Ticker

6/recent/ticker-posts

‘Tsuntsu kamata yai da shi yai kuka, irin na kaka nasa can mai nisa’ - RANAR HAUSA TA DUNIYA

Mene Ne Ya Sa Yawancin Masu Nazartar Hausa A Jami’a Suke Ɓoye Kansu Ko Ba Sa So A Alaƙanta Su Da Harshen Hausan Da Suke Nazarta?

Kai tsaye a fahimtata amsar ita ce, ‘Kallon Ƙasƙanci’ da rashin ƙima da suke wa harshen. Da kuma ganin nazartar harshen ba zai kai su inda suke fatan kasancewa ba. Da yawan ɗalibai da suke nazartar Hausa sukan ji harshen bai kai a nazarce sa ba , duk da irin wahalar da nazarin harshen ke da shi wajen nazarta a manyan makarantu da jami’o’i.

 Shin hakan na faruwa ne, domin Hausar ta kasance ita ce harshen uwa? Ko kuma babu amfanin nazartar harshen ne . Saboda babu wani takamaimen aiki da mutm zai iya yi bayan ya kamala jami’a? Ko kuwa suna ganin rashin ƙoƙari ne ko hazaƙa kan sa mutum ya nazarci harshen Hausa?

 Wata kila dai dalilan ba su wuce haka ba , idan ma sun wuce akwai waɗannan a ciki. Matukar waɗannan ne dalilan da mutane ko ɗalibai masu nazartar harshen Hausa ke sa su boye kansu da rashin son a alaƙanta su da Hausar. Tabbas, abun akwai matukar ba da mamaki.

 Domin ina ganin ɗalibai ko ma matasanmu na yau ba su da abun koyi da suke wuce Turawa da Labarawa , wanda kowannensu yana nazartar harshensa na uwa cikin alfahari. A wasu ƙasashen ma, masu nazartar harshe musamman ma na uwa su ne abun girmamawa .Wani babban abun mamaki da harshen Hausa shi ne, a iya cewa Turawa ne suka fara nazartar sa tare da yin rubuce-rubuce da samar da hanyar rubuta Hausar cikin harrufan boko, domin sanin amfanin harshen da suka yi.

 Dangane da tunanin ko da mutun ya kamala jami’a ba zai sama abun yi ba, saboda Hausa ya nazarta. A iya cewa masu irin wannan tunani sun zama tamkar makafi. Domin ba su gani yadda wasu da Hausa sun zama Farfesoshi da sanatoci da ‘yan majalisu na jihohi da na tarayya wasu ma’aikatan gwamnati da kafafen sadarwa na Tb da rediyo, wasu da yawa sun zama manyan ‘yan kasuwa . Sannan sun manta da yawan kwasa-kwasai da ake nazarta a jami’o’in Nijeriya ba su da mazauni ko gurbin aiki a ƙasar , domin ko da mutum ya nazarce su babu inda zai yi aiki da su .Duk da ana ganin su ne abun tuƙaho da cika baki sabanin harshen Hausa.

 Da yawan mutane suna ganin duk wanda yake nazartar Hausa a matsayin kwas a jami’a kamar gazawa ce ta rashin ƙoƙari ko rashin fahimta da rashin son wahala wajen karatu. Wanda ba haka ba ne . Ni dalibi ne, da ke nazaartar harshen Hausa a Jami’a . Da yawan ‘yan uwana da muka yi sakandire da su, na fi su fi su fahimatar karatu. Amma yanzu wasu suna sassa mabambanta, kuma da yawa daga cikinsu su suke jagorantar ɗaliban sassan wajen ƙoƙari. Kenan wannan ya nuna cewa ba gazawa ce ba don mutun ya nazarci harshen Hausa.

 Daga ƙarshe , harshen Hausa yana daga cikin manyan harsuna da gidajen rediyo da sauran kafafen sada zumunta da na yaɗa Labarai na nan gida da waje ke amfani da su wajen watsa labarai da sauran manufofinsu . A nan gida Nijeriya da ma Afirka baki ɗaya. Duk da cewa a nan gida Nijeriya kawai mun da harsuna sama da ɗari biyar . Bayan haka harshen Hausa yakan ba duk wanda ya nazarce shi da kyau damar sanin ilimin Kimiyar Harshe da Al’ada da kuma Adabi , ba iya na harshen Hausa ba har da sauran harsuna na duniya . Kai ba ma wannan ba, nazartar harshen Hausa kan sa mutum ya ƙware a fannoni kamar ; fassara da tafinta da kuma sanin ilimin zamantakewar dan Adam.

Ina taya ɗaukacin Hausawa murna a wannan rana (RANAR HAUSA TA DUNIYA)

SHITU MUHAMMAD LAWAL
SHUGABAN ƘUGIYAR HABAKA HAUSA
Sashin Harsuna Da Al’adun Afirka,
Tsangayar Fasaha,
Jami’ar Ahmad Bello, Zaria.

Ibnshitu1220@gmail.com

Kafar Intanet Ɗin Da Za Ku Samu Dubbannin Rubuce-Rubuce Game Harshe Da Al'ada Da Adabin Hausawa

Post a Comment

0 Comments