Ticker

6/recent/ticker-posts

Kyautata Dabi’a A Zamantakewar Mata Hausawa

Cite this article as: Dikko, A.L. (2023). Kyautata Ɗabi’a A Zamantakewar Mata Hausawa. Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture, (2)2, 219-226. www.doi.org/10.36349/tjllc.2023.v02i02.027.

Kyautata Ɗabi’a A Zamantakewar Mata Hausawa

NA 

Abdullahi Lawal Dikko (Ph.D)
Department of Linguistics and Nigerian Languages,
Nigeria Police Academy, Wudil, Kano, Nigeria
abduldikko9@gmail.com
08023564283 

Tsakure

Kyautata ɗabi’a a zamantakewar mata Hausawa ado ce, kamar yadda al’ummar Hausawa kan ce ‘kyau adon ‘yan mata”. Kyautata ɗabi’a na ƙara wa mace ƙima da daraja a idon ɗa namiji da ma al’umma baki ɗaya. Nagarta da halin ƙwarai abu ne mai kyau a wajen mace. Al’umma na maraba da su da mutunta duk mai waɗannan ɗabi’u. Abubuwan da ke bayyanar da kyautata ɗabi’u a wajen matan Hausawa sun ƙunshi: al’adu, da sana’a, da addini da kuma ilimi. Duk an yi sharhi akai. Burin wannan nazari shi ne fito da muhimman abubuwan da suka shafi kyautata ɗabi’a a jinsin matan Hausawa da bayyana tasirin su ga al’umma da kuma fa’idarsu. Wajen gudanar da wannan bincike an yi amfani da manyan hanyoyin gudanar da bincike cikin maƙalu da manazarta da masana suka rubuta. Sannan kuma an tuntuɓi littattafai da aka rubuta a wannan ɓangare. A ƙarshe ana sa ran wannan takarda ta fa’idantar da manazarta ta hanyar samun bayanai a kan kyautata ɗabi’u a zamantakewar matan Hausawa, kuma zai zama ma’ajiya ga al’ummar matan Hausawa da sauran jama’a.

Fitilun Kalmomi: Ɗabi’a, Zamantakewa, Mata, Hausawa

1.1 Shimfiɗa

Kyautata ɗabi’a a rayuwar mata, abu ne mai muhimmanci ta kowace fuska. In mun kalle shi ta fuskar addini, addinin musulunci abu ne da ya koyar da mu, ya kuma umurce mu wajen nuna mu’amular mu, mu kyautata ɗabi’a ta kowace fuska. Sannan ta fuskar zamantakewar al’ummar Hausawa tun tali-tali an san su da kyautata ɗabi’a. Saboda haka, ya zama wajibi ga rayuwar mata su kasance masu kyautata da ƙarfafa ɗabi’u na ƙwarai, a harkokin rayuwarsu ta yau da kullum. Sakamakon waɗannan dalilai ya sanya tilas mata su nemi ilimi na addini da boko, saboda ƙoƙarin ganin sun cimma wannan buri na kyautata ɗabi’a a zahiri da baɗini. Sanadiyyar haka wannan takarda ta yi ƙoƙarin zaƙulo abubuwan da suka danganci kyautata ɗabi’u a rayuwar mata Hausawa an yi tsokaci da yin bayanai akai da kuma tasirinsu a rayuwar mata Hausawa. Daga cikin waɗannan muhimman bayanai da aka tattauna a cikin wannan nazari sun ƙunshi: al’ada, da sana’a, da addini da kuma ilimi, da gaskiya, da haƙuri, da karatu, da amana,da kunya. Duk an zayyana su tare da yin sharhi ɗaya bayan ɗaya.

Tsarin wannan aiki ya ƙunshi gabatarwa da yin tsokaci akan kalmomin fannu da kuma yinshi kan aikin kamar yadda aka kawo tare da bayanin yadda aka nazarce su. Haka kuma a ɗarshe an naɗe aiki da abin da aka nazarta a taƙaice da ba da shawarwari.

1.2 Kalmomin Fannu

Ɗabi’a: ɗabi’uu ko ɗabii’oo’ii halin mutum, ko al’adarsa. Wato ana nufin wani abu da mutum ya saba yi na yau da kullum, ko kuma faɗarsa.

Al’ada: hanyar rayuwar al’umma. Bunza, (2006: XXV) Ainihin wannan kalma ba bahaushiya bace, aro ta Hausawa suka yi daga larabci. Ba za mu bi diddigin tarihin aron kalmar ba, domin are – aren kalmomi tsakanin harshen Hausa, da na Larabcin daɗaɗɗen abu ne a tarihi.

A lugar Larabci al’ada na nufin wani abin da aka saba yi ko ya saba wakana, ko aka riga aka san da shi.

Sana’a: Sanaa’oo’’ii. aikin da mutum yake yi don samun abinci. Saboda haka, duk wani aiki da ɗan adam ke yi da nufin samun abin masarufi na yau da kullum shi ake kira da sana’a, wato hanya ce ta samun abin da mutum zai sami kuɗi ya iya biyan harkokinsa na yau da kullum.

Addini: Addini na nufin hanyar bauta da ɗan adam ya yi Imani da ya gasgata shi. A shari’ar musulunci addini na nufin yin bautar Allah ta hanyar kaɗaita Allah da bin umurnin sa, wato yin hani da horo.

2.1 Ayyukan da Suka Gabata

Duk wani aiki da aka gabatar da bincike a kai, ba’a rasa samun wani ya gudanar da na shi nazarin a wannan fage, sai dai yadda kowa ya kalli aikin ya bambanbta, ko kuma akwai buƙatar a faɗaɗa nazarin a kai domin amfanin manazarta. Wannan aiki shi ma haka, an sami masana da manazarta sun gudanar da bincike da dama. Saboda haka za mu ƙyallaro kaɗan daga ciki domin su zama madubin wannan bincike da aka gudanar.

Daga cikin irin wannan bincike akwai aikin Bunza, (2006) da Alhasan da wasu, (1988) da kuma Rimma da wasu, (1983) duk ciki sun yi tsokaci akan abin da ya shafi al’ada da sana’a. Bunza, (2006) ya yi tsokaci akan al’ada inda ya taɓo abin da ya shafi sabo da, gado da, hali da tada. Sannan ya yi bayani akan abin da dangano kowane da kuma bayyana alaƙarsu a gargajiyance. Alhassan, (1988) ya tattauna ne akan abin da ya ta’allaƙa akan aure, da haihuwa, da tarbiyya, da sana’o’i, da sarautu da muƙamai a al’ummar Hausawa. Rimma, (1983) ya yi tsokaci kan abubuwan da suka shafi muhimman sana’o’i na gargajiya na Hausawa. Kasancewa wannan nazari an gudanar da shi ne akan abin da ya danganci kyautata ɗabi’a a rayuwar mata Hausawa ya zama wajibi a yi la’akari da waɗannan littattafai domin sun zama zakarun gwajin dafi.

A duk lokacin da ake magana akan kyautata ɗabi’a, ya zama wajibi mu yi batu akan irin darussan da aka samu ko ilimin da ake amfani da shi domin rayuwa ta zama mai albarka kuma mai manufa. Sakamakon haka, waɗannan aiki na Abbas, (2013) da Hassan, (2013) na da alaƙa ta kusa da wannan nazari da ake yi. Abbas, (2013) ya yi sharhi akan abubuwan da waƙoƙi suke koya wa yara, wanda ya ƙunshi: sanin dubarun rayuwa da fahimtar kyawawan halaye da ɗabi’u da riƙon alƙawari da ƙarin ilimi da fahimtar al’adunsu na Hausa. Ya yi bayanai masu gamsarwa da ankarar da jama’a fa’idarsu a rayuwar al’umma. Shi kuwa Hassan, (2013) bayani ya yi dangane da karatun boko a Arewa, ya bayyana tarihinsu a mataki daban daban na ilimi yana nusar da irin rayuwar da suke takawa tare da zayyana alƙaluma a ciki da jadawali ta fuskar ilimi. Sallau, (2013) ya bayyana abinda ya shafi tarbiyya wajen inganta rayuwar al’ummar Hausawa. Ya ankarar da cewa tarbiyya ma ginshiƙi ne wajen samar da rayuwa mai inganci.

Ta fuskar abin da ya shafi harshe an sami manazarta da suka yi nazari. An fahimci cewa babu yadda al’umma za ta iya kyautata rayuwarta ba tare da yin amfani da harshe ba, harshe ginshiƙi ne wajen kyautata zamantakjewar al’umma. Daga cikin irin waɗannan aiki da aka duba akwai na Dikko, (2021) da Abdul, (2016) da kuma Dikko, (2016). Dikko, (2016) ya yi nazari akan fa’idar harshe a rayuwar al’umma, in da ya taɓa batun abin da ya danganci ma’anar harshe, da zamantakewa, da kasuwanci, da kuma ilimi a rayuwar al’umma.

Ita kuwa Abdul, (2016) ta yi bayani dangane da bunƙasa kalmomin harshen Hausa ta fuskar faɗaɗa ma’ana. A cikin muƙalar an yi ƙoƙarin zayyana yadda ake faɗaɗa ma’anar kalmomin Hausa a bakin ɗalibai tare da kawo ma’anar wasu kalmomin. A muƙalar Dikko, (2016) ya yi bayani akan abin da ya shafi salon Hausar matan Hausawa, a nan ya yi ƙoƙarin bayyana yadda magana ta banbanta a tsakanin maza da mata. Sannan an bayyana irin lafuzza da mata ke amfani da su masu ɗauke hankali.

Magaji, (2017) ya yi tsokaci kan abin da ya ta’allaƙa akan wasu tufafin Hausawa na gargajiya da fasalolinsu. Ya nusar da cewa akwai tufafin gargajiya na mata waɗanda suke amfani da su tun tali-tali kamar su Fatari, da Bante, da Baƙurɗe, da Ɗanbarasoso da sauransu. Shi kuwa Yakasai, (2017) ya bayyana yadda auren Hausawa yake jiya da yau. Yana mai zayyana nau’o’insu tare da wasu al’adu da tasirinsu a auren Hausawa.

3.0 Ginshiƙan Kyautata Ɗabi’a a Zamantakewar Mata Hausawa

Abubuwan da ke tabbatar da kyautata ɗabi’a a zamantakewar mata Hausawa, sun ƙunshi muhimman al’amura kamar haka:

3.1 Addini

Addini ginshiƙi ne na rayuwar ɗan adam. Wajibi ne duk wani mai tunani da hankali ya san cewa akwai wanda ya halicce shi da kuma dalilin halittar sa. Addinin Bahaushe wanda shi ake bayani akai shi ne musulunci. Saboda mafi yawan Hausawa da garuruwan da suke zaune a ƙasar Hausa musulmai ne. Matan da ake nazarta a wannan aiki musulmai ne. A tsarin musulunci Allah shi kaɗai ne, ba shi da wani abokin tarayya. Babu yadda za mu iya tantance wannan batu sai mun san Allah, in kuwa wannan batu haka ne dole mu yi karatu, mu san Allah (SWT) ya umurce mu da mu yi, da kuma ya hane mu mu bari. Yin haka ne kawai zai taimaka mu samu kyawawan ɗabi’u da halaye nagartattu.

Mata Hausawa ba a bar su a baya ba musamman wajen neman ilimin addini da na boko. Tarihi ya tabbatar da cewa tun zamanin jihadin Shehu Usma Ɗanfodiyo an sami Asma’u ɗiyar Shehu tana karantarwa da yin wa’azi cikin waƙoƙi na wa’azi, fiqhu da tauhidi, da kuma al’amuran yau da kullum. Wannan bai tsaya ba har zuwa ƙarni 19 da ƙarni na 20 an sami mata irin su modibbo kilo da makamantarsu. Maƙasudan waɗannan faɗakarwa da karantarwa shi ne a kore jahilci a samar da ilimi ingantacce ga al’ummar mata Hausawa. A yau islamiyoyi da makarantun boko a ƙasar Hausa na taimakawa wajen inganta zamantakewar mata domin su tabbata har tsawon rayuwa. A cikin wannan ƙarni mata na iya gogayya da maza domin babu wani fanni da maza kan nazarta ba a sami mace tana iya yi ba. Domin tun daga aikin likita, da lauya, da alƙalanci da koyarwa a makarantu tun daga elimantiri har zuwa jami’a akwai mata da suke ba da gudummuwa wajen karantarwa. Haka abubuwan da suka shafi aikin rediyo da talabijin duk mata na yi. Da aikin zane – zane da ƙere - ƙere duk ba a bar su a baya ba.

Mata Hausawa suna ƙoƙarin ba da gudunmuwa a waɗannan fannoni da ma waɗanda ba a samu damar Ambato su ba. Saboda haka, wajibi ne ga kowace mace ta ɗabi’untu da halaye na ƙwarai, musamman ta fuskar addini domin su zama abin ado a rayuwarta da mu’amulanta da al’umma daga ciki akwai:

1.          Tsoron Allah

2.          Haƙuri

3.          Ilimi da aiki da ilimin

4.          Tarbiyya

5.          Sana’a

6.          Halin ƙwarai

7.          Jinƙai ga na ƙasa.

8.          Biyayya ga miji

9.          Kyakkyawar mu’amula

10.       Tallafawa juna

Waɗannan da aka kawo suna daga cikin kyawawan al’amura da za su inganta zamantakewar mata Hausawa ta fuskar addini.

3.2 Ilimi

Ilimi gishirin zaman duniya. Ilimi ginshiƙi ne wajen kyautata ɗabi’a a rayuwar matan Hausawa. Da mai ilimi da marasa ilimi basu taɓa zama dai – dai. Aiki da ilimi ya fi aiki da jahilci. A duk inda aka sami mace mai ilimi na addini ko na boko wato, zamani za ka ga ta ɗara ma wadda ba ta yi ko ɗaya ba. Ilimi a cikin rayuwar mata Hausawa na da matuƙar ƙima da daraja ta fuskar abin da ya shafi tsafta a cikin gida da waje. Ana iya tantance mai ilimi da wadda ba ta da ilimi. A rayuwar al’ummar Hausawa mace mai ilimi kan kasance kullum cikin tsabtar jikinta da wurin kwanciyarta da duk inda take mururin rayuwarta. Saboda haka, ta kan kasance abin ƙauna ga mijinta da sauran abokan hulɗar ta. Sannan ta na zama abin sha’awa. Har wa yau, ta fuskar abinci macen da ta sami ilimi kan taimaka wajen gina al’umma cikin ƙoshin lafiya da walwala. Wannan ya sanya a yau matan ke ɗaukar ilimi da daraja kuma suke gogayya da maza wajen neman ilimi domin inganta rayuwarsu. Kusan ana iya cewa a zamantakewar Hausawa babu mai son ya auri wadda ba ta da ilimi na addini ko na boko. Saboda haka, karatun boko na daga cikin martabobi da al’ummar Hausawa ke la’akari da shi kafin su auri mace, kuma, aiki na ɗaya cikin abin da kan taimaka a yau wajen inganta zaman aure.

A rayuwar Hausawa, musamman a halin da ake ciki a yau na tsadar rayuwa, matan da ke aiki kan taimaka wa mazajensu da dama wajen ciyar da gida da rufawa juna asiri a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso. Haka kuma ilimin da ‘ya mace ta samu kan taimaka wajen gina da samar wa yara ilimi nagartacce ta hanyar koyar da su da tuna musu abin da aka koya musu a makaranta. Saboda haka harshe na da matuƙar muhimmanci wajen samar da ilimi sai da shi ake iya karatu da rubutu. Da taimakon harshen karatu ake iya adana duk wasu muhimman bayanai na tarihi, da al’adu, da addini da kuma muhimman bayanai da akan tanada domin amfanin gobe. Sakamakon haka, karatu da ilimi na da fa’ida sosai a rayuwar mata Hausawa na yau da kullum.

Allah (SWT) da ya halicci ɗan adam ya umurce shi da ya yi karatu wato ya iya karatu da rubutu. Bunza, (2013: 218) Da mai halitta ya halicci halittarsa ta farko magana ya fara koyar da ita. Sai da baki ya biyu da magana aka fara zancen. Sanin yadda za’a yi bautar wanda ya yi halitta. Harshe shi ne ci gaba da ya fi kowane ci gaba fice daga aikin ci gaban ɗan adam. Wanda ya karanci harshe shi ne sarkin sarakuna cikin masu ilimi da basira. Yakasai, (2013) ya bayyana ma’anar harshe da kuma yadda ake adana harshe, da fa’idar adana harshen tare da yanayi da tsarin harshe a rayuwar al’umma.

3.3 Al’ada

A mahanga ta kusa wadda kuma aka fi sani da yin tsokaci a kai dangane da ala’ada ita ce duk wani abu da al’umma suka saba da yinsa a kai – a kai, wato wani abu da ya zama kamar ruwan dare a gare su, ba sa rabuwa da shi. In ana batun abin da ya danganci harshe a ɓangaren al’ada to ya zama dole a yi maganar ‘sabo’ da ‘gado’domin kusan suna tafiya da juna ne. Sannan kuma ya zama tilas a yi maganar kyautata ɗabi’a, saboda kowace al’umma tana tunƙaho da ɗabi’un da aka san ta da su, da kuma irin yadda take aiwatar da su cikin zamantakewa na yau da kullum. Duk waɗannan basu iya tabbata sai da gudummuwar harshe domin zance duk baya iya ginuwa sai an yi amfani da magana, ta hanyar furta kalmomi masu ma’ana. Saboda haka, in muna son mu ƙyallaro abin da ya shafi kyautata ɗabi’a a zamantakewar matan Hausawa dole mu yi la’akari da al’adunsu jiya da yau, wace irin rawar harshe ke takawa, kuma ta wace hanya?

A cikin al’adun gargajiya na Bahaushe akwai waɗanda suke ta’allaƙa ga mata. Alal-misali akwai bukukuwa da suka shafi mata a cikin gida: da bikin aure da na suna waɗanda suka ta’allaƙa ga mata Hausa a cikin gidaje, ba’a cika ganin maza ba kuma galibi ma matan ne ke gudanar da su. Sannan wani lokaci akwai wasannin gargajiya da suka shafi mata zalla. Hausawa kan ce ‘sabo jini ne ba ya sauyawa’.

Ɗabi’u kan inganta ta hanyar al’amuran da aka saba da su, wato ana gudanar dasu. In aka ɗauki bakin suna akwai abubuwan da ake yin la’akari ko ake aiwatar da su kuma suna da matuƙar tasiri. Daga ciki akwai abin da ya danganci ciyarwa a ranar, samar da gudummuwa don tallafawa waɗanda al’amarin ya jiɓanta, da kuma taruwa domin nuna zumunci da ‘yan uwantaka. Duk waɗannan ba abu ne na zubarwa ba a rayuwar matan Hausawa. Daga cikin fa’i’dojin da akan samu sun haɗa da ƙauna da son juna wadda aƙarshe kan ƙarfafa zumunta da kuma zamantakewa ta ƙwarai mai ɗorewa a cikin zamantakewar al’ummar Hausawa.

Sannan idan an duba gado da gargajiya tushen su abu guda ɗaya ne, domin daga gado aka sami gadajen ala’amari. Wanda al’ada ce take haifar da haka. In kuwa haka ne al’adar Bahaushe na ƙunshe da abin da ya danganci gado da gargajiya asalin tushe. Saboda haka wasu abubuwan da suka shafi gado da gargajiya nason su ta al’ada ne, kuma idan aka kwatanta al’adunmu na gargajiya zamu iske cewa akwai su da tasiri da fa’ida fiye da baƙin al’adu, wanda ko dai a sanadiyyar zuwan turawa aka same su, ko kuma zuwan baƙin ƙabilu Ƙasar Hausa.

Tarbiyya a cikin al’adun matan Hausawa babban ginshiƙi ne, domin duk wata al’umma mai tarbiyya takan zama abin alfahari kuma abin ƙauna. Da wannan ne ma ya sa ba a iya cewa kusa babu wata ƙabila ko al’umma da za ka ga ba ta yi auratayya da al’ummar Hausawa. Nagartattun halaye da ɗabi’un matan Hausawa suna bayyana ta fuskar mu’amula da ladabi da biyayya da sukan nuna wa sauran ƙabilu ko al’ummar da ba Hausawa ba. Haka kuma tsare mutuncinsu da mutuncin waɗanda ke tare da su.

Haka kuma idan aka waiwaya baya za a fahimci lallai, mu’amala abu ne da bai ɓoyiwa sai ta hanyar amfani da harshe domin duk abin da ya shafi tarbiyya da harshe yake tabbata, sannan a aiwace ne ake iya ganin haka. Wani abin sha’awa da tunƙaho a rayuwar mata Hausawa ita ce kunya da kara, da wannan mata Hausawa kan ce kunya adon mata”. Kunya kan sa mata su ɓoye sunan miji da sunan uwar miji da uban miji da kuma sunan ɗan fari. Wannan bai tsaya a nan kawai ba, ya kan sa faɗin magana sakaka, sai a sakaya magana in da aka ga bai dace a faɗi ba, ko kuma cikin waɗanda ba tsaranka ba. Bahaushe kan ce “magana zarar bunu ce” sai an tauna sannan a ciza. Mata Hausawa kan yi taka tsantsan wajen yin magana, kusan ma ana iya cewa basu cika yin magana ba sai in da ya zama dole. Kunya da kara a wajen mata ɗan juma ne da ɗan jummai, domin wasu lokuta mata kan yi kara, maimakon su aike wani abu da kansu ko furta wani abu sukan ƙaddamar da majiɓansu a madadinsu, wato a matsayin waliyi ko wakili. Wannan ita ma kyakkyawar ɗabi’a ce a zamantakewar al’ummar matan Hausawa.

3.4          Gaskiya

Abin da ke ƙara wa mace daraja a wajen mijinta da sauran al’umma a zamantakewar Hausawa ita ce gaskiya. Ɗabi’un da kan tabbatar da gaskiya ga mace sun haɗa da hankali, idan mace ta zama mai cikakken hankali da sanin ya kamata to za’a same ta da faɗin gaskiya a cikin zantukanta na yau da kullum. Sa’annan mutunci na ƙara wa mace sanin ya kamata da kare mutuncin rayuwarta a wajen mai gida da sauran jama’a. Duk macen da ke da mutunci ta kan zama mai ƙima da daraja a idon jama’a. A cikin zamantakewar mata Hausawa babu wadda take so a kusheta, ko a muzanta ta da halayen banza da ɗabi’u marasa kyau. Saboda haka mata Hausawa kan so a yaba musu. Yabo na daga cikin halaye dake tabbatar da kyawawan ɗabi’u a rayuwar mata Hausawa. Sanannen al’amari ne ƙarya ba abu ne da ake so mutum ya ɗabi’antu da shi ba, sai mutumin banza ke ƙarya. Saboda haka kyautata ɗabi’a na buƙatar lura da natsuwa da sanin abin da ya dace mutum ya faɗa kafin ya furta duk wata magana, a cikin jama’a domin samun daraja da ƙima a idon jama’a.

3.5          Amana

Amana shi ne ginshiƙi na kyautata ɗabi’a a zamantakewar al’umma. Wajibi ne mutum ya zama mai kiyaye amana ta hanyar magana da ake yi da shi, ko wani abu da aka bashi ijiya, ya tabbatar ya ije shi cikin aminci ba tare da cin amanar wanda ya bashi ba. Yana daga cikin halaye na ƙwarai mace ta kasance mai riƙe wa mijinta amana, duk wani abu na shi ta zama mai sirri da kaffa-kaffa da shi. Ba komai ne za ta sanar da kowa ba tsakaninta da mijinta. Sa’annan ko wajen zamantakewa na yau da kullum an fi son mace ta zama me kula da maganganunta na yau da gobe, kar ta zama mai yawan taɗi barkatai. Kuma duk abin da aka ce mata amana ta zama mai kiyayewa ga wanda ya bata amanar ko ma ba’a ce ba, ta zama tana kula da abin da bai shafi wani ba.

Macen da ta kasance mai riƙon amana a cikin harkokin ta na yau da kullum ta kan sami ƙima da daraja a wajen mijinta da sauran al’umma baki ɗaya. Rike amana ga jama’a zaɓi ne na Allah (SWT) sai yardajje mai hankali mai addini kan sami wannan baiwa ko matsayi.   

3.6 Haƙuri

A cikin kowace al’umma haƙuri na daga cikin ginshiƙai na samar da zaman lafiya da walwala da natsuwa da ci gaban tattalin arziƙi. Babban ginshiƙin zaman aure shi ne haƙuri, mata kaɗan ke iya zama da kishiya ko kishiyoyi. Amma namiji shi kaɗai ne, ita mace sai an nemo a kawo a bata, ta dafa, ta gyara sannan a ci. Kuma tarbiyyar yara daga gida take farawa, makarantar farko na yara tushen mata ne a gida. Saboda haka, wajibi ne ga mata su zama masu haƙuri ta kowacce fuska a zamantakewar su ta yau da kullum. Ba kowacce magana miji zai yi a bashi amsa ba, wani lokaci shuru ya fi shi. Kyautatawa wajen zamantakewa ga mata Hausawa na da matuƙar tasirin dorewar zaman lafiya a tsakanin ma’aurata da sauran jama’a. Sanadiyyar haƙurin da mata ke yi, ya sanya a kan cimma nasarorin zaman aure da mutunta juna, da daraja na gaba da biyayya ga malami da magidanta, rayuwa duk ɗan hakuri ne.

3.7 Kara

A al’ummar mata Hausawa, kara na tare da kawaici. Kara na daga cikin zkyawawan ɗabi’un zamantakewa na mata Hausawa. Ba wai sai abin da ya shafe ka ba kawai, zaka yi ruwa da tsaki ba, har na abokanan zamantakewar ka na yau da kullum, kama miji ko abokiyar zama ko maƙwabta ko abokanin hulɗoɗin yau da kullum.

Zamantakewar yau da gobe, cuɗa – ni – in cuɗe ka ce mutum bai iya ƙulla ma kansa komai sai tare da taimakon ɗan uwansa. Saboda haka mata Hausawa akwai su da kara tun daga biki na suna ko na aure, har ma da sauran bukunkunan al’adun Hausawa. Wannan kara bai tsaya nan ba, har ma abin da ya shafi baƙin ciki na mutuwa ko wani abu mara daɗi da ya shafi ɗan uwa a zamantakewar yau da kullum. Wannan na iya fitowa fili, in an kalli gudummuwar da mata ke bayarwa wajen sha’anunnuka na farinciki ko akasin haka. Sannan da irin ruwa da tsaki da suka nuna idan wani abu ya faru.

3.8 Kunya

Hausawa kan ce “kunya adon ‘yan mata”. Mata na taka muhimmiyar rawa wajen jin kunya a rayuwarsu ta yu da kullum. Ba kamar namiji ba, shi duk in da ya so zai yi magana kai tsaye. Ita kuwa mace sai ta ciza sannan ta busa. A zamantakewar mata Hausawa akwai kunya iri uku: na farko mace ta ji kunyar mahaliccinta wato Allah (SWT), na biyu kunyar mutane, wato duk abinda za ta yi wani ya gani ko ya ji ya ce tir, to ta guje shi, na uku ta ji kunyar kanta. Kunyar kai shi ne ita kanta ta tabbatar a zuciyarta yin wannan abun in ta yi da zai shafi ƙimarta da darajarta a idon jama’a, yin haka zai sa ta kauce wa duk wani abu mai rage mutunci da ƙimar ɗan adam. Sannan zai sa darajarta da ƙimarta ya ɗaukaka a idon jama’a kuma martabar ta ta ƙaru. Kunya na daga cikin imani da Allah da Manzon Sa, sai mutum mai son Allah da Manzon Sa ke kula da kunya, kuma ya ɗabi’antu da ita.

3.9 Sana’a

A cikin rayuwar al’umma akwai abin da mutum ke yi domin darajarsa ta ɗaukaka, kimansa ta samu matsayi, sannan rayuwarsa ta inganta ba tare da ƙasƙanci ba. Wannan bai wuce sana’a ba, domin sana’a ita ce aiki da mutum zai yi ya sami abinda zai ci, da abinda zai biya buƙatunsa na yau da kullum. Da wannan ne ma wata mawaƙiya Barmani coge ke cewa:

Ga misali daga waƙar Barmani Coge:

Waƙar Barmani Coge

Barmani: Don Allah maza a koyi sana’a.

Yan Amshi: Sakarai ba ta da wayo.

Barmani:             Ku mata ku zo ku koyi sana’a.

Da ban da sakarar mace sauna,

Wadda tana wurin miji su ukku

Duk saura suna ta sana’a

Matan gida suna ta sana’a

Yaran gida suna ta sana’a

Ita ko sai gari ya waye,

Ta tashi noƙai-noƙai,

Ta leƙa wancan ɗaki,

“Yaya ina kwananku?”

Yan Amshi: Sakarai ba ta da wayo.

 

Barmani: “Mun kwana lafiya mun tashi

“Ko za ki itace Yaya?”

Sai su ce ba za mu ice ba,

Kowa yana da sana’a.

Haka sai ta leƙa wancan ɗaki.

Yan Amshi: Sakarai ba ta da wayo.

 

Barmani: “Kai Yaya ba kwi komai ba?”

“Na dawo gidan da yunwar daji.”

“Yo ai muna ta sana’a,

“Kin san ba ma yi tuwo ba.”

“To ba ki da saurar dawa?”

“Sai ki je ki duba falo,

“Akwai ragowar dawa.” “

Ballagaza bazar-bazar ta ɓarza.

“Ke Kwari ina Tallen ki?”

“Ai Tallen ki ya fi saurin tafasa.”

Saboda haka, sana’a muhimman lamari ne ga rayuwar mata Hausawa. In kuwa haka ne, ashe kyautata ɗabi’a cikin rayuwar matan Hausawa tilas ne. A nan, ana iya cewa kamar yadda tarihi ya nuna asalin sana’a ta farko a rayuwar ɗan adam ita ce noma, daga noma aka gano shuka auduga daga nan saƙa ta samu asali. Wannan ya sa ake kyautata zamantakewa ta hanyar suturta kai da sakaya al’aurarsu da jikinsu maimakon yin amfani da ganye ko fatun dabbobi.

Akwai sana’o’i da dama a rayuwar mata Hausawa da suke yi domin samun abin masarufi. Duk da cewa wasu sana’o’in a yanzu ana musu ruƙon sakainar kashi. Misali ada duk inda ka je garuruwan Hausawa ba ka raba su da saƙa ta gargajiya, in da za ka ga mace ta saƙa zani ko majanyi ko tuma ƙasa, ko mayafi na rufa da dai sauransu. Wannan babban lamari ne a sana’a a ƙasar Hausa da mata ke yi. Sakamakon ƙaruwar kekunan saƙa da na ɗunki ya sanya abin ya sami tawaya, sai ɗaiɗai ke yin na gargajiya. Abin ban sha’awa a haka matan kan yi ɗinki na zamani ta hanyar amfani da kekuna. Har wa yau, mata Husawa kan yi sana’o’i daban – daban a cikin gida domin samun abin masarufi daga cikin irin sana’o’in da suke yi sun haɗa da Tuyan Ƙosai da Tuyan Waina da mashe da Ƙwal-Ƙwali da Fankaso da Tsatstsafa da Cin – cin da Alkaki. Sannan akan sami wasu matan suna sayar da abinci ko Ɗanwake da Tuwo da dai makamantansu.

Duk waɗannan abubuwa ne da kan taimaka wajen inganta zamantakewa da mu’amula ta ƙwarai. Zamantakewa da nuna ɗabi’u nagartattu kan taimakawa mata wajen samun nasarar duk wata sana’a da za’a gudanar. Ta hanyar sanadiyar sana’a akan samu fahimta da iya magana na ƙwarai, saboda samun kyakkyawan hulɗa a tsakanin mai saye da mai sayarwa. Sannan kuma makaranta ce ga waɗanda kan koyi sana’ar domin su iya riƙe kansu. Matan Hausawa bas u yarda da zaman banza ba.

4.0 Naɗewa

Wannan takarda an yi ƙoƙarin zayyana muhimman abubuwan da suka danganci kyautata ɗabi’un mata, waɗanda suke taimakawa wajen ɗaukaka darajar mace da ƙimanta a idon al’ummar Hasawa da ma sauran jama’a baki ɗaya. An nusar da cewa akwai al’adu na ƙwarai waɗanda suke da tasiri, sannan kuma akwai wasu sana’o’i da mata Hausawa kan yi domin kare mutuncin rayuwarsu, da ƙimarsu domin al’ummar Hasawa ba su yarda da zaman banza ba. Abin da ya shafi addini binciken ya tabbatar da cewa mafi yawan al’ummar Hasawa sun fi ga addinin musulunci, saboda haka addinin musulunci na tattare da nusar da al’ummar kyawawan ɗabi’u wanda kuma matan Hausawa sun ɗabi’antu da haka.

A ƙarshe fahimci ilimi na boko da addini kan taimaka wajen kyautata ɗabi’un mata da zamantakewar su a cikin rayuwa mai albarka. A nan, ana iya cewa ya zama wajibi ga manazarta su faɗaɗa bincike a sauran ɓangarorin kyautata ɗabi’un mata a adana su domin zama kundi. Wannan zai fa’idantar a sami abin karatu da kuma abin koyo ga masu zuwa a nan gaba.

Daga cikin abubuwan da ke tabbatar da kyautata ɗabi’u a wajen mata Hauswa sun haɗa da: gaskiya, da addini, da amana, da haƙuri, da kara, da kunya, da ilimi. Duk macen da ta ɗabi’antu da waɗannan halaye ta tsira kuma ta zama cikakkiyar mace da kowanne ɗa namiji zai so ya aura.

Bugu da ƙari, an gano lallai gaskiya na daga cikin halayen kyautata ɗabi’a a zamantakewar mata Hausawa. Komai za ka faɗa, faɗi gaskiya domin faɗin gaskiya ɗabi’a ce ta ƙwarai. Har wa yau, riƙon amana ga mace na ƙara mata daraja da ƙima a idon jama’a da mijinta. Sannan an fahimci cewa haƙuri, na daga cikin ginshiƙan da mata Hausawa kan ɗabi’antu da su, su cimma nasarar zamantakewar aurensu da mazajensu. Haka kuma kara ma ɗabi’a ce mai kyau wajen kyautata zamantakewar mata Hausawa kamar yadda nazarin ya ankarar. Babu shakka, kunya babban lamari ne a abubuwan da ke haifar da kyautata ɗabi’a a zamantakewar mata Hausawa wanda wannan aiki ya nazarce su baki ɗaya kuma ya bayyana yadda suke.

Manazarta

1.       Abbas, H. (2013). Darussa daga Wakoki don yara na M.B. Umar. Studies in Hausa Language, Literature and Culture. In The 1st National Conference Center for the Study of Nigerian Languages (pp. 1-10). Kano: Bayero University.

2.       Abdul, F. I. (2016). Bunƙasa Kalmomin Harshen Hausa ta Fuskar Faɗaɗa Ma’ana: Tsokacikan Ɗaliban Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi da ke Kano. Harsunan Najeriya, 26, 43-54. Center for Research in Nigerian Languages, Translation and Folklore. Kano: Bayero University.

3.       Alhassan, H., Musa, U. I., & Zuruk, R. M. (1998). Zaman Hausawa (2nd ed.). Lagos: Islamic Publishing Bureau. Permitted by Academiy press Ltd.

4.       Bunza, A. M. (2006). Gadon Feɗe Al’ada. Lagos: Tiwal Nigeria Limited.

5.       Bunza, A. M. (2013). Don me ake karatun hausa? Harsunan Najeriya, 23(Special Edition), 67-76. Center for the Study of Nigerian Languages. Kano: Bayero University.

6.       Dikko, A. L. (2016). Salon Hausar Matan Hausawa. Degel. The Journal of the Faculty of Arts and Islamic Studies, 5(2), 145-158. Sokoto – Nigeria: Usman Ɗanfodiyo University.

7.       Dikko, A. L. (2021). Fa’idar Harshe ga Rayuwar Al’umma. The Journal of the Faculty of Arts and Islamic Studies, 19(1), 32-45. Sokoto – Nigeria: Usman Ɗanfodiyo University.

8.       Hassan, M. B. (2013). Karatun Boko a Arewacin Najeriya. Studies in Hausa Language Literature and Culture. In The 1st National Conference. Center for the Study of Nigerian languages (pp. 20-30). Kano: Bayero University.

9.       Magaji, A. (2017). Wasu Tufafin Hausawa Na Gargajiya da Fasalolinsu. Algaita Journal of Current Research in Hausa Studies, 1(10), 76-88. Kano: Bayero University.

10.    Rimma, B. M. (2009). Zama Inuwa, A. Mutum da Sana’arsa Musawa. Zaria: Northern Nigeria Publishing Company Ltd.

11.    Sallau, B. A. (2013). Tarbiyyar Hausawa a Matsayin Ginshiƙi na Samar da Ingantacciyar Al’umma. Studies in Hausa Language, Literature and Culture. In The 1st National Conference. Center for the Study of Nigerian Languages (pp. 55-66). Kano: Bayero University.

12.    Yakasai, M. G. (2017). Auren Hausawa Jiya da Yau. Algaita Journal of Current Research in Hausa Studies, 1(10), 112-125. Kano: Bayero University.

13.    Yakasai, S. A. (2013). Adana Harshe: Yaya yake kuma menene fa’idar sa? Harsunan Najeriya, 23(Special Edition), 89-99. Center for the Study of Nigerian Languages. Kano: Bayero University.

Post a Comment

0 Comments