Ticker

6/recent/ticker-posts

Ma’anar Salo

Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali  SububuAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Amali  Sububu

Ma’anar  Salo

Malamai da masu nazarin adabi sun bayar da ma’anar salo ta hanyoyi da dama duk da yake kusan manufa ɗaya suka fuskanta, kalmomin da suka yi amfani da su kawai ka bambanta.

Salo a waƙoƙin baka wata hanya ce wadda makaɗi ke kyautata zaren tunaninsa, ya sarrafa shi cikin azanci don ya cim ma burinsa na isar da saƙo a waƙa. Gusau (2003:54).

 

Ga abin da wanna masani ya nuna salo shi ne dabarun da mai magana ya ƙunsa a cikin zancensa da nufin isar da saƙo ta hanyar da za a fahimce shi cikin sauƙi ko da wahala, a cikin raha ko cikin ƙosawa. Duk ta hanyar da masu saurare suka ji jawabin daga hanyoyin da aka ambata, to shi ne irin salon da mai zancen ya yi amfani da shi.

 

A wata ma’anar da aka bayar cewa aka yi:

 

Salo yana nufin duk wata dabara ko hanya a cikin waƙa wadda aka bi domin isar da saƙo. Ita wannan dabara ko hanya tana yi wa waƙa kwalliya ta yadda saƙon waƙar zai isa ga mai saurare ko karatun waƙar. Yahya (1999:3).

Wannan ma’ana ita ma kusan manufarta ɗaya da wadda ta gabace ta. Bayani yana nuni ne ga iri dabarun da mawaƙi yake amfani da su wajen isar da saƙonsa ga jama’a a cikinsa ba tare da gundura ba. Wato saƙonsa ya isa cikin birnin zuciyar masu saurare cikin nishaɗi da ban sha’awa[1].

 

Shi kuma wani malamin cewa ya yi:

Masana da manazarta suna ganin cewa salo yana da wuyar a gane shi a bisa kansa, sai dai ana iya gane wasu sigogi nasa dangane da ma’anarsa. To amma muna iya cewa salo shi ne hanyoyin isar da saƙo[2], Ɗangambo (2007:34). 

Bayanin wannan malami bai tsawaita ba. Ya taƙaita abin da waɗanda aka fara ambata suka faɗa tare da ƙara bayyana wahalar bayyana ma’anar salo ta amfani da kalmomi kawai. Duk da haka ya taƙaita ya ce hanyoyin isar da saƙo su ne salo, waɗanda nake ganin su ne waɗanda waɗancan malamai da na fara ambata suka faɗa.

A bisa bayanan masana ana iya cewa, salo wata dabara ce ta isar da saƙo ta hanyar zaɓen kalmomin da suka dace da abin da ake zance ta yadda zuciyar mai saurare ko karatun abun za ta karɓe[3] shi, ya Allah a cikin sauƙi ko tsauri.

 



[1]  Waɗanda kan sa mutane su yi dariya.

[2]  Abin da ake son nuna wa ga jama’a.

[3]  Yarda da shi.

Post a Comment

0 Comments