Cite this article as: Haruna, A., Idris, Z.B. & Yankara, M.M. (2023). Nazarin Sauye-Sauyen Wasulan Karin Harshen Katsina Da Maraɗi. Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture, (2)2, 143-151. www.doi.org/10.36349/tjllc.2023.v02i02.016.
Auwal Haruna
07051012207
aharuna3@fudutsima.edu.ng
&
Zahraddeen Bala Idris
08036793221
zbidris@fudutsima.edu.ng
&
Muhammad Musa
Yankara
08062367496
mymuhammad@fudutsima.edu.ng
Department of Hausa, Federal University Dutsin-Ma, Katsina State, Nigeria
Tsakure
Bincike ya nuna
cewa, harshen Hausa na da kare-kare masu yawa, daga cikinsu har da
Karin harshen Katsinanci Bello (1962). Kazalika, a karin harshen Katsinanci, Sakamakon yawan al’umma da ke amfani da shi da kuma faɗin ƙasa da Katsinanci
ya mamaye ana da hasashen cewa akwai ƙananan kare-karen harshe, ciki har da karin Maraɗi. Domin tabbatar
da haka an yi amfani da hanyar tattara bayanai ta ganawa da lura ta ƙwaƙƙwafi domin samun bayanan da za su tabbatar
da haka. Haka kuma, an yi amfani da ra’in tsarin sautin tsirau wajen tantance
bayanan da aka samu kamar yadda Chomsky da Halle (1968) suka yi amfani da shi a
littafinsu na (Sound Pattern of English) (S.P.E). Kamar yadda aka yi
hasashe da farko binciken ya tabbatar da cewa, an samu sauye – sauye tsakanin karin harshen Katsinanci a birnin
Katsina da na birnin Maraɗi a wasu wurare da suka haɗa da sauyawar baƙi da wasali, saƙala sauti, shafe ƙwayar sauti, musayar gurbi, kore
raunanar baƙi, kore ganɗantawa da kuma kore hanɗantawa. A
wannan takarda an yi ƙoƙarin kawo sauye-sauyen da
suka shafi wasulla.
Fitilun
Kalmomi: Karin Harshe, Walwalar Harshe, Harshen Rukuni, Wasula
1.0 Gabatarwa
Masana
harsunan duniya sun karkasa harsuna zuwa kashi biyar, domin samun sauƙin nazarinsu da kuma fahimtar asali da dangantakar kowannensu. Daga cikin
waɗannan manyan harsuna guda biyar
akwai wanda aka kira a harshen Ingilishi da (Afro-Asiatic) wato kakan harsunan
Afirika da Asiya. Har wa yau, daga cikin waɗannan harsuna ne aka sami harshe wanda ya zama uba ga harsunan yankin
tafkin Chadi (Proto-chadic) wato harsunan mutanen da suke zaune kusa da tafkin
Cadi (Chadic languages) da kewayensa, kafin su watsu zuwa sauran sassa na
yammacin Sudan. Bunƙasa da ci gaban wannan harshe, ya
haifar da rarrabuwarsa zuwa manyan rukunai biyu wato rukunin A’ (Chadic A) da kuma rukunin ‘B’ (Chadic B).
Sakamakon nazarin masana harsuna, ya danganta wasu harsuna kamar harshen
Bolanci da Angas da Karekare da harshen Hausa da sauransu a matsayin misalai na
harsunan da aka kira (Chadic Languages),
Hausawa da harshen Hausa sun kasance suna rayuwa a wani wuri da masana
tarihi suka kira ‘Sudan ta Tsakiya’. Bahaushe yana wannan wuri yana rayuwa tun
shekaru da dama da suka wuce, shi kaɗai a bisa tsari na bin nau’o’i na
rayuwa da suke da dangantaka da al’adarsa da kuma adabinsa. Kuma a ƙoƙarin tafiyar da waɗannan abubuwa biyu, wato al’ada da adabi duk da harshe ake amfani wajen
gudanar da su daidai da tsarin zamantakewa. Masu nazarin harsuna sun yarda da
cewa, harsuna sun bambanta da junansu, haka nan ma suka ƙara da cewa, harshe abu ne da yake ci gaba, kamar yadda jikin Ɗan’adam yake ginuwa ko haɓaka yau da kullum. A harshe ɗaya, sakamakon yawan Al’ummomi da
ke amfani da shi, yakan bunƙasa ya kai wani mataki da akan iya
fahimtar wasu ’yan sauye-sauye da ke wakana a cikin harshen. Irin waɗannan sauye-sauye su ne sannu a hankali sukan kai wani adadi na lokaci da
akan iya danganta su da wani karin harshe. Kuma ana iya fahimtar wannan sauyi
ta fuskar tsarin sauti ko ƙirar kalma ko kuma ginin jumla.
Don haka, a wannan takarda za a yi ƙoƙarin fito da sauye-sauye ƙwayoyin sautikan wasulla a tsakanin Karin harshen birnin Katsina da
birnin Maraɗi.
1.1 Dalilan Bincike
Dalilan da suka assasa wannan bincike sun haɗa da cewa, tun kafin zuwan Turawan mulki ƙasar Hausa, ƙasar Katsina ta ƙunshi manyan garuruwa cikinsu har da Maraɗi, wato al’umma ɗaya ce, masu gudanar da mu`amala
iri ɗaya, kuma suna tarayya a karin
harshe ɗaya. Amma a sakamakon zuwan Turawa
ƙasar Hausa, sai ƙasar Katsina ta rabu gida biyu: Katsina a yankin Nijeriya (Jahar Katsina)
da kuma Katsina a yankin Nijar, wadda aka fi sani da Maraɗi a yau. Saboda haka, a yau wannan ƙasa ta Katsina ta kasu gida biyu; kuma kowane ɓangare daga cikin waɗannan ɓangarori a kan ji aukuwar sauye-sauyen lafazin magana, da
bambance-bambance ta fuskar tsarin mulki, kuma mu`amala tsakanin waɗannan al’ummomi ta ragu. An kuma sami bambance -bambance ta fuskar baƙin al`adu da tasirin bambancin tsarin ilimin boko da tsari na mulkin
siyasa. Saboda haka ake da zimmar fito da waɗannan yan sauye-sauye da suka shafi nazarin harshe zalla.
A sakamakon ɗaukar dogon lokacin rabuwar waɗannan al’ummomin biyu, tattare da
wannan bambance-bambance a tsakanin waɗannan al’ummomin na al’adu, ya sa
a mahanga ta wannan takarda, ake da tunanin cewa, shin ko karin harshen
Katsinanci a waɗannan al`ummomi yana nan yadda aka
san shi? Ko kuwa an sami wasu sauye-sauye. Bisa ga waɗannan dalilai ne takarda ke ƙoƙarin gabatar da wannan gudunmuwa ta sauye-sauye wasulla a tsakanin Karin
harshen birnin katsina da na Maraɗi.
Bugu da ƙari, duk da cewa akwai bincike da
dama da aka gudanar waɗanda suka shafi karin harshen
Katsinanci kamar irin gudunmuwar Dan’Alhaji (2014) da kuma waɗanda suka shafi al’ummomin Nijeriya da Jumhuriya Nijar kamar irin gudunmuwar Yakasai, (1999) da Aichatou (1996) da Malka (1978)
da sauransu, waɗanda suka zama jagora ga manazartan
da suka biyo baya. Ita ma wannan takarda, ana hasashen za ta yi wa sauran
manazarta jagora a nan gaba, musamman waɗanda nazarce-nazarcensu suka shafi
al’ummomin ƙasar Najeriya da kuma na
Jumhuriyar Nijar. Haka kuma, karin harshen Katsinanci yana ɗaya daga cikin kare-karen harshen
Hausa kuma yana buƙatar kyakkyawar kulawa ta fuskar
nazarin abin da ya shafi sauye-sauyen furucin wasulla da ke wanzuwa a cikinsa.
Waɗannan yana daga cikin dallilai da
suka assasa ƙoƙarin gudanar da wannan takarda.
1.2 Farfajiyar Bincike
Nazarin karin harshe, fage ne mai faɗi saboda ya kasance wani ɓangare na harshe da ake magana da shi na wata nahiya ko sashen ƙasa ɗungurungum. Haka kuma nazari ne da
ya shafi karin harshen wasu rukunin al’ummomi (sociolect) ko karin harshen wani
mutum wato, (idiolect).
An taƙaita wannan bincike ne a kan
nazarin karin harshe nahiyar birnin Katsina da birnin Maraɗi ta la’akari da furuci da tsarin sauti kaɗai, wato bai shafi ƙirar kalma ko ginin jumla ba.
1.3 Mazhabar Bincike.
An ɗora wannan bincike a kan mazhabar “tsarin sautin tsirau”
(Generatiɓe Phonology). Mazahabar ta ƙunshi nahawun
tsirau na bai ɗaya da Noam
Chomsky da Halle (1968) suka samar, domin mazahabar kai tsaye ta shafi ɓangaren sauyi da bambbance -bambancen ƙwayoyin sauti a da’irar furucinsu
tare da gurin samar da dokar nazarin waɗannan bambance
–bambance ko sauye - sauye ta bai ɗaya.
Mazahabar tsarin
sautin tsirau ana kallon ta a matsayin wadatacciyar mazahaba a ɓangaren fayyace ko ƙalailaice furucin harshen ɗan’adam musamman a ɓangaren tsarin
sauti ko gamayyar tsarin sauti da tasarifi. Manazarta da dama irin su: (Kisse
Birth 1979 da Anderson 1979 da 1980) da sauransu duk sun yi amfani da wannan
ra’i a nazarin harshe.
1.4 Taƙaitaccen Tarihin Ƙasar Katsina
Ƙasar Katsina,
babbar masarauta ce wadda ta yi iyaka da Jamhuriyar Nijar daga arewa wato ƙasar Maraɗi da kuma, ƙasar Daura daga
gabas da masarautar Kazaure daga gabas maso kudu da masarautar Zazzau daga kudu
da kuma masarautar ’Yandoto daga yamma maso Arewa. Katsina, tana da kirari na
‘tudu garin Ɗanmarina’ kamar
yadda ake faɗa. Asalinta ya
samu ne tun a farkon ƙarni na goma sha
uku, kuma mazaunin wannan masarauta a tarihi na wannan gari yana a wani wuri da
ake kira “Ambuttai” cikin garin Katsina na yanzu (Birth 1963:475-476).
Akwai ra’ayoyi da
dama mabambanta dangane da kafuwar Katsina da masarautarta. A wani ra’ayi ana
ganin cewa akwai mutane da ke zaune a wurare irin su: Durɓi-ta-kusheyi ƙaramar hukumar Mani, da Bugaje ƙaramar hukumar
Jibiya, da Ruma ƙaramar hukumar
Batsari, da Runka ƙaramar hukumar
Safana, da Gozaki ƙaramar hukumar Ƙafur, da Maska ƙaramar hukumar
funtuwa da sauransu (Usman,1981:7:45-49). Mazaunan waɗannan wurare sun zaɓi wannan wurare ne
domin gudanar da sana’o’i irin su: noma, da kiwo da haƙar tama. Waɗanda ake danganta su da masarautar Katsina kuwa, duk da cewa
akwai ra’ayoyi da dama ana iya cewa tsarin sarautar Katsina ya samu ne a ƙarƙashin ƙarni na sha uku.
Haka kuma, wani
ra’ayin ya zo da bayanin cewa, Sarkin Katsina na farko shi ne, wani Sarki mai
suna; Kumayau ɗan Sarkin Daura
Bawo ɗan Abu Yazid
(Bayajidda).An ce Kumayau ya kafu a karagar sarautar Katsina bayan cinye birnin
Durɓawa da yaƙi. Daga nan
zuriyarsa suka ci gaba da riƙon Katsina har
zuwa lokacin da aka sami Sarki Korau daga Yandoto ya karɓe mulki daga hannunsa ya ci gaba da nasa mulkin.To, ko yaya
asalin Katsina ko kafuwar Katsina ya ke, ta fito a sarari wato inda aka santa a
tsakanin karni na (13-14), Wato tun lokacin da aka gina ganuwar Amina kusa da ƙoramar Tula da ƙoramar Gizu. A
lokacin kasuwancin noma, da kiwo da fatauci da kuma wanzuwar tsari na addini,
na daga cikin abin da ya fito da Katsina a fili da masarautarta. Akwai al’umma
da dama da ke zaune a ƙasar Katsina kuma
mafi rinjayensu Hausawa ne da kuma Fulani. Wannan yanki na ƙasar Katsina ana
iya kallon sa ta fuska ko ɓangare biyu. Wato
Katsina kudu. A nan idan an ce, Katsina kudu ana nufin Katsina da ke yankin
Nijeriya, sai kuma Katsina Arewa, wato Katsina da ke yankin Nijar. Saboda haka
a nan an yi bayanin yankin ƙasar Katsina dangane
da yankunan da aka Ambata a sama.
Katsina Kudu:
wannan yanki Allah ya al’abarkace shi da ƙasar noma da wuraren kiwo wato, dazuzzuka da kuma duwatsu
manya da matsakaita. Haka kuma, wannan yanki yana da manyan koguna jefi-jefi
misali: kamar kogin Karaɗuwa, da kogin zobe
(Dutsin-ma) da kogin Jibiya, da kogin Ajiwa da sauransu. Bayan haka, ƙasar Katsina tana
da tafkuna da dama da ke ajiye ruwa, haka kuma wannan yanki yanayin ƙasarsu mai laka
ce, kuma akwai wadatar itatuwa.
Katsina Arewa:-
wannan yankin shi ma ta fuskar noma, yanayin ƙasar ya bambanta
da Katsina arewa, ƙasar noman Jigawa
ce, wadda aka fi cin gajiyar noman gyaɗa, da gero, da
wake, da soɓorodo da sauransu.
Kuma wannan yankin, na da tsaunuka waɗanda ke ƙunshe da ma’adanai a ƙarƙashinsu. Haka
kuma, akwai manyan koguna da ƙoramu misali:
kamar gulbin Maraɗi, gulbin haɗe yaro (gawo da cibi) da ke Dankama. Wannan yanki na da
itatuwa jefi-jefi, amma ba kamar na yankin Katsina ta kudu ba. Haka kuma,
wannan yanki na da yawan burtali wato hanyar dabbobi. Usman (1981).
1.5 Taƙaitaccen Tarihin Maraɗi
Maraɗi ta kasance gari ne mai iko da dukkanin sassan garin a
wani wuri da ake kira gulbin Maraɗi. Katsinawa ne waɗanda sakamakon sabon tsarin mulki da aka samu daga
’Yandoto, ya sa al’ummomin tsohuwar daular Katsina gusawa daga Katsina suka yi
arewa, wasu daga cikin al’ummomin sun zauna a Dankama, wasu suka matsa gaba
bakin gulbi da ake kira gulbin Maraɗi. A sakamakon ambaliyar ruwa da gulbin ya yi, wasu
al’ummomin sun yi hijira daga wurinsu na ainahi zuwa sabon gari a shekara ta
(1945).
A sakamakon wani bincike da hukumar ƙidaya ta yi a (2001) an samu adadin mutane kimanin
(148,017) waɗanda suke a cikin maraɗi waɗannan ƙabilu sun haɗa da: Hausawa, da Fulani, Bugaje da Zabarmawa,da
Bare-bari,da Tubawa, da Larabawa, haka kuma akwai sauran ƙabilu da ke zaune a cikin garin kamar yarbawa, da zugu,
kwatakwalawa, da Fallon, da Ibo, Bambarci da sauran yaruka daban-daban.
Ta fuskar sana’o’i kuwa, al’ummomin wannan wuri, na
gudanar da sana’ar kiwo, da noma, da fataucin dabbobi da sauransu. Maraɗi gari ne da ya ƙunshi manoma, makiyaya, yan kasuwa da ma’aikatan
gwamnati. Akwai kafafen yaɗa labarai kamarsu R.J.M, Amfani, Sarauniya, Tenene,
Garkuwa. Sannan ita ce babbar cibiyar kasuwanci ta ƙasar Nijar, kasancewarta tana da albarkar ƙasar noma musamman gyaɗa. Maraɗi ta bunƙasa a cikin shekara ta (1980), wannan ya biyo bayan samar
da garin Maraɗi bisa babban titin da ’yankasuwa daga ɓangarori da dama na
yammacin Afirika ke amfani da shi domin gudanar da harkokin kasuwanci. Nama’aji (2017).
2.1 Ma’anar Harshe
Masana da dama sun
yi bayani mai gamsarwa dangane da ma’anar harshe. Ladan (1996) ya ce,
“Harshe abu ne da ya ƙunshi alamomi da Ɗan’adam yake
amfani da su wajen bayyana tunaninsa. Ya cigaba da cewa alamomin harshe
sun ƙunshi sautukan da ake furtawa a jajjere, kuma ake amfani da
su cikin tsari”.
Shi kuwa Fagge (2001) cewa ya yi; “Harshe wata hanyar
sadarwa ce da Ɗan’adam yake amfani da sauti mai ma’ana wanda
kuma ta haka ne kowacce al’umma da ke zaune a doron ƙasa take fahimtar abubuwan da ke ƙunshe a zukatan jama’a, kamar tunani, ra’ayi, hikima, sha’awa da sauransu”.
2.2 Ma’anar Karin
Harshe
Akwai masana da
dama da suka kawo ma’anar Karin harshe, wasu daga ciki sun haɗa da: Zarruƙ da wasu (1990:9) wanɗanda suka bayyana ma’anar Karin harshe da cewa:
“Karin harshen Hausa yana nufin ‘yan bambance-bambancen
lafazi da na kalmomi da jimloli a tsakanin rukunonin al’umma ko shiyoyin ƙasa mai harshe ɗaya.”
Shi
kuwa, Wurma, (2005:36) ya bayyana ma’anar karin harshe da cewa:
“Karin harshe, shi ne harshe wanda ake amfani da shi
takamaimai a wani ɓangare ko sashe na ƙasa. Ana gane shi a wajen lafazin kalmomi da jumloli
tsakanin mutane”
A taƙaice za a iya cewa Karin harshe, rarrabuwa ce da ake samu
a cikin harshe, da kuma yadda ake tafiyar da wannan tasirin rarrabuwar wajen
amfani da harshe ɗaya.
2.3 Ire-Iren Karin Harshe
Karin
harshen Hausa yana da manyan rassa guda biyu: Karin harshe na nahiya da Karin harshe na
rukuni/zamantakewa, kowanne ɗaya daga cikin waɗannan rassa ko ɓangare yana da
nasaba da kuma tasiri ga juna.
2.3.1 Karin Harshen Nahiya
Masana
irin su Haugen (1972:98) ya nuna cewa, a ƙasar tsohuwar Girka, kare-karen harsunan ƙasarsu ne suke
amsa sunayen lardunan da ƙasar ke da su. Waɗannan nau’o’i na Karin harsuna ba a amfani da su a zance ko
magana, sai dai kowanensu na nan a rubuce. Ana amfani da su a fannoni na
musamman kamar a fagen rubuce-rubucen adabi. Misali Karin harshen ‘Lonic’ ana
amfani da shi wajen yin bayanin abubuwan da su ka ƙumshi Tauhidi. Sauran kare-karen harshen irin su: ‘Domic’ da
‘Attice’ ana amfani da su wajen rubuta waƙoƙi da wasannin
kwaikwayo na ban tausayi.
Karin
harshen nahiya shi ne Karin harshe da ake amfani da shi a tsakanin manyan
garuruwa kuma shi ne kare karen harshen da ake samu a sakamakon
bambance-bambancen da ke tattare da garuruwa. A taƙaice dai, Karin
harshen nahiya shi ne, wanda yake fayyace rukunin mutane ko yanki, kuma yana
nuna wurin da suka fito. A ƙasar Hausa kuwa,
an lura, kusan kowace Daula ko masarauta tana da irin waɗannan bambance-bambance. Wato kowace masarauta tana da Karin harshe daban wanda ya saɓa da na kusa da shi. Hasali ma, sunan masarautar shi ne ɗauke da laƙabin Karin
harshen. Misali Dauraci daga Daura, Kananci,
daga Kano, Katsinanci daga Katsina, Zazzaganci
daga Zazzau (Zariya) da sauransu (Zarruk, da wasu 1990:9).
2.3.2 Karin Harshen Rukuni/Zamantakewa
Karin
harshen rukuni wani ɓangare ne da ya
danganci Karin harshen wasu mutane masu halayyar zamantakewa da kuma hanyoyin
sarrafa harshe iri guda. Wato yanayin zamantakewa yana da tasiri na musamman
dangane da harshe da kuma yadda ake amfani da shi. A wata mahanga, Karin harshen zamantakewa nau’i’ne daga cikin kare - karen
harshen Hausa kuma yana da wasu siffofi na Bahaushiyar al’ada wadda ba a iya
barin su ba, idan ana magana kan yadda
yanayin zamantakewa take kasancewa. Waɗannan siffofi, su
ne, na jinsi da shekaru da kuma dangantaka wadda ta kasance tsakanin mai magana
da kuma mai sauraro”. Wannan ɓangare na Karin
harshen rukuni ko na zamantakewa da shi ake kallon kowace al’umma ta duniya da
irin tsarin zamantakewarta wadda ta bambanta da sauran al’ummomi. Dangane da
wannan, masana sun raba al’ummar Hausawa zuwa, manyan rassa guda biyu, wato
ajin saraki da ajin talakawa, wanda shi wannan ajin na talakawa ya ƙara rabuwa, zuwa
ajin malamai da attajirai da sauran jama’a. Misali:- Hausar malaman asibiti, Hausar ‘yan acaɓa, Hausar mahauta da sauransu Hauwa Muntari (2008).
3.0 Sauye-sauyen Wasulan Karin Harshen Katsina da Maraɗi
An yi nazarin karuruwan harshen Katsina da na
Maraɗi domin gano sauye-sauyen wasula da ake samu a tsakanisu.
Wannan bincike ya gano cewa akwai
sauye-sauye na wasula da ake samu tsakanin
Karin harshen Katsina da na Maraɗi kamar haka:
3.1 Sauyawar Wasalin /i/ zuwa [u]
Bincike ya nuna
ana samun sauyawar gajeren wasalin sama
ɗan gaba marar kewaya /i/ zuwa gajeren wasalin sama ɗan ƙurya mai kewaya /u/. A harshen birnin Katsina
wannan wasali na /i/ yana sauyawa zuwa /u/ a wasu kalmomi na katsinancin birnin
Maraɗi. Misali:
S/No |
Daidaitacciyar Hausa |
Gloss |
K/H Katsina |
K/H Maraɗi |
1. |
Milyan |
Million |
Milyan |
Mulyan |
2. |
Mil-tara |
Name of place |
Mil-tara |
Mul-tara |
3. |
Milki |
Administration |
Milki |
Mulki |
4. |
Zulai |
Name of
female |
Zilai |
Zulee |
5. |
Zulƙibilu |
Name of Hausa
Male |
Zilƙibilu |
Zulƙibulu |
6. |
Zuriya |
Family |
Ziriya |
Zuruya |
S/No |
Daidaitacciyar Hausa |
K/H Katsina |
Lafazi |
K/H Maraɗi |
Lafazi |
1. |
Milyan |
Milyan |
Mìlyân |
Mulyan |
Mulyân |
2. |
Mil-tara |
Mil-tara |
Mìl-tara |
Mul-tara |
Mul-tárà |
3. |
Milki |
Milki |
mìlkìi |
Mulki |
mulkíi |
4. |
Zulai |
Zilai |
zìlâi |
Zulee |
zùlee |
5. |
Zulƙibilu |
Zilƙibilu |
zílƙìbíilù |
Zulƙibulu |
Zulƙìbúulùu |
6. |
Zuriya |
Ziriya |
zìrí’à |
Zuruya |
zurù’à |
Bayan la’akari da
misalan da suka gabata, an fahimci cewa, wannan sauyi na waɗannan ƙwayoyin sautuka da aka ambata, ya auku a kalmomin suna
kamar yadda misali na (01) rukunin( b) a misalai na (1, zuwa 6,) suka nuna. Dangane da tsarin gaɓa kuwa, sauyin ya
auku a kan cibiyar rufaffiyar gaɓar farkon kalmomin suna, kamar yadda misali na (01), rukuni
(b) a misali na (1,2, 3 da 4,) suka nuna. Sai kuma a cibiyar buɗaɗɗiyar gaɓar farko kamar a
misali na (4, da 6,).
Haka kuma wannan sauyi na ƙwayar sautin gajeran wasalin sama ɗan gaba marar kewaya a karin harshen Katsinancin birnin Katsina /i/ na sauyawa zuwa gajeran wasalin sama ɗan ƙurya mai kewaya a karin harshen Katsinancin birnin Maraɗi kamar yadda aka gani a rukunin misalai na (1, zuwa 6,).
Dokar a nan ita
ce, sautin wasalin sama ɗan gaba da ya zo a wasu kalmomin karin harshen birnin
Katsina bai sauɓa wa tsarin
daidaitacciyar Hausa ba. A karin harshen birnin Maraɗi kuwa, sauyin da
aka samu, wanda yazo da sautin wasalin sama na ƙurya mai kewaya ya saɓa wa tsarin daidaitacciyar Hausa.
3.2 Sauyawar Sautin Wasalin Tsaka-tsaki /a/ zuwa /i/
A karin harshen Katsinancin birnin Katsina, bincike ya
bayyana cewa, gajeren wasalin ƙasa ɗan tsaka-tsaki marar kewaya /a/ kan sauya zuwa gajeren wasalin sama ɗan gaba marar
kewaya /i/ a Katsinancin birnin Maraɗi. Misali:
S/N |
Daidaitacciyar Hausa |
Gloss |
K/H Katsina |
K/H Maraɗi |
1. |
kira |
call |
kira |
kiri |
2. |
mani |
to me |
mani |
mini |
3. |
misali |
example |
misali |
Masala |
4. |
sa’adda |
at the time |
sa’adda |
sá’idín |
5. |
misaabaha |
settlemen |
misabaha |
masabaha |
S/N |
Daidaitacciyar Hausa |
K/H Katsina |
Lafazi |
K/H Maraɗi |
Lafazi |
1. |
Kiraa |
kira |
kirà |
kiri |
kírí |
2. |
Mani |
mani |
mání |
mini |
mìní |
3. |
Misali |
Misali |
mísàlí |
masali |
màsàli |
4. |
sa’adda |
sa’adda |
sa’adda |
sa’idin |
sá’ìdîn |
5. |
Misalaha |
misalaha |
misàlahà |
masalaha |
màsalàhà |
A sakamakon
nazarin misalan da suka gabata, an fahimci cewa, wannan sauyi ya faru ko ya
auku ga wasu daga cikin azuzuwan kalmomin Hausa irin su: kalmar suna kamar a misali na (02), rukuni (b) a misali na (1, 3, da 5,) suka nuna.
Sai kuma, a kalmar wakilin suna jakada a
misali na (2,) da kuma a harafin sharaɗi kamar a misali na (4,).
Ta fuskar tsarin
gaɓa kuwa, wannan sauyi ya auku a cibiyar rufaffiyar gaɓar kalmomi, kuma
yana wakana a gaɓar farkon kalma kamar a misali na (02), rukuni (b) a misali
na (3, da 5,) da kuma a tsakiyar kalma,
kamar a rukunin misali na (4,) da kuma ƙarshen kalma kamar
a rukunin misali na (1).
A sakamakon
nazarin misalan kalmomin da bincike ya zo da su, an fahimci cewa, a karin
harshen Katsinancin birnin Katsina, gajeren wasalin tsaka-tsaki marar kewaya
wato sautin /a/ ya sauya zuwa gajeran
wasalin sama na gaba marar kewaya a karin harshen Katsinancin birnin Maraɗi, kuma wannan
sauyi ya faru a cibiyar gaɓar kalma ne kawai. Za kuma a iya bayyana wannan
bambanci kamar haka:
Dokar a nan ita
ce, sautin gajeren wasalin tsaka-tsaki da ya zo a cikn wasu kalmomin karin
harshen Birnin Katsina, bai saɓa wa daidaitacciyar Hausa ba. A karin harshen Birnin Maraɗi kuwa, sauyin da
ya zo na gajeren wasalin sama na gaba marar kewaya a wasu kalmomin, ya saɓa wa tsarin daidaitacciyar Hausa.
3.3 Sauyawar Sautin Wasali /a/ zuwa /u/
A karin harshen Katsinanci birnin Katsina an
sami gajeren wasalin ƙasa tsaka-tsaki /a/ ya sauya zuwa gajeren wasalin sama ɗan ƙurya mai kewaya wato sautin /u/ a karin harshen Katsinancin
birnin Maraɗi a wasu kalmomi.
Misali:
Daidaitacciyar Hausa |
Gloss |
K/H Katsina |
K/H Maraɗi |
|
1. |
madubi |
mirror |
madubi |
mùdubi |
2. |
mazuru |
male cat |
mazuru |
muzuru |
3. |
bahari |
name of male |
bahari |
buhâri |
4. |
mazugal |
name of place |
mazugal |
muzugal |
5. |
mahalli |
shelter |
mahalli |
muhalli |
6. |
mahawara |
argument |
mahawara |
muhawara |
S/No |
Daidaitacciyar Hausa |
K/H Katsina |
Lafazi |
K/H Maraɗi |
Lafazi |
1. |
madubi |
madubi |
màduubìi
|
mudubi |
mùduubii |
2. |
mazuru |
mazuru |
màzúurù |
muzuru |
mùzuuruu |
3. |
bahari |
bahari |
báhàaríi
|
buhari |
bùhâarii |
4. |
mazugal |
mazugal |
màzugàl |
muzugal |
mùzuugal |
5. |
mahallii |
mahalli |
màhállí |
muhalli |
mùhâllii |
6. |
mahaawaaraa |
mahawara |
mahàawáaràa |
muhawara |
mùhaawàaràa |
A sakamakon
nazarin waɗannan misalai da wannan bincike ya samar a sama, an fahimci cewa, wannan sauyin ƙwayar sautin wasalin
/a/ a karin harshen Katsinancin birnin Katsina, ta sauya zuwa sautin /u/ a karin harshen Katsinancin birnin Maraɗi. Kuma wannan
sauyi ya auku a kalmomin suna, kamar yadda aka gani a misali na (03) a rukunin
(b) a misali na (1,2, 3, 4, da 5,). Sai kuma a suna ɗan aikatau a
rukunin misali na (6,).
Haka kuma, ta fuskar tsarin gaɓa kuwa, wannan
sauyi ya wanzu a cibiyar buɗaɗɗiyar gaɓar farkon kalma
suna, kamar yadda aka gani a rukunin misalai daga na (1, zuwa 6,).
/a/ a karin
harshen Katsinancin birnin Katsina
da ya sauya zuwa gajeran wasalin
sama na ƙurya mai kewaya /u/ a karin harshen Katsinancin birnin Maraɗi ya auku ne lokacin
da cibiyar buɗaɗɗiyar gaɓar ta gabaci ƙwayar sautin baƙi baleɓe a farkon kalma. A na iya fayyace
wannan bambance-bambance kamar haka:
Dokar a nan ita ce, sautin gajeren wasalin tsaka-tsaki da ya zo a wasu misalai
na karin harshen birnin Katsina ya saɓa wa tsarin daidaitacciyar Hausa. A karin harshen birnin Maraɗi kuwa, sauyin da aka samu na
gajeren wasalin sama ɗan ƙurya mai kewaya ya yi daidai da
tsarin daidaitacciyar Hausa.
3.4 Sauyawar sautin wasali /ii/ zuwa [ai]
Wani ƙarin bayani, an sami sauyi a tsakanin karin harshen Katsinancin birnin Katsina da na birnin Maraɗi a wurin da ake samin dogon wasalin sama ɗan gaba marar
kewaya/ii/ na sauyawa zuwa tagwan wasalin /ai/ a wasu kalmomin Katsinancin
birnin Maraɗi. Misali
S/No |
Daidaitacciyar Hausa |
Gloss |
K/H Katsina |
K/H Maraɗi |
1. |
ʔawaki |
goats |
ʔawaki |
ʔawakkai |
2. |
Gonaki |
farms |
gonaki |
gonakkai |
3. |
dawaki |
horses |
dawaki |
dawakkai |
S/N |
Daidaitacciyar Hausa |
K/H Katsina |
Lafazi |
K/H Maraɗi |
Lafazi |
1. |
ʔawaaki |
ʔawaaki |
ʔawaaki |
ʔawakkai |
ʔawakkai |
2. |
gonaki |
gonaki |
gonaaki |
gonakkai |
gonakkai |
3. |
dawaki |
dawaakii |
dawaaki |
dawakkai |
dawakkai |
Bayan la’akari da
misalan da wannan bincike ya kawo a sama, an fahimci cewa, wannan sauyi ya auku
a kalmomin suna jam’i kamar yadda misali
na (04), rukunin (b) a misali na (1, 2, da 3,) suka nuna.
Ta fuskar tsarin
gaɓa kuwa, an fahimci cewa wannan sauyi ya auku a cibiyar buɗaɗɗiyar gaɓar ƙarshen kalma kamar yadda misali ya nuna daga na (1, zuwa na
3,).
3.5 Sauyawar Sautin wasali /ai/ zuwa /ee
A ƙoƙarin gudanar da wannan bincike, an fahimci cewa, a furucin
karin harshen Katsinancin Birnin Katsina tagwan wasalin /ai/ na sauyawa zuwa
dogon wasali tilo /ee/ a Katsinancin birnin Maraɗi. Misali:
S/No |
Daidaitacciyar Hausa |
Gloss |
K/H Katsina |
K/H Maraɗi |
1. |
saiwa |
steam |
saiwa |
sewa |
2. |
daidai |
right |
daidai |
Dede |
3. |
wasai |
fresh |
wasai |
wase |
4. |
maida |
take it bach |
maida |
meda |
5. |
mairo |
name |
mairo |
Mero |
6. |
ƙosai |
beans cake |
ƙosai |
Ƙose |
7. |
ƙorai |
calabashies |
ƙorai |
Ƙore |
8. |
taimako |
help |
taimako |
Temako |
9. |
ɗaweniya |
responsibility |
ɗawainiya |
ɗaweniya |
S/No |
Daidaitacciyar Hausa |
K/H Katsina |
Lafazi |
K/H Maraɗi |
Lafazi |
1. |
saiwaa |
saiwaa |
sáiwàa |
seewaa |
Sêewàa |
2. |
daidai |
daidai |
dâidâi |
deedee |
Dèedèe |
3. |
wasai |
wasai |
wàsai |
wasee |
Wàsêe |
4. |
maida |
maida |
máidà |
meda |
Mèeda |
5. |
mairoo |
mairo |
mairòo |
meroo |
mèeroo |
6. |
ƙoosai |
ƙosai |
ƙóosai |
ƙose |
Ƙòosèe |
7. |
ƙorai |
ƙorai |
ƙóorai |
ƙore |
Ƙòorèe |
8. |
taimako |
taimako |
táimàkóo |
temako |
Têemàkoo |
9. |
ɗaweenijaa |
ɗawainiyaa |
ɗàwáinijáa |
ɗawainiya |
ɗàwèeníjàa |
A sakamakon ƙalailaice bayanan misalan da suka gabata, an fahimci cewa,
wannan sauyawar ƙwayar sautin wasali ta auku a wasu daga cikin kalmomin suna,
kamar a misali na (05) rukunin (b) a misali na (1, 2, 5, 6, 7, 8, da 9,). Sai
kuma a kalmar aikatau, a rukunin misali
na (4,). Da kuma a kalmar amsa kama a rukuni na (3,).
Ta fuskar tsarin
gaɓa kuwa, a wannan gudunmuwa an fahimci cewa, wannan sauyin ƙwayoyin sauti na aukuwa a cibiyar gaɓar farkon
kalma, kamar yadda ya zo a misali
na (05), a rukunin misalai na (1, 2, 4, 5, da 8,). Sai kuma a tsakiyar
kalma kamar a rukunin misali na (9,). Da kuma a ƙarshen kalma kamar a rukunin misalai na (2, 3, 6, da 7,).
Haka kuma, a
sakamakon nazarin wannan misalai da wannan bincike ya kawo, an fahimci cewa,
wannan sauyi ya wanzu a cibiyar gaɓar ne, kuma ana samun wannan sauyi a farko da tsakiya da
kuma ƙarshen kalma.
A nan dokar ta nuna cewa, tagwan wasali da ya zo a misalan
karin harshen birnin Katsina ya yi daidai da tsarin daidaitacciyar Hausa. A
karin harshen birnin Maraɗi kuwa, sauyin da aka samu na dogon wasalin gaba na sama
marar kewaya ya saɓa wa tsarin daidaitacciyar Hausa.
4.0 Kammalawa
Daga ƙarshe kamar yadda
manufar wannan takarda ta nuna cewa, takardar na ƙoƙarin fito da
sauye-sauyen sautukan wasulla a tsakanin karin harshen birnin Katsina da na
Maraɗi ta fuskar furuci
da tsarin sauti. Takarda ta yi ƙoƙarin fito da waɗannan sauye-sauye na wasulla kuma an yi bayani dalla-dalla
na ajin nahawun kalmomin da wannan sauyi ya shafa. Haka kuma, an yi ƙoƙarin fayyace irin
gaɓar da sauyi ya
auku a kanta. Tun da farkon wannan takarda, an nuna cewa an yi amfani da mazahabar Tsarin
Sautin Tsirau na Bai-ɗaya, (Generative Phonology Theory) musamman wajen fayyace bambance-bambancen ƙwayoyin sautukan
wasullan da aka gabatar.
Manazarta
1.
Ado, A.
(2017). Ra’o’in Bincike Kan Al’adun Hausawa, Katsina: Sashen Harsunan Nijeriya Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua.
2. Aliyu, M. (2010). Kamanci Da Bambanci Tsakanin Hausar Katsina Da Ta Maraɗi: Bincike Kan Sana’ar Ƙira. Kundin Digiri Na Ɗaya, Katsina: Jami’ar Ummaru Musa Yar’adua.
3.
Alkasim, H. (1995) Dialectal Differences In Hausa
Language: A Case Study Of Bausanci. Kundin Digiri na Ɗaya, Kano: Jami’ar Bayero.
4.
Amfani, H.A
(1980) Nazari A Kan Bambance-Bambance Tsakanin Zazzaganci Da Daidaitacciyar Hausa, Kundin
Digiri Na Ɗaya. Zaria: Jami’ar Ahmadu Bello.
5.
Bello, A.
(2016) Hausa Dialects and Distinctive Feature Analysis: Zaria, Ahmadu Bello University
6. Busa, A. M (2013) A Comparative Study Of Some Aspect Of Hausa And
Gbagyi Phonological
7.
C.N. H.N,
(2006) Kamusan Hausa Cikin Hausa. Kano: Centre for the Study of Nigerian Languages, Bayero University.
8.
Chomsky, N.
& Halle (1968): The Sound Pattern of English (SPE). New York Harper, & Row
9.
Crystal, D.
(1980) A First Dictionary of Linguistic
and Phonetics, London.
10.
Gusau, S.M.
(2015) Mazahabobin Ra’i da Tarken Adabi
da Al’adu na Hausa. Kano: century Research ltd
11.
Haruna, S.
(2012) “Phonological Processes and
Phonemic Merger In Hausa” Kundin Digiri Na Uku, Kano: Jami’ar Bayero.
12.
Ibrahim, S.J.
(2007) Hausar Jalingo, Kundin Digiri
Na Ɗaya, Zaria: Jami’ar Ahmadu Bello.
13.
Kenstowiez,
M. & Kisseberth, C. (1979) Generative
Phonology, Academic Press London
14.
Malka,
J.G.(1978) Nazarin Bambance– Bambance Da
Ke Tsakanin Daidaitacciyar Hausa (Nijeriya)
Da Hausar Filinge (Jamhuriyar Nijar) Ta Fuskar Tsarin Fannin Furuci.
Takardar Ƙarawa Juna Ilimi. Zaria: Jami’ar
Ahmadu Bello
15.
Sani, M.A.Z.
(2005) Jagoran Nazarin Tsarin Sauti.
Benchmark Publishers LTD, Kano. System, Takarda Ƙarawa Juna Sani, Zaria, Jami’ar Ahmadu Bello.
16. Wurma, A.G, (2008) Kalma Ɗaya Ma’ana Tuli, Algaita Journal
of Current Research in Hausa Studies. Vol. 1No5.
17. Zarruk, R.M (1980). Lafazin Hausa a Taƙaice. Zaria: Institute of Education, Ahmadu Bello University.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.