Ticker

6/recent/ticker-posts

Nijeriya Ta Zo Ta Biyar A Yawan Alhazai A Shekarar 1444/2023

Kasar Nijeriya ce ta zo  ta biyar a duniya a yawan alhazai (95,000) a wannan shekara ta 1444/2023

1. Indonesia: 221,000

2. Pakistan: 179,210

3. India: 175,025

4. Bangladesh: 127, 198

5. Nigeria: 95,000 

"Daɗin da nij jiya Haji Ɗanƙwairo,
Tutarmu wadda ak' ƙasam Makka da Alhaji Musa kwance take
Mulkinka Shehu Shagari an tashshe ta ta koma tsaye,
A wajen huskam Musulunci yau Nijeriya ita ce ta ɗaya"

Inji Makaɗa Musa Ɗanƙwairo Maradun a faifan Marigayi Mai Girma Shugaban Ƙasar Tarayyar Nijeriya a Jamhuriya ta biyu, Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari GCFR Turakin Sakkwato mai taken 'Shugaban Ƙasa jikan Sule, wada duk aka so kayi'. Allah ya kyauta makwanci, amin.

Daga Taskar

Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
Ɗanmadamin Birnin Magaji
Imel: birninbagaji4040@gmail.com
Lambar Waya: 08149388452, 08027484815

Post a Comment

0 Comments