Ticker

6/recent/ticker-posts

Bayar Da Maganin Ƙayyade Haihuwa (Family Planning)

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah, Na ga amsar tambayarka da ta gabata na kayyade haihuwa, to ina hukuncin wanda ake zuwa wurinsa ya bayar da maganin na family planning? Domin ina bayarwa, ni ce ma in-charge na section ɗin, na yi training babu adadi, akwai ma NGO da nake yi wa agent a kan family planning. Ina son gamsassun bayanai.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

Da farko, abin da ya wajaba garemu a duk inda mu ke, a matsayinmu na musulmi shi ne: Mu ji tsoron Allaah, mu tsaya a kan dokokinsa da shari’arsa da gwargwadon ikonmu da ƙarfinmu. Kar mu sake neman abin duniya ya janye mu daga kan hanyar Allaah, har mu koma mu zama mataimaka wurin cutar da al’ummarmu, a fili ko a ɓoye bisa sani ko rashin sani. Al’ummar da kowa a yau ya san tana fama da maƙiya da mahassada, masu neman durƙusar da ita ko ta halin ƙa-ƙa, a ciki da wajenta.

Abin da Allaah ya ce shi ne:

... ۘ وَتَعَاوَنُوا عَلَى الْبِرِّ وَالتَّقْوَىٰ ۖ وَلَا تَعَاوَنُوا عَلَى الْإِثْمِ وَالْعُدْوَانِ ۚ وَاتَّقُوا اللَّهَ ۖ إِنَّ اللَّهَ شَدِيدُ الْعِقَابِ

Kuma ku taimaki juna a kan ayyukan alheri da ƙarin taƙawa, kuma kar ku taimaki juna a kan zunubi da ƙetare haddi, kuma ku ji tsoron Allaah; haƙiƙa Allaah Mai Tsananin Uƙuba ne. (Surah Al-Maaidah: 2)

Don haka, ya halatta masana su bayar da shawarwari a ma’auratan da aka san cewa: Samun haihuwa gare su yana tattare da hatsari, kamar waɗanda aka bincika aka gano cewa jariran da za su haifa za su zama cikin matsanancin halin rayuwa ne, kamar masu fama da matsanancin ciwon amosanin jini (sickle cell), ko dai wasu larurori makamantan hakan. Mun yi ishara ga hakan a cikin amsar tambaya da ta gabata.

Tsarin iyali ta hanyar shan wasu ƙwayoyi, ko yin allurori, ko cusa waɗansu abubuwa a cikin jiki abu ne da ke tattare da hatsari ga lafiyar jiki, kamar yadda su kansu masana harkar lafiya suka bayyana. Don haka, barin saduwa a tsawon lokacin da ma’aurata suke buƙatar yin tsarin iyali a cikinsa ita ce sananniya kuma daɗaɗɗiyar hanya mafi kyau kuma mara hatsari, in Shã Allãh. Wannan kuwa ba ta buƙatar sai an zaunar da maaurata, an bayar da shawara gare su kafin su yi aiki da ita, tun da har dabbobi ma sun san ta, kuma suna amfani da ita. Domin yawancinsu suna da lokacin yin barbara a tsakaninsu, wanda kuma mace ba ta yarda da namiji a lokacin da ba wannan ɗin ba.

Amma mutanen da ba su san wannan ba, waɗanda harkokin rayuwarsu ta sa ba su damar sanin irin wannan ba, to babu laifi a wayar musu da kai kuma a fahimtar da su.

 

Allaah ya taimake mu gaba-ɗaya, ya sa mu iya yin amfani da matsayinmu a duk inda mu ke, domin taimakon al’ummar musulmi da addinin musulunci da gwargwadon iyawarmu.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullah Assalafiy

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/J1hm5Tw12uYBƙfaiPwf28l

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177 

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments