Ticker

6/recent/ticker-posts

Waiwaye Kan Ire-Iren Auren Hausawa

AUREN SOYAYYA

Shi auren soyayya aure ne wanda saurayi ke ganin budurwa yace yana sonta da aure,itakuma sai ta amince masa, wasu kanyi soyayya ta lokaci mai tsawo kafin iyaye su shigo cikin lamarin wasu kuwa ba’a daɗewa iyaye ke shigowa da zarar an samu yarda da amincewa a ɓangarorin biyu, sai azo ayi niyyar daure

AUREN ZUMUNTA:

Auren Zumunta aure ne da ake nema wa yaro ko yarinya daga cikin dangin uba ko dagin uwa, batare da an nemi shawarar yarinya ko yaro ba, wasu lokutan kuma yakan faruwa ga abokin mahaifin yaro ko na yarinya.

Ana yin wanann aure ne domin kara danƙon zumunci a tsakanin ɓangarorin biyu.

AUREN DOLE:

Shi kuma auren dole aure ne da saurayi kan ga yariya yace yana sonta da aure, amma ita bata sonsa. Iyayenta kuma su amince akan batun aura masa ita, wasu lokutan kuma iyayen ba’a son ransu zasu aurar da ƴar tasu ba. sai don bisa wani dalili a tsakaninsu.

A irin wannan yanayi akan nemawa saurayi budurwa ba tare da  yana sonta ba, saboda wata alaƙa ta mahaifinsa ko mahaifiyar ko yarjejeniya dake tsakanin ɓangarorin biyu.

A irin wannan auren akan samu kaga an aurawa yarinya sa’an mahaifinta ko makamancin haka.

AUREN KASHE WUTA:

Wannan auren yakan kasance ne bayan miji ya saki mace saki uku, alhali kuwa suna son junan su, kawai sakin yazo ne bisa wani dalili na sakin baki ko kuma wata matsala da makamantansu.

Sai ta auri wani mutum daban kuma ta nemi lallai ya sake ta saboda ƙudirinta na komawa gidan tsohon mijinta,

To, auren nan da tayi, da ƙudurin cewa zata sanya sabon mijin ya saketa ta dawo wurin mijinta na da, wannan shine ake cewa dashi auren kisan wuta.

AUREN SADAKA:

Shi auren sadaka aure ne da ake bayar da yarinya ga wani, saboda wani aiki da yayiwa iyayenta, ko kuma irin sadakar da malamai ke bawa almajiransu kasancewar kamun kansu da kuma soyayyar da malamin ke musu.

Sannan wasu lokutan yakan faruwa ne idan yarinya ta girma bata samu saurayi ba saboda wasu dalilai ko kuma haka kawai.

Wasu lokutan akanyi auren sadaka don gudun kada yarinya ta jawo wa iyayenta abin kunya saboda kasancewar ganin canji a cikin halayyar ta.

AUREN ƊAUKI SANDA:

Auren ɗauki sanda aure ne da Mutum ya kan auri matar dake zaune a gidan kanta, yakan iya zama mijinta ne ya mutu ya bar gidan kokuma ita ta gina kayanta.

Sai ya kasance bazata iya zuwa gidan don yin wannan zaman auren ba, kasancewar wasu dalilai daga wurinta

Haka kuma shima ba zai iya zuwa gidanta ya zauna ba. Sai dai ya riƙa zuwa cen gidanta yana kwana idan ya gama abin da yake sai ya fita.

AUREN DIBE HAUSHI:

Wannan aure akanyi shi Idan matar mutum ta dame shi da fitina ta hanshi sakewa masifar yau daban ta gobe daban, sai ya yanke shawarar aurar wata mace mai kyau ko dukiya ko ilimi domin hushe takaici. 
Kafar Intanet Ɗin Da Za Ku Samu Dubbannin Rubuce-Rubuce Game Harshe Da Al'ada Da Adabin Hausawa

Aminu Musa 
26082023
Ranarhausataduniya

Post a Comment

0 Comments