Ticker

6/recent/ticker-posts

Waƙar “Daudun bara”:

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

Waƙar “Daudun bara”:

Jagora: Ni daudun bara ɗan galadiman bara.

 Amshi: To.

 Jagora: Na saba bara ba ni kwana ban ci ba.

 Amshi: To.

 Jagora: Kun ga rawat tuwo kun ga sassakad dawo kun : ga kalmaɗaren miya.

 Amshi: To.

 Jagora: Ko kun dahwa kudaku abincin cika mummuƙe

 Amshi: To.

 Jagora: Kak ka ci kar kasha rabon wani ba naka ba.

 Amshi: To.

 Jagora: In da naka ne kana ɗaka aka baka shi.

 Amshi: To.

Jagora: Mai babban rabo ba zai wuce aljanna ba.

 Amshi: To.

 Jagora: Mai ƙaramin rabo ba zai wuce alhamdu ba.

 Amshi: To.


Post a Comment

0 Comments