Ticker

6/recent/ticker-posts

Yabo Da Faɗakarwa A Cikin Wasu Waƙoƙin Babangida Kakadawa

Cite this article as: Kurawa, H.M. & Abubakar, B. (2023). Yabo Da Faɗakarwa A Cikin Wasu Waƙoƙin Babangida Kakadawa. Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture, (2)2, 152-158. www.doi.org/10.36349/tjllc.2023.ɓ02i02.017.

Halima Mansur Kurawa
Lambar Waya: 08069611163
Email: hmkurawa72@gmail. com
Sashen Nazarin Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya, Gusau 

Bilyaminu Abubakar
Email: bilyatask1@gmail. com
Sashen Nazarin Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya, Gusau

Tsakure

Wannan binciken yana da manufar fito da yabo da faɗakarwa da makaɗa Babangida Kakadawa ya zuba a matsayin wasu turakun waƙoƙinsa. Kakadawa makaɗi ne mai tsinkaye cikin rayuwar Hausawa, don haka ya gina turakun faɗakarwa da nufin yin gargaɗi da nasiha da wayar da kai gami da jan hankali. Daga sakamakon binciken an fahimci wasu waƙoƙinsa sun haska yadda wasu al'adun Hausawa suke, misali, waƙarsa ta 'gidan haya', da waƙar " ina son in yi aure". An kuma duba irin salon da ya bi don faɗakarwa. Waƙoƙin da aka yi sharhinsu don fito da yabo da kuma faɗakarwar sanannu ne ga jama'a. An samu waƙoƙin ta hanyar saurare daga kaset, da kuma wasu littattafai. An ɗora aikin a kan ra'in waƙar Baka Bahaushiya (WBB), inda aka duba wasu turaku a waƙoƙin baka na Babangida Kakadawa. Binciken ya gano shi makaɗi ne da ya ƙware wajen zaɓo kalmomi na yabo da suka dace.

Fitilun Kalmomi: Adabi, Waƙoƙi, Yabo, Faɗakarwa

1. 0 Gabatarwa

Waƙar baka a wurin Hausawan ƙasar Hausa, aba ce da ta jima sosai tana rayuwa tana bunƙasa har zuwa yau. A cikin ta ne mawaƙa ke bayyana al’amuran da suka shafi rayuwar Hausawa har suna haɗawa da lele (yabo), ko faɗakarwa (ilimantar da al’umma). Waƙoƙin Babangida Kakadawa suna ɗauke da irin waɗannnan turaku: turken yabo da na faɗakarwa, su ne madubin dubawa a wannan maƙala. Saboda haka ne, ake hasashen muƙalar ta share fage, ko kuma ta zamo ƙari, wanda aka ce, ya fi ƙara a fagen karatu.

1. 1 Ma’anar Waƙa

Masana irin Gusau, (2003), da ‘Yar’aduwa, (2010), da Bunguɗu, (2016) da sauransu, sun ce wani abu a kan waƙa. Gusau, (2003: xiii), ya naƙalto, Yahaya, (1976: 1) ya ce, “Waƙa magana ce ta fusaha a cure wuri ɗaya a cikin tsari na musamman.” Yayin da ‘Yar’aduwa (2010: 75), ya ce, “Waƙa magana ce aunanniya wadda ake rerawa. ” Inda a wurin Bunguɗu, (2016: 3) cewa ya yi: “Waƙa tana nufin ƙololuwar hikima da basira da hazaƙa da fasaha ta sarrafa kalmomi bisa ga tsari madaidaici tare da amfani da baiti ko ɗiya a cikin rauji mai daɗin gaske domin nishaɗantarwa tare da jan hankalin mai sauraro ga abin da ake isarwa na saƙo a gare shi. ” Duka dai a cikin wannan gaɓar, masanan da aka kawo a sama sun kasa waƙa zuwa kashi biyu biyu kamar haka:

1. Waƙar Baka.

2. Rubutacciyar Waƙa.

Kacokan wannan aiki yana gudana ne a ƙarƙashin rukunin waƙar baka wadda masana kamar Yahaya (2007), da Gusau (2014), suka bayyana ma’anarta:

Yahaya (2007: 21) a littafin ‘Darussan Hausa Na 1’, ya ce, “Waƙar baka zance ne sarrafaffe, aunanne wanda ake aiwatar da shi ta bin hawa da saukar murya, mai zuwa gunduwoyin layuka da ake rerawa bisa wani daidaitaccen tsari, wani bin har tare da kiɗa”. Ko a wurin Gusau, (2003: XIII) da (2011: 2) ya ce: “Waƙar baka, wani zance ne shiryayye cikin hikima da azanci da yake zuwa gaɓa-gaɓa bisa ƙa’idojin tsari da daidaitawa, a rera cikin sautin murya da amsa-amo na kari da kiɗa sau da yawa kuma a tare da amshi. ”

1. 2 Ma’anar Turke

 A Ƙamusun Hausa, (2006: 446) an bayyana turke da 'wani guntun itace da ake kafawa don ɗaure dabba a jikinsa'. Gusau, (2003: 28) ya ce turke "Shi ne abin da waƙa take magana a kansa wanda ya ratsa ta tun daga farkonta har zuwa ƙarshenta. Wato dai turke shi ne ainihin manufar waƙa". Har ila yau Gusau, (2008 370) ya bayyana turke da saƙon da makaɗi yakan zaɓa ya gina waƙarsa, ya tauye kansa da kansa ya zuba ɗiyanta bisa wasu zaɓaɓɓun kalmomi da za su doshi wata babbar manufa ɗaya.

Duba da waɗannan ma'anoni za mu ce turke dai shi ne ainihin manufar waƙa, wato abin da waƙa take magana a kansa.

1. 3 Ma’anar Yabo

A Ƙamusun Hausa, (CNHN 2006: 476) an bayyana, “Yabo shi ne faɗar wata kalma mai daɗi ga wani mutum da ya aikata wani kyakkyawan abu”. A wurin Ibrahim, (1983: 9) cewa ya yi, “jigon yabo, jigo ne da a cikinsa makaɗi yakan yabi ubangidansa da ambaton darajar kakansa, da jaruntaka da kuma alheri”. Ko a wurin Zulyaddaini, (2000: 45) bai ƙi abin da Ibrahim ya ce ba, sai dai ma’anar da ya kawo, ta fi tsawo, inda ya ce: “Mawaƙan baka, kan rera waƙa mai ɗauke da wannan jigo na yabo. Mawaƙan kan yi haka ne ta hanyar fito da wasu kyawawan halayen mutumin da suke yi wa waƙa, suna yaba masa. A wasu lokutan ma sukan koma su ɗebo ta tun daga tushe domin waƙa ta yi zaƙi, tare da ƙara armashi. ”

1. 4 Ma’anar Faɗakarwa

Ƙamusun Hausa, (CNHN 2006: 129) an ambaci faɗakarwa da farkarwa ko lurarwa ko ankararwa da al’umma”. Auta, (2017: 25) ya ce faɗakarwa tana nufin nusar da mutum a kan abubuwan da ya sani tun tuni amma ya manta da su. Don haka ne ake yi masa tuni da yi masa hannunka-mai-sanda don ya dawo ya yi la'akari da su. Zulyadaini, (2000: 91) ya ambaci, “jigon faɗakarwar da sunan jigon wayar da kai” in da ya ce, “Mawaƙan baka kan rera waƙa mai ɗauke da wannan jigon, domin su wayar wa jama’a kansu kan wani abu da gwamnati ta ƙirƙiro. A lokuta da dama idan hakan ta faru gwamnatoci ne ke sanya su mawaƙan su nusar da jama’a kan wani al’amari. Dalilin wannan kuwa shi ne, domin su mawaƙa ne suka fi kusa da jama’a. Haka kuma su ne za su iya sadar da komai ga al’ummar Hausawa cikin sauƙi da kuma hanzari. ”

2.0 Ra’in Bincike

Domin ɗora wannan bincike ga sahihiyar hanya ne, ya sa aka yi amfani da Ra'in Tarken Wsaƙar Baka Bahaushiya (WBB) wadda Gusau ya samar a (1993). Haka kuma a Gusau, 2011 da Gusau 2015 an faɗaɗa bayani. A cikin ra'in an yi bayanin turke da tubulan ginin sa.

 3.0 Taƙaitaccen Tarihin Babangida Kakadawa

Manazarta da suka haxa da Gusau (2016) da Abubakar (2006) da ma wasu, sun ce sunan makaxin na yanka Abdurrahman. An haife shi a qofar Jange garin Gusau, a jahar Zamfara akwai savani ga ranar haihuwarsa, Abubakar (2006) ya ce an haife shi a shekarar 1981 a yayin da Gusau (2016) ya ce an haife shi a shekarar (1972). Babangida Kakadawa gadon kixa ya yi ba haye ba, mahaifinsa Usman makaxin Duman Girke ne a garin Gusau, ya kuma yi kixan Kalangu da banbaxo, haka ma yayan Babangida mai suna Alhaji Sani Kakadawa makaxin Kalangu ne, kuma daga wajensa ne Babangida Kakadawa ya qware da kixan kalangu da waqa, har ya zamo mataimaki na musamman cikin ayarinsa. (Abubakar 2006)

Babangida Kakadawa soma sha’awar kixan kuntigi saboda qaunar da hyake wa makaxa Alhaji Adamu Xanmaraya Jos da yawan sauraren waqoqinsa, wannan ta bashi dama ya qware wajen kwaikwayon muryarsa har wasu basa iya rarrabewa tsakaninsu.

Gusau (2016) da Abubakar (2006) sun ce Babangida Kakadawa shi ne halifan Marigayi Alhaji Adamu Xanmaraya Jos har an sahale masa yana iya maimaita rera wasu waqoqinsa a bisa wasiyyar da shi marigayin ya yi.

Makaxa Babangida makaxin jama’a ne, ya yi wa Sarakuna da attajirai da malamai da ‘yan siyasa waqa, haka kuma ya yi waqoqin sha’awa da na soyayya.

Babangida Kakadawa yana da aure da ‘ya’ya biyar.

4.0 Nazarin Turken Yabo

Babangida Kakadawa ya shirya wasu waƙoƙinsa a kan turken yabo inda ya yi amfani da kalmomin da suke ɗaga daraja da fifita mutum tare da kwarzanta shi da faɗin wsuu halaye nasa kyawawa da dai dukkan abin da yake ɗaukaka ce ga ɗan'adam. Kamar yadda ya yi wajen yabon Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammadu Sa’ad, a waƙar ‘Murna Mukai’ ta biyu wadda ya yi masa cikin bukukuwan cikarsa shekaru biyar kan karagar mulki da ya gudana a ranar (4, Nuwamba-2011), in da ya ce:

 Tauraron duniya jikakan Shehu,

 Mai ba Musulmi nai shawara,

Turbar kakansa ita ce ta tsira,

Ba duniyar nan ba ko ma ƙiyama,

Ko waƙ ƙi bin sanku rainai sai yai baki,

A sa shi jahannama can ai mai bida.

 

 Hadari mai lulluɓe duniya,

 Rimi mai kere itace,

 Mai ɗai ba zai ƙi yin biyu ba,

 Kanal Sada dut nan gidan,

 Kai ɗai kai zara,

Ga ka kana Kanal ka yi Sultaniya,

 Ka zan Sarkin Musulmin Daular Usumaniyya,

A yau komi ya yi kyau.

 

Jikan Abdullahin Gwandu,

Allah Yai ma tsari,

Mu fata mukai.

In, jikan Sarki Hassan Ɗanmu’azu,

Halinsa halin waliyan farko yake.

 

A nan mawaƙin ya yabi Mai Alfarma Sarkin Musulmi ta hanyar yi masa kinaya da kalmomin 'tauraro' don ya nuna ɗaukakarsa da hasken mulkinsa. Kalmar 'hadari' kuma don ya alamta fatan da jama'a suke yi masa na samun alhairai masu yawa da kare su daga abin da zai cutar da su. Kalmar 'rimi' kuwa don makaɗin ya nuna fifikon da yake da shi a kan saura jama’a ne. Wani yabon shi ne ya ambaci nasabarsa ta danganta shi da kakaninsa don hidimar da suka yi wa addinin Musulunci. Kuma cewa da ya yi "Ga ka kana Kanal. . . "Shi ne matsayin da yake a kai, na aikin soja, lokacin da aka naɗa shi 'Sarkin Musulmi' (Sultan). A wani ɗan waƙar, yabo ya yi ta fuskar ambaton nasaba da iya mulki da yin kyauta da rashin ɗaukar wargi ga mai martaba Sarkin Ƙayan Maradun Alhaji Garba Muhammad Tambari, inda yake cewa:

Haske mai korewad duhu,

Ruwa mai wankewaf fari,

Jikan Usuman ƊanFodiyo,

Wannan magana hakanan take,

Ɗan kwaɗɗo aka taki lafiya,

Kowat taki kunama ya sani. ”

 

Kalmomin 'haske' da 'ruwa' kinaya ce, an alamta Sarkin Ƙayar Maradun ne, suna nufin mutum mai kyauta ta yanke talauci. Sai kuma ya jingina nasaba tasa ga Shehu Usmanu ɗan Fodiyo wanda ya jaddada addinin Musulunci. Don ya yaba masa ta fuskar shirin ko ta-kwana shi ya sa ya ce: " Kowat taki kunama ya sani". Wannan ya yi kama da wani ɗan waƙa na makaɗa Musa Ɗanƙwairo ya yabi Baura Ɗanmaliki ta fuskar yin kyauta wurin da ya ce:

". . . in kana biɗar sutura,

A wajen Baura samowa kake,

Yaro in kana biɗar mari,

A wajen Baura samowa kake. "

 (Gindin waƙa: Jiƙan Musa Ɗanmaliki.)

 

A waƙar da ya yi wa Sarkin Katsinan Gusau kuma ga abin da ya ce ta fuskar yabon sa kan asali dangane da matsayin da Allah ya yi wa kowa kamar haka:

 

“Haihuwar sarauta jari,

Talakka ba ya haihuwar ɗan sarki,

Sai dai ya haihi mai masa noma,

A ko faskare a samu abinci,

Mai asali bai kai ba kamatai,

Kaka naka shi ya sara Gusau,

Ibrahima Bello mi kaka sauna?”

 

Babu shakka kowa da irin ɗaukakar da Allah ya yi masa, ɗaukakar da aka yi wa masu mulki ba iri ɗaya ce da wadda aka yi wa talaka ba. Idan aka dubi abin da makaɗin ya faɗa za a fahimci hakan domin ya aje talaka wurin da Allah ya aje shi, sannan kuma bai wulaƙanta shi ba. A gefe ɗaya kuma, ya bar masu sarauta a daidai bagiren da Mai duka ya aje su.

 

5. 0 Nazarin Turken Faɗakarwa

 

5. 1 Faɗakarwar da ta Shafi Gargaɗi

 Ma'anar gargaɗi kamar yadda aka fassara a Ƙamusun Hausa (CNHN, 2006: 159) shi ne 'Jan kunne ko yin kashedi ko horo'. Wato a nusar da mutum aikata abin da zai yi masa amfani ko nuna hatsari don ya kauce masa. Babangida Kakadawa ya yi irin wannan faɗakarwa ta gargaɗi a wasu waƙoƙinsa. Duba wannan gindin waƙa:

"Gidan nan ba gida ba ne, matsala dai ne zaman haya".

Gargaɗi yake don faɗakarwa ga mazauna gidan haya cewa ba gidan da za a zauna a shatanke ba ne, musamman da nuna wasu suna hayar ne ba don rashi ba. Dubi abin da yake cewa:

"Mai ban takaici ɗan zaman haya,

 Kuma ya yi gije a cikin gidan,

 Wanga lalaci ne mai yawa,

Kai tashi gidan nan ba na zama ba ne,

Matsala dai ne gidan haya,

Gidan nan ba gida ba ne,

Matsala dai ne gidan haya.

Wanda yana a gidan haya ga ya da ƙarfi,

Ga ya da ƙarfe ga ya da harka wadda yake yi,

Amma ya raɓe a gidan haya. "

 

Makaɗin ya ji takaicin mutumin da yake da ƙarfi da ƙarfe (kuɗi), amma bai mallaki muhalli ba. Sai ya kira abin da lalaci, ya kuma nuna a gidan hayar maa raɓe yake, tun da ba nasa ba ne, baya ga tarin matsalolin da yake fuskanta. A wani wuri ya sake irin wannan gargaɗi ga mutumin da yake da mata huɗu, kuma kowace a gidan haya. A lissafi iyalinsu mutumin har shi da kansa su ashirin da huɗu ne (24) ga kuma ciki da za a haifa.

 

" Akwai ɗan ragaitar zaman haya,

Shi ne mai mata huɗu duk a gidan haya,

Gidan su Bango yana gabas

Ga 'ya‘yanta guda shidda,

Gidansu Delu yana kudu,

Ga ‘ya‘yanta guda shidda,

Gidansu Gwamma yammaci,

Ga ‘ya‘yanta guda shidda,

Ga amarya Turai nan kuma,

Tare da gogan su duka,

 Ita ko ga goyo ga ciki, 

Wannan matsala ƙaƙa take?

 

Ku duka kun ribce a gidan haya,

Malam ko noma za ka yi,

Sai ka tanadi rumbu don hatsi,

Ya za ka yi mata har huɗu?

Kuma ko wace na a gidan haya?

Wanga lalaci ne mai yawa,

Kai tashi gidan nan ba gida ba ne,

Matsala dai ne gidan haya. "

A wani wuri kuma yace:

 “Ɗan zaman haya mai ban tausaai,

Mai ban takaicin ɗan zaman haya,

Ɗan zaman haya mai ban tausai,

Shi ne wanda yana a gidan haya,

Ba ya da harka wadda yake yi,

Ga iyali sun yi mai yawa,

 

 A nan Mawaƙin yana ƙoƙarin ya nuna, zama a gidan haya ga wasu, tamkar rashin yin amfani da karin maganar nan ne da ake cewa, ‘ido ba saci amma sun san ƙima’ ga ɗawainiyar biyan haya kuma da faman ya wanyin aure-aure babu lissafa wa saboda haka sai mawaƙin ya biyo da abinda ake cewa, ‘da rashin kira karen bebe ya ɓata’.

 

5. 2 Faɗakarwa don wayar da kai:

Makaɗin ya yi ƙoƙari don ya wayar da kan waɗanda ba su fahimci matsalar zama a gidan haya ba, musamman zama irin na haɗaka. In da yace:

"In kana a gidan haya,

Matarka ba ta da walwala,

‘Ya‘yanka ba su da walwala,

Baƙonka ba ya da walwala,

In kai magana a ƙadam maka. "

Wannan faɗakarwa ce don mazaje su sani iyalinsu da baƙinsu ba su da walwalar rayuwa a tsari irin na zaman haya. Wannan kuwa yana iya faruwa ko daga abokan zaman haya, a zama na haɗaka wanda galibi ake samun rashin jituwa dalilin sa ido ko tsana ko ƙyashi da hassada ko kuma don wasu dokoki da su masu gidan hayar ke gindayawa da za su iya zama tarnaƙi ga jin daɗi da walwalar iyali. Kamar yadda a wani wuri yace:

 

 “Kai gaka gidan haya, 

Wancan ga shi gidan haya,

Waccan ga ta gidan haya,

Ku duka kun gamu kun haɗe,

In In kai kana da dangana, 

Ƙila wancan baya da dangana. "

A nan kuma sai yace:

" Matsalar gidan haya, 

Ko da kun kai ku tara, 

Makewayinku guda ake, 

Matar wancan ta shiga,

Matar wannan na jira,

Kai ma gaka kana jira,

Shi ne matsalar zaman

 

 Matsalolin zama a gidan haya ba za su lissafu ba, makaɗin ya faɗi rashin dangana da amfani da makewayi guda komai yawanku, wanda hakan yana iya saɓawa shari'a musulunci da tsari na al'adar zamantakewa. Wajibi magidanta su fahimci irin halin da iyalinsu ke shiga a gidan hayar da suke zaune.

5.3 Faɗakarwa Da Ta Shafi Nasiha Da Jan Hankali

Akwai faɗakarwar da ta shafi nasiha da jan hankali don mutum ya fahimci abin da yake shi ne daidai, shi makaɗa Babangida Kakadawa ya yi a nan. In da ya yi nasiha gami da jan hankali don jama'a su tashi, su yi fafutukar mallakar muhalli. A ƙoƙarin yin hakan ya buga misali da rayuwar wasu halittu. Ga abin da yace:

"Tun farko asalitan,

Duk tsuntsun da yake sama,

Ya gina gida nai ya shige,

Ƙwarin da suke ruwa,

Kowane ya yi gida nasa ya shige,

Hatta ƙwarin da suke tudu,

Kowane ya yi gida nai ya shige,

Diba misali tun a zanzaro

Gashi dai abu ne ɗan ƙanƙane

Ya je daji ya ja ƙasa,

Ya e bo(ɗebo) ruwa nai yahaɗa,

Yaginagidanasayanashiga,

Tokai matsayinka na ɗan’Adam,

Ya zaka tsaya agidanhaya?

 Kaitashigidannanbagidabane,

Matsaladainegidanhaya".

A wata waƙar ga abin da yake cewa:

“Ina son in yi aure,  Ina son auren Bazamfara,

Ni Babangida,

Ita tana ƙaunata ni ina ra’ayinta,

Ubanta sai yac ce a’a,

Ita tana ƙaunata ni ina ra’ayinta,

Ubanta sai yac ce a’a,

Wanda ba ta ƙauna,

Wai da shi za a yi aure,

To don Allah a daina auren dole,

Saboda auren tilas,

Ka sa ɗiya yawon banza.”

Gindin waƙa: Ina bakin kogi,

Kada na dibi na.

 

Har ila yau, wata matsalar da ta tuzgo, kuma take son zamowa ruwan dare ita ce kwaɗayin sai mai kuɗi iyaye za su aura wa 'yarsu koda ita yarinyar ba ta so. Wannan shi ne auren tilas da ke saka 'ya shiga yawon bariki. Kamar yadda makaɗin ya ambata, don ya faɗakar ta hanyar yin nasiha ga iyaye.

A wata waƙar daban nuna irin halin da shi kansa ya shiga da aka raba shi da yarinyar da yake so take so sa, saboda shi talaka ne. Yana cewa:

“Yau na yi tagumi na rame,  Ban iya cin komai, Allah koro !  Allah koro da masoyyiya ta,  Rashin ganin ta na rame,

Ba na iya cin komai,  Yau ga ɗan talakawa,  Yana son ‘yar mai kuɗɗi, ”

Abin da duk ya haifar da hakan, bai rasa nasaba da bijire wa kyawawan al’adun neman aure, irin na dauri da aka yi watsi da su a cikin wannan zamani, kamar yadda mawaƙin ya sake ambata:

“Amma yanzu mun tsiro,

Al’adummu ma su son lalata mu,

Don yau ba a baka aure ba kuɗɗi,

A su dai sun fi son su baiwa,

Mai taƙama da adda a cikin gida,

Yana datse kanu,

Sannan za su bashi mata kyakkyawa. ”

Don haka sai ya faɗakar tare da jan hankali ga iyaye :

“Iyaye ku duba ku hango matsalar aure,

Malamai suna ta tambihi,

Kuma kun ƙyale kun yi shu,

To ku sani duniya a ke tuba,

Lahira fa ba tuba,

In ‘yar ku tai cikin shege,

Ba za ku ga Manzo ba,

Sai dai kuga walakiri ya zo da kulake nai.”

6.0 Kammalawa

Wannan muƙala kamar yadda bayanai suka gabata, wani yunƙuri ne na hasko turken Yabo da na Faɗakarwa a wasu daga cikin waƙoƙin, mawaƙi Babangida Kakadawa mai kiɗa ƙanin Sani, kuma halifan marigayi Alhaji Dakta Adamu Ɗanmaraya, Jos. Wannan takarda ta duba ma'ana waƙa da kuma ma'anar Yabo da Faɗakarwa, sai kuma aka bayar da misan yabo da faɗakarwa a cikin wasu waƙoƙin makaɗin. Wannan ya haɗa da yin gargaɗi da wayar da kai da kuma yin nasiha da jankali ga al'umma.

6.1 Sakamakon Bincike

Wannan muƙala kamar yadda bayanai suka gabata a sama, ta yi tozali ne da turakun yabo da faɗakarwa a wasu daga waƙoƙin Babangida Kakadawa. Dangane da haka ne aka gano wasu ɓoyayyun saƙonni kamar haka:

a.       An gano a zaman haya, akwai matsalolin tattare da zama a gidan haya, wasu daga cikinsu na ɗan hayar ne, wasu kuma na abokan zaman hayar ne.

b.       Haka kuma an gano wata ɗabi’a da wasu Hausawa ke aiwatarwa ta kiyashiɗauki abin da ya fi ƙarfinka, ma’ana mutun na zaune a gidan haya, ba tunaninsa ya yi ƙoƙarin mallakar gidan kansa ba, maimakonhaka sai ya yi ta ƙara aure, kuma ya yi ta haifar ‘ya’yan da baya iya tarbiyarsu balantana iya ɗaukar takalihunsu matan, da a ƙarshe sai a sami matan cikin wahala, su ma ‘ya’yan ciknin wahala daga nan saisu zamo wa al’umma alaƙaƙai.

c.        An gano wata ɗabi’ar kwaɗayin wasu iyaye sun fi son baiwa mai kuɗi auren ‘ya’yansu mata, ba tare da son 'ya'ƴan ba, hakanke sa su gudu daga gidan auren, sushigakaruwanci.

Manazarta

1.       Abubakar, A. T. (2015). Ƙamusun Harshen Hausa. Zaria: Northern Nigeria Publishing Company. L. T. D

2.       Abubakar, B. (2006). Babangida Kakadawa da Waƙoƙinsa. Ba’a wallafa ba.

3.       Ado, A. (2019). Ra’o’in Bincike Kan Al’adun Hausawa. Katsina: Government PrintingPress, Katsina State, Nigeria.

4.       Ainu, H. da Wasu. (2007). Alu Ya Gode ! Amal Printing Press.

5.       Ainu, H. da Wasu. (2016). Alu Na nan Dai. Zaria: Published and Printed Ahamadu Bello University Limited, Kaduna State, Nigeria.

6.       C. N. H. N. (2006). Ƙamusun Hausa. Kano: Wallafar Cibiyar Nazarin Harsunan Najeriya, Jami’ar Bayero, Jahar Kano.

7.       Bunguɗu, H. U. da Wani. (2016 ). Waƙa Zancen Hikima. Gusau: Nasara Printer CanteenArea, Zamfara State.

8.       Ɗangambo, A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa Da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa. An Shirya a Sashen Buga Littattafai na Kamfanin ‘Triumph’.

9.       Ɗangambo, A. (2007). Ɗaurayar Gadon Feɗe waƙa. Ammana Publishers Limited.

10.    Ibrahim, M. S. (1983). Abokin Fira 2: Kowa Yasha Kiɗa. Nigeria: Published by Longman, Plc.

11.    Gusau, S. M. (1993). Jagoran Nazarin Waƙar Baka. Gusau: Benchemark Publishers Ltd.

12.    Gusau, S. M. (2008) Waƙoƙin Baka A Ƙasar Hausa: Yanaye-yanayensu da Sigoginsu. Kano: Benchemark Publishers Lt d.

13.    Gusau, S. M (2011). Waqar Baka Bahaushiya. Kano: Century Research Publishing Limited.

14.    Gusau, S. M. (2003) Jagoran Nazarin Waqar Baka. Kano: Benchmark Publishers Limited

15.    Gusau, S. M. (2014). Waƙar Baka Bahaushiya (Oral Songs). Kano: Cibiyar NazarinHarsunan Najeriya, Jami’ar Bayero, Inagural Lecture Serial No. 14.

16.    Gusau, S. M. (2016). Makaɗa Da Mawaƙan Hausa Littafi Na Biyu. Kano: Century Reseach and Publishing Ltd, Nigeria.

17.    Sarɓi, S. A. (2007). Nazarin Waƙar Hausa. Kano: Samarib Publishers.

18.    Sa’id, B. (1982). Dausayin Soyayya. Zaria: Published by Northern Nigeria Publishing, Gaskiya Bulding Comparny Limited.

19.    Yahaya, I. Y. da Wasu. (2001). Darussan Hausa 3. Universty Press Plc.

20.    Yahya, A. B. (1997). Jagoran Nazarin Waƙa. Kaduna: Firsbas Media Service.

21.    Yahya, A. B. (2001). Salo Asirin Waƙa. Kaduna: Firsbas Media Service.

22.    ‘Yar’Aduwa, T. M. (2010). Jagoran Nazarin Rubutaccen Adabin Hausa. HEBN Pulishers Plc.

23.    Zarruƙ, R. M. da Wasu (2006). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Littafi Na Biyu. Universty Press Plc.

24.    Zulyadaini, B. da Wani. (2000). Nazari Kan Waƙar Baka Ta Hausa. Zaria: Gsakiya Corporation. 

Post a Comment

0 Comments