maganin Matsalar Rashin Sha'awa Ga Mata

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum malam ina da tambaya inada karancin sha'awa mijina bayasamun gamsuwa dani harsai inaso inkuma banaso haka zatawahala, mezanyi malam Dangane da mastalar. afahimtar dani nice ko mijina, nagode

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumussalamu..

Dangane da matsalolin dake damun maza, su mata Allah baya jarabtasu da irin waɗannan matsaloli? a'a abun bahaka baneba. ba shakka suma Allah yakan jarabcesu dasu suma, dan idan akasami matsala narashin sha'awa, amma fa wannan Ina maganane akan mata Kaɗai.

To idan akasami karancin sha'awa, koko karancin ni'ima, ga shawara da malaman muslunci suka bada zaɓi kamar haka:

1. Za'a samo rabin kofi na garin habbatisauda. Asamo rabin kofi na yansun. Sai kuma asamo man yansun ɗin. Za'a debi habba da yansun atafasa, bayan haka adiga man yansun sannan asha, akalla anaso kullum za'a sha sau uku, kofi dai dai ko sau biyu arana, in Shã Allah za'adace.

2. Kokuma asamo garin irkusus, da garin hulba arika tafasa cokali ɗaya anasha. kuma za'a iya arika cin ruman shima ruman malaman muslunci sukace idan ana yawan cinsa to yana magance wannan matsala narashin sha'awa ko karancin ta amma ga mata.

3. Kokuma arika tafasa garin habbatisauda cokali ɗaya asanya zuma, kuma adiga man ruman ɗan kaɗan anaso shima za'a sha kofi 3 arana safe darana dayamma, ko sau biyu.

4. Ko asamo maremiyya za'a iya samunsa wajan masu saida magungunan muslunci, shima tafasa shi akeyi anasha.

5. Kokuma asamo gari na kafi suga shima wani maganine baya da wahalar samu, sai ahaɗa da minnanas, wato gari na abarba shima baya da wahalar samu, sai ahaɗa, da dabino, dakuma aya, amma za'a nika dabino ɗin da aya ko adaka, sai ahaɗa, kuma azuba citta yar kaɗan, azuba suga rawar doki, ko farar suga da aka sani, ko adafa kokuma ajika awaje maikya yayi kamar kwana biyu ko awa 24, sai kuma atace asanya awaje maikya asanya a fireza,zaarika shan kofi dasafe, darana, dayamma, ko sau biyu arana, wannan shima yana magance karancin ni'ima, koko karancin sha'awa ga mata, in Allah yaso za'a dace.

6. Kokuma asamo man hulba, daman habbatisauda, da man tafarnuwa, da man Na'a Na'a, zait lauz halawi, sai ahaɗa asha amma anaso bayan ansha ba'aso aci komai ko asha har sai dan wani lokaci, kuma anaso amike tsaye namintina 10-15 amma wanda jini yakusa zuwa mata to kada tasha wannan haɗin nakarshe, shima wannan idan ansamo masu kya, to yana magance karancin ni'ima ga mata wasu malaman muslunci sunfada mubashara cewa anfanin dawannan maganin yakeyi yafi duk wani shaye shayen magunguna damata keyi amfani ajiki, domin babu wata illa acikinsa, in Shã Allah za'ayi mamaki.

7. Ki nemi ruwan kwakwa, madara peak, da kuma ruwan Inabi ki rika sha. Domin waɗannan duk sukan haddasa dawowar ni'ima ko sha'awa ajikin Mace ko namiji.

8. Ki samu shammar ki nikashi ki rika haɗawa da zuma kina sha. In Shã Allah zaki samu lafiya.

Allah ta'ala yasa mudace

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/DSdbBS8RZVoIKYG5exOuZE

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments