Hukunchin Wanda Yawu Yake Taruwa A Bakinsa Acikin Sallah

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuh. menene hukunchin wanda yawu yake taruwa a bakinsa koda yana sallah?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumussalam warahmatullahi wabarakatuh

    Wanda yawu yake taruwa acikin bakin sa a lokacin da yaje yana a halin sallah babu komai akansa in shaa Allah, domin taruwan yawu a bakin mai yin sallah baya daga cikin abubuwa da suke ruguza sallah ko su karhantar da ita don haka babu komai akansa in shaa Allah, sai dai saboda yanayin karatun wanda yawu ya taru a bakin sa ba lallai bane ya fita dakyau yadda ake bukata to sai ya samu wani kyalle mai kauri karami wanda yasan zai iya yin amfani dashi wajen cire yawun daga cikin bakin sa ba tare da yayi motsi mai yawa ba ta yadda zai zamana cewa karatun sallar sa yana fita kamar yadda ake bukata, kuma muna addu'ar Allah ya bashi lafiya domin wannan yana da alaƙa da rashin lafiya sai a bibiyi masana harkan lafiya in shaa Allah za'a samu abinda zai takaita faruwan hakan akai akai koda ba a daina ba gaba daya Allah ne mafi sani

    Ustaz Hussaini Haruna Kuriga

    Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/IƘUc0RxgCwA3JFiEKl8j5E

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.