Ticker

6/recent/ticker-posts

Kato Yaz Zan Bai Noma

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Ƙato Yaz Zan Bai Noma

 

G/Waƙa: Ƙato Yaz zan bai Noma,

: Shi da buhun kowa duɗ ɗai.

 

Jagora: Sarki huwallazi ya mai girma,

: Nai roƙon sarki mai girma,

 : Allah gyara ya rabbana,

: Kai kiɗa aikin noma,

: Na ce jama’a a tai a yi noma,

: A’a ke yi maza da mata baki dai,

: Ka ji Ɗankurmi can zan kwana,

: Ɗankurmi can zan kwana,

: Don in gano Mamman Sani,

: Sai na  biyo ta Ɗan kurmi,

: Sai na biyo ta Tsontsomawa,

: Sai na tsomo waƙar Sani,

: Mamman sani.

  ‘Y/Amshi: Babin noma.

 

 Jagora  : Ai ka ji kidan aikin noma,

: Amma Yaro in yaz zan bai noma,

: Ba ni kular samnan banza.

 

Jagora  : Sai Yaro yaz zan bai noma.

‘Y/Amshi: Shi da buhun kowa duk dai,

: Ataɓuka[1] kuma na noma,

: Ɗan Ige shi ma na noma,

: Ali shi ma na noma,

: Ɗan ladi ashe shi ma na noma,

: Mamman sani,

: Mamman sani,

: Mamman sani,

: Babin noma.

 

 Jagora : Don Allah ka dakata don rabbani,

: Ga maganar aikin noma,

: An ce dan Ige na noma,

: Kuma ashe Ataɓuka ma na noma,

: Ɗan Mafara ma na noma,

: Audu ka ga yana noma,

: Sannan bilya ma na noma,

: Kasan dogon kwalba ma na noma,

: To balle mamman sani,

: Mamman koma ban noma,

: Bari Mamman in riƙe kwashe[2] na,

: Kai Mamman ko ban noma,

: Bari Mamman in rike galma ta,

: Amma Mamman ko ban noma,

: Bari Mamman in rike hauyata,

: Mun jeki wajan gayya,

: Ka duka na duka Sani,

: In nag gaji in miƙewa ta,

: In ɗauko kwano mai dama,

: To sai in tai kiran mai yin noma,

: Allah kawo Mamman  Sani.

 ‘Y/Amshi: Mamman sani,

: Babin noma,

: ‘Yan mata da maza na noma,

: Ka ji kidin waƙar noma,

: Waƙar noma,

: Darajar ɗanɗa.

: Ina wani nac ce ɗan sarki?

: Ko da na ce alkali,

: Ko wani mai iko Sani,

: Yaz zan lallai bai noma,

: Ba ni kular samnan banza,

 

 Jagora : Kasan maganar dai-dai,

  : Guda-guda kai bai yarda ba,

: Guda-guda kai mai,

: Guda-guda kai mai ganga,

: Ko can kiɗin ga ni dai ne Sani,

: Ai ka san gabas da yamma,

: Dama da hauni,

: Mamman duk wani mai noma,

: Mamman noma,

: Mamman Sani,

: Ka ga yana noma,

: Garba ka ga kana noma,

: Yaro in yaz zan bai noma,

‘Y/Amshi: Shi da buhun kowa duk ɗai.

 

  Jagora  : Kato yaz zan bai noma.

  ‘Y/Amshi: Ba mu kula samnan banza.

 

 Jagora  : Amma sarkin Mafara ka kyauta man,

: Don saboda albarkar noma,

: Mamman ya kyakkyauta ma,

: Ya  ba ni kuɗi don jin daɗi,

: Sai kiɗin aikin noma,

: Mamman ko ban noma,

: Bari Mamman in riƙe galmata,

: Mamman ko ban noma,

: Bari Mamman in rike hauyata[3],

: Mamman ko ban noma,

 : Bari Mamman in riƙe kwashena,

: Mun jeki wajen gayya,

: Ka duka na duka Sani,

: In nag gaji in mikewa ta,

: In ɗau kwano mai dama,

: In tai kiran mai yin noma,

: Allah kawo Mamman Sani.

‘Y/Amshi: Mamman Sani,

: Babin noma.

 

Jagora  : Ɗan maje can zan kwana,

: Dan in ga buhun dawa zalla,

: Ɗan maje can zan kwana,

: Ga buhuhuwan wake,

: Sannan sai kuma shinkahwa,

: Mamman Sani ya bakkani.

‘Y/Amshi: Hali na duniya mamman Sani,

: Birnin Kano ma na noma,

: Birnin Sakkwato ma na ji suna noma,

: Kuma na duba Mamman Sani,

: Hali na duniya Mamman Sani.

 

Jagora  : Ka ji ka dakata kai mai turu,

: Ga maganar aikin noma,

: Lallai arewa to duk baki ɗai,

: Mamman ka ga ana noma,

 : Gara mu miƙe mu yi noma,

: Don ko noma darajar ɗanɗa,

: Amma ƙato in yaz zan bai noma.

‘Y/Amshi: Ba ni kula samnan banza.

 

Jagora  : Amma ƙato yaz zan bai noma.

‘Y/Amshi: Shi da buhun taki duk dai.

 

Jagora  : Wannan maganar dai-dai,

: Ka san ai ban maganar,

: Ka san ni ban maganar banza,

: Sai dai ni in maganar tsishi,

: Mamman darajar noma,

: Ka ga riga mai dama,

: Mamman darajar noma,

: Ka ga wando mai dama,

: Mamman darajar noma,

: Ka ga hula mai dama,

: Ga kuma mota baki dai,

: Ga mata Mamman Sani,

: Mamman darajar noma,

: Amma kato in yaz zan bai noma.

‘Y/Amshi: Ba ni kular samnan banza.

 

Jagora  : Sai kato in yaz zan bai noma,

  ‘Y/Amshi: Shi da buhun kowa duɗ ɗai,

: Sai kato yaz zan bai noma,

: Ba ni kular samnan banza.

 

 Jagora  : Yawwa.

‘Y/Amshi: Mamman Sani,

 : Mamman Sani,

: Mamman Sani,

: Babin noma.

: Kuma Ɗan Ige ban raina mai ba,

: A taɓuka ma na fili,

: Na faɗi lawali bizi nauwa,

: Ya biyani alheri yam man,

: Usman ban rena mai ba.

 

Jagora  : Ali na mani kotoko alheri yam man,

: Mamman darajar noma,

: Lallai ko ya kyauta ma,

: Kudin ka shi yab bakkani,

: Ya  ba ni kudi don jin daɗi,

: Ku dakata don rabbani,

: Bayan na ji kiɗin noma,

: Nay yi kiɗi nab bi,

: Mamman duk ko baki dai,

: A hankali kai mai turu,

: Ko da ilimin mallan kay yi,

: Kai koda tukin mota kay yi,

: Aikin gwamnati ka riƙe Sani,

: Mammam tai ka yi noma,

: Ƙato yaz zan bai noma.

‘Y/Amshi: Ba ni kular shirgin[4] banza.

 

Jagora  : Lallai ƙato yaz zan bai noma.

‘Y/Amshi: Shi da buhun kowa duɗ ɗai.

 

Jagora  : Yawwa.

‘Y/Amshi: Ɗan Haruna Zariya na noma,

: Birnin Tureta nake kwana,

: Sarkin tasha ya kyauta min,

: Sarkin tasha ya kyauta min,

: Ɗan Haruna mai Allah sarki, 

: Ya biya ni kan halin noma, 

 

Jagora  : Ka ji sarkin ƙaya ya kyauta min,

: Lallai ko ya kyauta min,

: Don ko na Maradun na komai[5],

: Mamman ya kyauta min,

: Ya  ba ni kuɗi don jin daɗi,

: Mamman ya kyauta min,

: Ka ji kansila ka kyauta min,

: Babba Ibrahim ka ga ƙarin kuɗɗi,

: Adalilin babin noma,

: Mamman ko ban noma,

 : Mamman ko ban noma,

: Bari Mamman in rike hauyata,

: Mamman ko ban noma,

: Bari Mamman in riƙe kwashe[6]na,

: Mamman ko ban noma,

: Bari Mamman in rike galmata,

: Mun je mu wajen gayya,

: Ka duƙa na duƙa Sani,

: In nag gaji in miƙewata,

: In ɗau kwano to Sani,

: Na tai kiran mai yin noma,

: Alheri shi ne yam man,

: Hassan ɗan bawa yana komi,

: Ɗankurmi can zan kwana,

: Tsontsomawa can zan kwana,

: Amma saboda na ji suna noma,

: Aikin noma am mai daɗi,

: Amma kato in yaz zan bai noma,

‘Y/Amshi: Shi da buhun kowa[7] duk ɗai,

 

Jagora  : Lallai kato yaz zan bai noma.

 ‘Y/Amshi: Ba ni kular shirgin banza.

 

 Jagora  : Amma kato yaz zan bai noma.

‘Y/Amshi: Ba ni kular samnan banza.

 

Jagora  : Amma ƙato yaz zan bai noma.

 ‘Y/Amshi: Shi da buhun taki duk dai.

 

 Jagora  : Amma ƙato yaz zan bai noma.

  ‘Y/Amshi: Ba ni kular shirgin banza.

 

 Jagora  : Yawwa.[1]  Suna wani mutum ne.

[2]  Magirbi.

[3]  Fartanya.

[4]  Wani tuli wanda aka tattara shi ba cikin tsari ba har ya girma.

[5]  Bayar da kyauta.

[6]  Magirbi,

[7] Kunɓaɓin wake, wanda ake cirewa bayan an sussuke waken an cire ƙwayar.

Post a Comment

0 Comments