Ticker

6/recent/ticker-posts

Isah Kure

Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Isah Kure

 

G/Waƙa : Akwai hura gidanai,

: Yana tsaye da hure[1].

 

  Jagora: Akwai hura gidanai,

: Yana tsaye da hure.

‘Y/ Amshi: Akwai hura gidanai,

: Yana tsaye da hure.

 

  Jagora: Kure mai abin rabo,

‘Y/Amshi: Ko wata yag hwaɗi  a ɗauka,

 

  Jagora: Kure mai abin daka,

 ‘Y/Amshi: Ko wata hwaɗi a ɗauka.

 

  Jagora: Yaro gahwarak ka ga,,

 ‘Y/Amshi: Manya sun taho ga aiki.x2

 

Jagora: Barau na goɗe,

 ‘Y/ Amshi: Wata’ala ya taimake shi,

 

  Jagora: Sarkin shanu ka biya,

‘Y/ Amshi: Wata’ala ya taimake shi.

 

Jagora: Alhaji Babawo ka biya,

‘Y/ Amshi: Wata’ala ya taimake ku.

: Akwai hura gidanai,

: Yana tsaye da hure.

 

 Jagora: Bari roƙon jini ga sa,

 ‘Y/ Amshi: Rannan ba jinni garab[2] ba,

 

  Jagora: In don kyauta gida garat,

‘Y/ Amshi: Ko rowa gida gareta..

 

Jagora: Ku san kyauta tana dad aɗi,

‘Y/ Amshi: Ko rowa tana da zahi.

: Akwai hura gidanai,

: Yana tsaye da hure.

 

 Jagora: Kowas samu duniya,

 ‘Y/ Amshi: Ya ci gad duniya ta ci shi.

 

Jagora: Kowas samu duniya,

 ‘Y/ Amshi: Shi ci gad duniya ta ci shi.

  Jagora: Bari mu ci ki duniya.x2

 ‘Y/Amshi: Kandan duniya ki ci mu.x2

: Akwai hura gidanai,

: Yana tsaye da hure.

 

 Jagora: Gero na gidanka Isah,

‘Y/ Amshi: Yau kowat taho a ba shi,

 

  Jagora: Dawa na gidanka Dule,

‘Y/ Amshi: Yau kowat taho a ba shi.

 

  Jagora: Masara gata nan ga Isah,

‘Y/ Amshi: Yau kowat taho a ba shi.

  Jagora: Kowake da shi da,

‘Y/Amshi: Shinkahwa gashi nan gidanku.

Jagora: Yaro gahwarak ka ga,

‘Y/ Amshi: Manya sun taho ga aiki.

: Akwai hura gidanai,

: Yana tsaye da hure.

 

 Jagora: Tafi gona biɗah hatci,

 ‘Y/ Amshi: Kowayai shi za ya samo.

 

 Jagora: Tafi gona biɗah hura,

 ‘Y/ Amshi: Kowayai shi za ya samo.

 

  Jagora: Ga makaɗin ɗiya nan,

‘Y/ Amshi: Sauna ban zuwa gidansu,

: Akwai hura gidanai,

: Yana tsaye da hure.

 

  Jagora: ‘Yan Keratsa ku ka noma,

‘Y/Amshi: Wata’alah ya taimake su.

 

  Jagora: ‘Yan Keratsa kun biya,

 ‘Y/ Amshi: Wata’alah ya taimake su.

 

Jagora: Gidan zago za ni na kiɗi,

 ‘Y/ Amshi: Don Allah tsaya mu samo.

  Jagora: Ko Usumanu ya biya,

 ‘Y/Amshi: Wata’ala Ya taimake su.

 

  Jagora: Ga Ummaru Manu ya biya,

 ‘Y/Amshi: Wata’ala Ya taimake su.

 

 Jagora: Usmanu ya biya kiɗi,

: Wata’ala ya taimake su.

‘Y/ Amshi: Wata’ala ya taimake su.

 

 Jagora: Jikan Magaji na gode,

‘Y/ Amshi: Ya biya buƙata.

  Jagora: Jika ka biya kiɗi,

 ‘Y/ Amshi: Wata’ala ya taimake su.

: Akwai hura gidanai,

: Yana tsaye da hure.

 

  Jagora; Zango zani na kiɗi,

‘Y/ Amshi: Wata’ala Shi taimake su,

 

 Jagora: Sarkin noma ya biya kiɗi,

: Jikan Magaji na gode,

 

 Jagora: Adamu ka ga ɗan ɗane naia,

 ‘Y/ Amshi: Wata’ala shi taimake su.

 

Jagora: Muhammadu ka biya kiɗi,

 ‘Y/ Amshi: Wata’ala ya taimake su.

 

 Jagora: Musa ka biya kiɗi,

 ‘Y/ Amshi: Wata’ala ya taimake su.

: Akwai hura gidanai,

: Yana tsaye da hure.

 

  Jagora: Ni dai zan kiɗi Turus,

 ‘Y/ Amshi: Domin in biya buƙata.

 

 Jagora: Isahn Maidawa shi da Idi,

 ‘Y/ Amshi: Wata’ala ya taimake su.

 

  Jagora: Ɗanbara ya biya kiɗi,x2

 ‘Y/ Amshi: Wata’ala ya taimake su.x2

: Akwai hura gidanai,

: Yana tsaye da hure.

 

 Jagora: Garba Abubakar ka kyauta,

 ‘Y/ Amshi: Wata’ala ya taimake su.

: Akwai hura gidanai,

: Yana tsaye da hure.

 

 Jagora: Tafi gona biɗah hura,

 ‘Y/ Amshi: Kowa yai shi za ya samo.

 

Jagora: Tafi gona biɗah[3] hatci,

 ‘Y/ Amshi: Kowa yai shi za ya samo.

: Akwai hura gidanai,

: Yana tsaye da hure.

 

 Jagora: Kowab bani in hwaɗi,x2

 ‘Y/ Amshi: Don kwab bani ba yawaige.x2

: Akwai hura gidanai,

: Yana tsaye da hure.

 

Jagora: In dai maganin maza,

: Ɗalha

 ‘Y/ Amshi: Wata’ala ya taimake su.

 

 Jagora: Ɗalha ya biya kiɗi.x2

‘Y/ Amshi: Wata’ala ya taimake su.x2

 

 Jagora: Sarkin noma ya biya kiɗi.

 ‘Y/ Amshi: Wata’ala ya taimake su.

 

 Jagora: Na gode ma Garba mai kuɗi.

 ‘Y/ Amshi: Wata’ala ya taimake su.

: Akwai hura gidanai,

: Yana tsaye da hure.

 

 Jagora: Tafi gona biɗah hura,

 ‘Y/ Amshi: Kowa yai shi za ya samo.

: Akwai hura gidanai,

: Yana tsaye da hure.



[1]  Huda shanu don a yi huɗa da su, wato a hude hancinsu a sa zari don sauƙin sarrafa su.

[2]  Gareshi.

[3]  Nema.

Post a Comment

0 Comments