13) Ji da kai gami da alfahari: Mai baƙin kishi takan gaya wa kanta cewa ta fi duk wace za ta auri mijinta komai, koda kuwa a zahiri ba haka din ba ne, za ta yi ƙoƙarin mamaye ƙwaƙwalwarta da nuna mata cewa ta fi ta din, ta yi ƙoƙarin gamsar da ita ta kowace hanya, in abinci ta dafa sai ta nuna mata ba wata 'ya mace da za ta iya yin abincin da maigidansu ke so kamarta, shi ya sa bai son cin wani abinci sai nata. Za ta yi ƙoƙarin ƙirƙiro wasu labarai ta bayar wadanda za su fito da ƙwarewarta a fannin. Wannan duk za ta yi su ne don gamsar da kishiyar cewa ba za ta iya dafa abinci kamar yadda take yi ba.
Har da ƙwarewar da take tinƙaho da ita, da wahala ta koyar da abokiyar zamanta yadda take dafa abin da maigidan yake so, tabbas wannan sirri ne kamar yadda suke fada domin in tuwo ne za ka taras wani maigidan ya fi son a tuƙa shi kamar dutse, wani kuma ruwa-ruwa kamar fate yake so. Koda kunu za a dama za ka taras wani yana son ya gansa kitiburbur ya yi kauri, wani kuma ya fi son ya sha shi ruwa-ruwa, kafin amarya ta gano irin wadannan sirrorin yana da wuya, don uwargidan in mai mugun kishi ce za ta ƙi dora ta a kan hanya, shi kuma maigida saboda kawaici bai iya nuna wa amaryar cewa ba ya jin dadin yadda take yi.
Duk yadda aka miƙa masa haka zai karba da
haƙuri, addini ya ja kunnen maza da kar su riƙa raina abincin da aka
dafa musu, don haka ba sa iya magana. Wace take ganin abincinta ya fi na kowa
da wadannan sirrorin take amfani amarya ba ta sani ba, da za ta gaya mata da
wahala a sami bambanci a abincin. Wani namijin bai son man-gyada saboda
shawara, ina da abokin da sam-sam bai cin manja, wani bai son mai da yawa a
abinci, shi kuma mai na ƙara ƙamshi, dandano da kyau a ido. In amarya ta zo da ƙwarewarta
daga gida ta cimma maigidan ba haka yake ba da wahala abincinta ya burge shi
komai dadinsa, sai ta yi yadda yake so, uwargidan kuma ta sani.
Akwai namijin da bai son magi da yawa a abinci, na
taba ganin wanda yake ta fada wai an saka masa seasonings a abinci shi kuma bai
so, to wani irin girki ne kika iya wanda wancan ba ta san shi ba? Ki ba ta
sirrin mana ki gani in ba ta yi ba? Duk wani alfahari da taƙama a
gaban kishiya na iya abinci na bayan wannan ne: A dafa shi ya dahu sosai, a
zuba kayan ƙamshi da na dandano, a inganta shi da wasu
ganyayyaki kamar su latas, cucumber da danyen tumatur, an gama.
Duk wace ke son tsallake wannan ta riƙa sa
maigidanta a gaba na dan lokacin da zai fara cin abincin, ta karanci fuskarsa,
ta saurari ra'ayinsa. In ta tambaye shi "Ya yi kuwa?" Amsar kawai
"I" koda bai yi masa ba, amma yadda ake tambayar maigida shi ne: In
kika yi tuwon da kauri sai ki ce masa "Tuwon ya yi kauri amma da na so in
yi shi ruwa-ruwa ne ban san wanda ka fi so ba, ko nan gaba kar ya yi kaurin
haka?" Anan za ki iya samun abin da yake so, don zai ce miki "Yauwa
ya fi haka kauri" ko "Yauwa ki yi shi ruwa-ruwa" kin ga kin sami
abin da yake so.
Duk wani nau'in abincin da kike son sanin
ra'ayinsa ta haka za ki fito masa. Na farko kenan wanda ya fi kowanne inganci,
na biyu kuma ki tambayi kishiyar za ta gaya miki, in kika ga abubuwan da take
gaya miki sun bambanta da wadanda take yi to ki sa ido sosai, sai ki dawo zabin
farko na fuskantar maigidan kai tsaye, ta haka ne buƙatunki za su biya gaba
daya. In kina sauraron tallace-tallace a talabijin za ki ji mata na cewa
"Dandano kaza shi ne sirrina" tabbas zabin magi da kayan ƙara ƙamshin
miya ko dandano sirri ne na girki, kar ki tsaya sai kishiya ta gaya miki ga
yadda za ki gyara girkinki.
Sai alfahari da kudi ko sana'a ko dangi, yadda
wasu lokutan mace za ta riƙa goranta wa kishiyarta, macen da zuciyarta ta
mutu ta fi shan wahalar kishi, in tana da ƙarfin halin da za ta
buda wa kanta hanya ta wurin zaben sana'ar da za ta kama, ko karatun da za ta
shagala da shi don isa ga biyan buƙatarta ta huta. Ba ta da lokacin da za ta bata don
wata, abin da za a nuna mata kawai kudi ne ita ma tana nemansu sai dai a nuna
mata yawansu, duniya kuma duk ta yaddaza ka kalle ta wani ya fi wani, in kana
da wadatar zuci an gama.
In kishiya za ta shekara tana cewa an fi ƙaunarta
kar wannan ya ba ki tsoro, in abin da take fadi gaskiya ne duba me ya sa? In
kika gano shi kawai ki gyara, a shimfida ne? Ado ne? Abinci ne? Tsabar ladabi
da biyayya ne? Taimako da tausayawa ne? Ko ma meye koya kawai, in ma ba da
gaske ba ne bar ta ta yi ta shirmenta. Babu ta inda ba a fito wa kishi, za ta
yuwu duk abin da take fada sam-sam ma ba haka ba ne, so take ta tura ki wani
lungun ta ba ki tsoro ki ja da baya ki sakar mata komai.
Anan Zan Dakata Sai Mun Haɗu a Rubutu Na Gaba
**************************
Daga: ✍ Baban Manar Alƙasim
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin rubuce-rubuce da ke cike da faɗakarwa da ilimantarwa, waɗanda ake samarwa daga Zauren Markazus Sunnah. Ku bibiye su a kafafensu na sada zumunta domin samun ƙarin bayani. Amsoshi ba ta da haƙƙin mallakar waɗannan rubuce-rubuce, amma tana ɗora su ne da izinin Baban Manar Alƙasim.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.