Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa. Ahmadu Bello University Press Limited.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
Kari
Kari shi ne awon da mawaƙi ya ɗora waƙarsa a kai. Akwai hanyoyi biyu da masu nazarin waƙa suka bayar da ake iya auna karin waƙar baka da su. Hanya ta farko ita ce ra’in Gusau (2003) wadda ya kira ta gidan dara. Hanya ta biyu ita ce ra’in Dunfawa (2003) wadda ya kira Bahaushen Kari.
A hanya ta farko ana ƙirga yawan gaɓoɓin kowane layi ne gwargwadon
yawansu, sai a iya cewa tana kan gajeren kari ko dogo ko kuma matsakaici.
Misali:
Jagora: Kai ɗan na burge – burge,
Amshi: Burge.
Jagora: Ɗan na burge –
burge,
Amshi: Burge.
Jagora: Ga Inna ta yi baƙi,
Amshi: Burge.
Jagora: Baƙin da ba su ƙoshi,
Jagora: Baƙin da ba su ƙoshi.
(Ɗan Naburgi)
Kai/ɗan/na/bur/gi/bur/gi
g / g / g / g / g/ g/ g
Ga/in/na/ta/yi/ba/ ƙi
g/ g/ g/ g/ g/ g/ g
Ba/ƙin/da/ba/su/ƙo/shi
g/ g/ g/ g/ g/ g/ g
Idan
aka lura za a ga kowane layi na ɗan waƙar da ta gabata yana da gurbi kari (gaɓa) bakwai (7), wanda ya nuna karin
waƙar matsakaice ne.Gusau (2003:53)
Hanya
ta biyu kuwa Dunfawa (2003), an nuna ana samun kari ne daga sautin kiɗan da ke tafiya tare da waƙar abin da ya kira ’ƙira’. Daga gaɓoɓin sauti huɗu na ƙarshe da
layukan waƙa ke ƙarewa tare da
sautin kiɗa ake
samun karin waƙar. Ta wannan
hanya ya ce ake samun karuruwa bakwai. Misali:
Jagora: Maula ta Sidi maula ta Balarabe.
Amshi: Maula.
Ja gora: Babban gida da daɗin bara yake.
Amshi: Maula.
Jagora: Waccan ta ba ka waccan ta hana maka.
Amshi: Maula.
Ja gora: Waccan ta ɗauki kulki ta aza maka.
Amshi: Maula.
(Maula ta sidi)
Idan aka lura sai a ga gaɓoɓi huɗu na
layin farko su ne Balarabe, na layi na biyu su ne bara yake, na layi na uku
hana maka, na layi na huɗu su ne
aza maka. Wato haka abin yake:
Balaarabee = v-v-
Baraa yakee = v-v-
Hanna maka = v-v-
Azaa makaa = v-v-
A bisa wannan
awo an sami karin da ya kira mai ‘cassawa’, wanda gajerar gaɓa da doguwa ke karɓa-karɓa, Dunfawa (2003:29). A bisa ra’i na biyu sai mu ce
wannan waƙa tana bisa kari mai cassawai.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.