Ticker

6/recent/ticker-posts

Mu San Tarihin Shuwagabanninmu 017

Mu San Tarihin Shuwagabanninmu 017
Na farko daga gefen hagu (a cikin babbar riga bula) shi ne Rt. Honorable Lawali Labbo Margai Tsohon Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Sakkwato wanda ɗa ne ga Marigayi Mai Girma Sarkin Kabin Kebɓɓe, Jihar Sakkwato wanda Malamin Waƙa ya yi wa waƙar nan mai Amshi:
"Aikin rinjaya yay yi makaye,
Ya kwan da shirin maza,
Sarkin Kabi gamda'aren Kilodi". 
Dalilin samun 'Margai' a cikin sunan Honorable Lawali Labbo shi ne a wannan Ƙauyen ne na Margai aka haife shi, a lokacin Mahaifin nashi ya na Dagacin Ƙauyen da laƙabin Sarautar "Kilodi". Dama ana tura ɗan Sarki ne daga gidan sarautar Keb'b'e ne a matsayin Dagaci a wannan Ƙauyen na Margai. A halin yanzu wani tsohon Ma'aikacin Banki ne da ake kira, Alhaji Abubakar Ƙasimu ne ke sarautar Sarkin Kabin Keb'b'e. Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana mai albarka, amin.
Daga Taskar

Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
Ɗanmadamin Birnin Magaji
Imel: birninbagaji4040@gmail.com
Lambar Waya: 08149388452, 08027484815 

Post a Comment

0 Comments