Ticker

6/recent/ticker-posts

Mijin Ba Ya Son Ƙaryata Matarsa

Wasa Ya Zama Gaske! 🤔 

Ƙanin mijinta ne ya kawo ma su ziyara ya tarar ana gyran gidan. Sai ya ce antinmu lafiya na ga a na gyara? Sai ta ce yayanku ne zai ƙara aure. Ta na yi ma sa wasa. Ya ce kai da gaske? ta ce ka tambayi yayan naku mana.


Ya na fita sai ya je shagon yayanshi yake cewa "Yaya a she aure zaka ƙara?" Sai ya ce waye ya faɗa maka? Yace matarka mana ita ce ta faɗa min yanzu. 


Mijin ba ya son ƙaryata matarshi. Hakan ya sa sai yace "eh" in sha Allah aure zan ƙara.


Ƙanin yace Allah Ya sanya alkhairi ya na tafiya. Sai mijin ya yi tunanin bai kamata ya ƙaryata matarshi ba. Kawai sai ya yanke shawarar YA ƙara auren gudun kar ƙanin nashi ya raina matar tasa.


Kun ji so na gaskiya Allah ya baku mazaje masu sonku kamar shi 😄🤣🥺 fatan alkhairi gareku.


Idan ke ce wani mataki za ki ɗauka a gaba?Post a Comment

0 Comments