Ticker

6/recent/ticker-posts

Kamun Ludayin Jemage

Tattabara uwar alƙawari ta nisa ta ce "Ko yaushe jagororin dajin nan za su fara tausayawa tsuntsaye?  Shekaru da yawa muna cikin azabar mulkin Babba-Da-Jaka, yanzu kuma ga shi Jemage shi ma dai yana neman ɗorawa daga inda ya tsaya, Kaico!"

Kurciya ta yi murmurshi sannan ta ce "Da ma ai mantawa ki ka yi, amma dama ai Jemage ya sha nanatawa cewa zai ɗora ne daga inda Babba-Da-Jaka ya tsaya, ya ko cika alƙawarin don ga shi nan ya fara aiki gadan-gadan"

Kanari da ke can gefe kuwa sai ta hau waƙa tana cewa;

"Iya yawan huƙurinku da juriyar ku,
Iya yawan azabar da za su yi mu ku.

A zaɓe yawan tsabar da su ka watsa,
Yawan Kogin wahalar da za ku ratsa.

Tsuntsun da a yini guda ya yi zalama,
Zai shekara ko yana cikin nadama...

"Ke Kanari! Yi mana shiru! Waƙar ta ki ma duk babu daɗi, ki ƙyale mu da abin da ke damun mu na ƙara farashin ruwan sinadiri da aka ƙara mana" Kurciya ta katse ta a fusace.

Bainu ta ce "Duk da dai babu alamun tsufa gare ni, amma na daɗe a rayuwa ban ga tashin hankali da matsi da aka shiga irin wannan lokacin ba, yanzu ta kai ta kawo tsuntsaye da yawa haka su ke kwana babu ƙoto, tsuntsaye duk an firgice, ni daga yanzu ma sheƙar bauta zan koma da zama, don da dukkan alamu ƙiyama ta kusa"

Hazbiya da tunda aka fara zancen ba ta ce komai ba, ta kaɗa fiffike ta kimtsa sannan ta ce "Na lura ba Jemage kaɗai ke da laifi ba, akwai majalissar Ragon-Maza, su ma da su ake haɗo baki a ga na mana azaba, sannan Balbela da ƴan'uwanta su ma da su, kullum sai a rufe ƙofa da su, sai su je jihohinsu su nuna su na gari ne, tabbas farin Balbela na yaudara ne, da ka bincika namanta sai ka ga baƙi ne"

Tsatsewala ta ce "Haka ne kam, yanzu dai Jemage dai ya ba su sulalla da yawa, don kowa ya je jiharsa ya yi bajinta sannan ya taimaki tsuntsayen jiharsa da tallafi don a rage raɗaɗin da ake ciki, yanzu yakamata tsuntsaye su sanya idanuwa akan Balbelu, don a tabbatar sun yi amfani da sulallar da Jemage ya ba su a hanyar da ta dace."

Da ya ke dare ya yi, nan tsuntsaye su kai sallama kowa ya nufi sheƙarsa.

*An hango Alhudahuda a ciƙin sheƙarsa a tsakkiyar wasu manyan littattafai sanye da farin gilashi ya na bincike.

Daga Taskar

Mukhtar Mudi Sipikin
22/07/2023

Post a Comment

0 Comments