Ticker

6/recent/ticker-posts

Zule-Zuleyya - Daga Littafin WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.

Zule-Zuleyya

Bayarwa: Iya ku ɓoye ‘ya’yanku ga abin mafarki,

Amshi: Ga Zule ya shigo.

 

Bayarwa: Zule-zuleyya mai idon sakaina,

Amshi: Ga Zule ya shigo.

 

Bayarwa: Kura ta leƙa ta ga babu dama,

Amshi: Ga Zule ya shigo.

 

Bayarwa: Damisa ta leƙa ta ga babu dama,

Amshi: Ga Zule ya shigo.

 

Bayarwa: Ɓauna ta leƙa ta ga babu dama,

Amshi: Ga Zule ya shigo.

 

Bayarwa: Gwanki ya leƙa ya ga babu dama,

Amshi: Ga Zule ya shigo.

 

Bayarwa: Zaki ya leƙa ya ga babu dama,

Amshi: Ga Zule ya shigo.

 

Bayarwa: Giwa ta leƙa ta ga babu dama,

Amshi: Ga Zule ya shigo.

Danda Dokin Kara

Bayarwa: Assalamu alaikum kun yi baƙo,

Amshi: Ga danda dokin kara.

 

Bayarwa: Masu gidan nan kun yi baƙo,

Amshi: Ga danda dokin kara.

 

Bayarwa: Sai ku ban kaji bakwai daƙwale,

Amshi: Ga danda dokin kara.

 

Bayarwa: Da tuwon shinkafa da miya ja,

Amshi: Ga danda dokin kara.

 

Bayarwa: Sai ku ban soyen nama na rago,

Amshi: Ga danda dokin kara.

WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Post a Comment

0 Comments