**********************
Sadaukarwa ga Mai Girma
Galadiman Katsina, Malam
Saddiƙ Abdullahi Mahuta, OFR
**********************
Babanmu ba ka haushin kowa,
Ɗan Abdullahi ba ƙyamar kowa.
Kai kaka dogaro da ikon Allah.
Na Mahuta ba ka ƙyarar kowa.
Ga haƙuri kamar damo Lallausa,
Don ba ka fushi da wautar wawa.
Ka riƙe 'yan uwan zumu har bare,
A karimci Jallah Yai maka baiwa.
Mai son zama da kai ya bi Allah,
In kuwa ya ƙiya yana shan tsawa.
Ga jinjina inai kullum ba fashi,
Don ni na yaba da aikin ƙawa.
Burinka duk a zam ana adalci,
Kullum gargaɗi kake ba ƙosawa.
Ni dai fata nake ka zamto ƙarko,
Mulkin kai ta yi muna ta yabawa.
Wani ya taho bujum yana surutu,
Share shi baba walla zai zaucewa.
Ya Allah daɗo Salati da Sallama,
Gun manzonKa rahimi gun kowa.
Ƙaro lafiya ga Saddiƙu Galadima,
Imani da aminci Allah daɗa ƙarawa.
***********************
© Bashir Yahuza Malumfashi
Fasihin Galadiman Katsina
Asabar, 20-12-1444 (Hijriyya)
08-07-2023 (Miladiyya).
Photo Credit: Taskargizago
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.