Ticker

6/recent/ticker-posts

Asalin Kalmar Hausa

Nil Skinner (1968) cewa ya yi, “Asalin kalmar Hausa, an samo ta daga Songhai. A ganinsa, akwai daɗaɗɗiyar dangantaka tsakanin Hausawa da su mutanen Songhai, har ta kai Hausawa suna aron kalmomin Songhai. Domin a nasa binciken cewa ya yi, kalmar Hausa an samo ta ne daga ‘Assa’ sunan da suke kiran mutanen da suke Gabas da su, su kuma Hausawa suka aro suka laƙaba wa kansu.

Malam Aminu Kano kuwa, ya bayyana cewa an samo kalmar Hausa daga kalmar Habasha, wai don a cewar sa, asalin Hausawa mutanen Habasha ne, kuma a maimakon a rinƙa cewa Habasha ɗin, sai ake cewa Hausa. 

 Mr. C.R. Niben (1971) cewa ya yi, an samo asalin kalmar Hausa ne daga Buzaye, domin kuwa haka suke kiran mutanen dake zaune a Arewacin Kogin Kwara, wato Hausa. 

 Martaba Sarkin Ningi; Alhaji Haruna Wakati, cewa ya yi, an samo kalmar Hausa ce daga labarin zuwan Bayajidda garin Daura, a lokacin, da ya isa da daddare ya sauka a gidan wata tsohuwa ‘Ayyana’ ko kuma ‘Wayre’, inda ya buƙaci ruwan sha a wurinta, da cewar ba ta da ruwa ya tambaye ta, ina zai samu? Ita kuma ta sanar da shi babu inda zai samu sai ya je rijiya, kuma matsalar ba a ɗiban ruwa sai mako-mako ake zuwa a ɗebo ruwan; saboda wata macijiya mai suna sarki.

Daga nan, sai ya buƙaci ta ba shi guga, ta nuna mai inda rijiyar take, ya je ya zura guga ya fara debo ruwan, sai wannan macijiyar ta biyo igiyar gugar, shi kuma ya sa takobi ya sare kanta. Inda labari ya bazu a gari har Sarauniya Daurama ta samu labarin abin da yake faruwa, ta sa a nemo wanda ya kashe macijiyar don a yi masa kyautar bajintar da ya yi.

Ana ta neman wanda ya kashe amma ba a same shi ba. Sai aka tambayi tsohuwa, wanda ya kashe ta ba a same shi ba. Sai ta ce musu “Ai ya hau”. Hau-sa maimakon ta ce ya hau doki tunda ita ba ta taɓa ganin doki ba. To wai wannan ‘Ya hau-sa’ ne aka haɗe kalmomin ne suka koma ‘Hausa’.

Haka kuma a wata fadar an ce, da can Larabawa da suka zo harkar cinikayya Arewa zuwa Kurmi, lokacin da suka zo, suka ga kalmomi da ɗabi’u irin nasu, sai suka ce waɗannan mutane sun so su yi kama da mu, amma sun ɗan karkace. To shi ne idan za su zo, sai su ce: “Za mu Hawasa”, wato za su garin karkatattu. 

Masu ra’ayin Harshe suna ganin cewa kalmar Hausa a wurin su ‘Bahaushe’ ma’anar ta “harshe”, domin idan ka yi magana da wani harshe daban, Bahaushe yakan ce ” Ya ji ana wata Hausa”, wato a nan Hausa sunan harshe ne, ba na ƙabila ba, kuma al’ummomin da suka taru suke magana da wannan harshe su ne Hausawa. 

A taƙaice dai, Kalmar Hausa tana nufin harshe, tana kuma nufin mutanen da suke magana da harshen Hausa a matsayin harshen uwa, kamar yadda kuma take nufin ƙasar da su waɗannan al’umma ta Hausa suke zaune.
Kafar Intanet Ɗin Da Za Ku Samu Dubbannin Rubuce-Rubuce Game Harshe Da Al'ada Da Adabin Hausawa

Aminu Musa 
26082023
Ranarhausataduniya

Post a Comment

0 Comments