Ticker

6/recent/ticker-posts

Alamci

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

Alamci

Salon alamci shi ne inda mawaƙi zai ambaci wani abu da nufin ya wakilci wani abu da bai ambaci sunansa ba, amma ya kasance mutane suna sane da wakilcin. Misali kamar naɗi a matsayin sarauta. Dumfawa, (2002).

Alamci dabara ce ta bayyana wani abu ta hanyar ba shi wata alama wadda za ta tsaya a maimakonsa. Ɗangambo, (2007)

Wato ke nan Idan mawaƙi ya bayyana wani abu ta hanyar ambaton wata kalma ko wani zance da za a iya hango abin da yake nufi ta dubin kalamin ko kalmar, to ana kiran wannan salo alamtarwa. Misali:

 Jagora: Kanta ƙwaƙwal, ƙwaƙwal ƙwaƙwal babu gashi,

 Amshi: To

 Jagora: Ko guiwar amali ta fi shi manga.

 (Waƙar Ƙazama : Inno mai bara Sabuwar hanya)

Manga wani nau’in gyaran gashi ne na gargajiya da mafi yawa mata masu yalwar gashin kai ke yi. A ɗan waƙar da ya gabata mawaƙin na cewa gwiwar amalin raƙumi ta fi kan mace ƙazama gashi. Sai dai a maimakon ya kira sunan gashi sai ya kira sunan wani abu da sai da gashi ake iya yinsa ya danganta shi ga gwiwar raƙumi. Wato ke nan kalmar ‘manga’ alamci ne na gashi wanda gwiwar amalin raƙumi ta ɗara kan ƙazamar mace da shi.


Post a Comment

0 Comments