DABI'A IRIN TA MACE: Mace a dabi'arta tana ba wa abubuwan da suka shafi zuciya mahimmanci sosai, ta tsananta damuwa a kan abubuwan da namiji sam bai daukarsu wani abu, da wani saurayi zai nemi wata budurwa soyayyar ta ƙi hannu in ya ce zai nemi ƙawarta dukansu biyun na iya fassara hakan da cewa cin amana ne ba ƙarami ba. Ta ya zai nemi wance don kawai abin bai yi kyau ba ya zo ya nemi ƙawarta? Da wannan fahimtar ko mace ta dade ba miji ba za ta amince wa mijin ƙawarta ba komai ƙaunar da take masa kuwa, ba ita na nuna tana son sa ba shi ya kawo kansa.
Bincike ya tabbatar da cewa an samu ba a wuri guda
inda mace ke roƙon
saurayinta da cewa ya hada ta da ƙawarta ya aure su tare saboda fahimtar
juna dake tsakaninsu. a kan sami yardar duka bangarorin a wasu lokutan, ko ka
ga ƙawar ta ƙi amincewa saboda tsoron hattannan ta kishi dake zuciyar mata, kishi nan
gaba ya tarwatsa alaƙar dake tsakaninsu. Ni dai da ido na ga wace ta
nemi maigidanta ya auri ƙawarya, an tabbatar har yanzu suna zaune lafiya.
In hakan na faruwa a ina ya zama cin amana?
Wasu matan kan ce: "Ba ƙin kishiya nake ba, amma
wa ya san abin da za ta shigo wa murum da shi?" In dai rashin sanin ne
abin tsoro ai kowace mace ta fi kowa sanin ƙawarta, sanayya, ƙauna
da taimakekeniya duk suna tsakaninsu ba gwara a auro ta ba da dauko wace ba a
san komai nata ba? In mata suka ce sam ba su yarda da wannan ba to gaskiya baƙin
kishi ya zama dabi'a a wurin wasu matan za su yi kayansu da duk wace maigidan
zai auro, ba maganar cin amana ba ce ko sanin sirri ko wani abu, wadannan ana
amfani da su ne kawai a matsayin makaman yaƙi.
A wannan nazarin an kawo kishin mace a matsayi
wata halitta, dukbmata suna da shi, sai dai wasu suna iya mallakar kansu duk
lokacin da suka ji shi yana ƙoƙarin tasowa, da ma akwai hanyoyi sanannu da muka
ambata a baya waÉ—anda
kishi kan biyo ta su ya fito waje, kodai ta hanyar tsoro, ko hassada, ko ƙiyayya,
ko raini da dadai sauransu. Ta hanyar tsoro dai mace kan jin cewa wancan ta fi
ta wani abu, don haka za ta iya ƙwace mijin ko ba joma ko ba dade. Kishi ya mallake
zuciyar da don haka ba mai zai hana ta jin cewa duk abin da za ta shigo da shi
ita ma tana da shi?
Ko ta yi amfani da dadewar da ta yi da maigidan
wurin sanin yadda za ta ma'alance shi a fiye da yadda wata baƙuwa za
ta yi. Sai dai in kishi ya rufe mata ido ta ari na suautaccen kare da kan bar
zo ya koma tunkuyi a lokacin da matsaloli suka taso masa. Zancen raini kuwa ba
amaryar ce ke raina uwargida ba, ita uwargidan ce ke kallon cewa gidan fa nata
a ko'ina yake kuwa tunda maigidan ita ya fara aure, amma ba ma wannan ne
matsalar ba sai ta fara cewa amaryar na ƙoƙarin ƙwace maigidan ne don
haka za ta tashi a tsaye ta kare maigidanta. A wannan matsayin duk abin da za
ta yi mutane na fassara ahi da kishi ne.
Dangane da maganar raini a zahiri kuwa, in
uwargida ta fara jin ta fi ƙarfin wace za a auro mata ta kowani bangare, ta
raya wa kanta cewa ta fi ƙarfin ta yi kishi da wancan, ta ce "Wai me
malam ya gani a jikin wance da har ya tafi a rude ya dauko ta? Wai duk ya rasa
wace zai auro sai wance? 'Yar talakawa jinin matsiyata? Ƙawaye su zuge ta da cewa
ya yi niyyar ya wulaƙanta ta ne ya sa haka. Alhali ita ce ma ke raina
matar da za za shigo, tana ganin ƙimarta ba ta kai yadda za ta zama kishiyarta ba.
Sai ta yi wa maigidan iyaka da cewa ya auro kowa amma banda mace irin wannan,
ba za ta riƙa gogayya da ita a matsayin kishiya ba?
A nan ta raina rukunin amaryan ne, to tunda ta
raina ta ne ba sai ta ƙyale ta ta ci arziƙinta daidai ƙarfinta
ba? Sai kuma ta juyo ta yaƙe ta, kodai in ba ta shigo ba ta hana ta shigo ba
ta ja mata layi, in kuma ƙaddara ta sa an auro ta, sai ta fara ƙoƙarin
cutar da ita wanda a ƙarshe in ta ji wuya ta yi wuya ta ƙara
gaba. Ko dai kullum zagi a habaice, wata har duka takan yi, ko ta sa mijin ya
wulaƙanta ta in ta fi ƙarfinsa, ko ta turo mata yara su yi mata dibar
albarka. In ba an yi sa'a ta yi saurin gogewa ba duk za ta lalace ta fita hayyacinta
saboda fitinar kishiya.
Babban taimakon da maigidan zai iya yi
amaryaryarsa a irin wannan matsayin shi ne ya daga darajarta a gaban uwargidan,
ya nuna cewa a wurinsa dukansu darajarsu daya ce, ya auro su ne din yana ƙaunarsu,
kuma ba wata halitta ta jiki wace wata ke da ita wata ta rasa. Don haka dukansu
matansa ne yana ƙaunarsu daidai wa daida. In aka lura da wannan ma
tana kishi da ita ne don dabi'a ce halittata tare da ita amma ba wai ta raina
matsayinta ne ba, wanda ya raina kasuwa ai ko sautu bai badawa da in ta ajiye
ta gefe guda ko tuno ta ba za ta sake yi ba. Daukan mataki a kanta na nuna ta
kai yadda za a yi ja in ja da ita.
A nan Zan Dakata Sai Mun HaÉ—u a Rubutu Na Gaba
**************************
Daga: ✍ Baban Manar AlÆ™asim
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin rubuce-rubuce da ke cike da faɗakarwa da ilimantarwa, waɗanda ake samarwa daga Zauren Markazus Sunnah. Ku bibiye su a kafafensu na sada zumunta domin samun ƙarin bayani. Amsoshi ba ta da haƙƙin mallakar waɗannan rubuce-rubuce, amma tana ɗora su ne da izinin Baban Manar Alƙasim.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.