Ticker

6/recent/ticker-posts

Kîshi Rahama Ne Ko Azaba // 53 - Sifofin Mai Nuna Kishi Da Hassada

A baya dai mun yi qoqarin bambance kishi na mazauna wuri guda masamman mata da miji, ko mace da kishiyarta ko tsakanin masoya, yanzu kuma za mu yi maganar yadda ake amfani da hassadar kai tsaye wajen nuna kishi:

1) Duk wani mutum na buqatar ci gaba ne, ko mace a gidan miji abin da take buqata kenan, duk matar da aka fara auro ta ta riga ta yi gaba, sai dai in ba ta kyautata zamanta da maigidanta ba ya zamanto ba ta sami zuciyarsa ba, yanzu kam da wata ta zo kuma ta ga lallai za ta iya mallaka nan ne matsala za ta shigo.

Amma ki zauna da mutum kin san komai nasa ciki da bai, wata qila ma kin haifa masa yara, su ne manya a gidan tabbas in wata ta zo daga baya wace ba wani abu nata da ya bayyana kuma kina tsoron ta har kina daukar wasu matakai tabbas akwai matsala. Ai babba a ko'ina take babba ce, dole qaramar ta girmama ta saboda rigaye a rayuwa wani abu ne. In ta kasa riqe girmanta yadda qaramar za ta yi koyi da ita, ta dawo tana amfani da girman kai a matsayin wani makami da za ta yi fada da qaramar to alkadarinta karyo qasa warwas.

Domin qaramar za ta dauke ta a matsayin abokiyar karawa daidai da ita, saboda ta yanke cewa kishi za su yi ba zaman girmamawa ba, irin wannan cikin sauqi baqo zai gane irin zaman doya da manjan dake tsakaninsu. Kamata ya yi a ce babbar da ma tana da tsarinta yanzu kuma za ta dada inganta shi a dalilin samun abokiyar zama, ba za ta bari a sami wata kafa da qaramar za ta raina ta ba, maigidan kuma tun da ya nuna qaunarsa ga amaryar duk wata matsala tsakaninsu za ta dinke ta, shi kenan an sami mafita.

Da ma amaryar baquwa ce, ba ta san komai ba, yanzu za ta fara dauka a wurin uwargidar, don haka in ta kwaikwaye ta ba wani abu ba ne, amma uwargidar da ta san me za ta koya wurin wace ta shigo yanzu? Sai dai in akwai abubuwan da ta gano cewa suna buqatar gyara sai ta gyara, misali uwargida ta dade tare da maigidan, ta yi manyan 'ya'ya ta fara tunanin cewa ita ta tsufa, kwatsam sai maigida ya dauko mata qaramar yarinya, wankan yau daban na gobe daban, babu laifi ta gyaggyara abin da aka bari.

Amma in akwai wani dauri na ture a ga tsiya da yara ke yi, uwargidar ta daura ita ma ta fito tsakar gida tana cewa "Yauwa ai ba an fi mu girman kai ba ne, atamfa kuma gidan uban kowa akwai! Duk tsiyar mutum sai dai ya biyo baya wallahi na gaba ya riga ya yi gaba!" Wannan takalar fada ce ba kwaikwayo ba, ko yi daurin da wahala ya yi kamar na yarinyar, kenan dole raini ya shigo, yarinyar za ta fara nuna cewa ita 'yar zamani ce, tun uwargidan na iya kwaikwayonta a wasu abubuwan har a zo inda za ta gaza, domin akwai abin da ko kadan ba za ta iya dauka ba, saboda zamaninta ya wucenan, qila ko yaranta ba za ta bari su yi a gidan yawa ba.

Misali: Qaramar na iya sanya gajeren wando da dan shirt ta leqo qofar daki yadda uwargidan za ta gani daidai lokacin da maigidan ya shigo. Wannan shirme ne daidai da shekarunta, ko maigidan zai yi mata hanzari, ta uwargidar za ta kwaikwayi wannan? Ta riga ta wuce shi, sai dai ta tuno wani nau'in da maigidan yake so, in kuma ta yi tabbas za ta burge shi. Daganan sai ta fara qoqarin tuno wasu abubuwan wadanda za ta sami damar tarairayan masoyinta a sifar da ta saba ta hanyar da take so, ya fi a ce ta koma kwaikwayon abin da ba za ta iya ba.

A zahiri kyau dai ba qarya ba ne, koda ba mu karanta cewa an qawata wa maza son mata ba muna gani a zahiri yadda hankulan mazan ke komawa kan kyawawan, shi kuma kyawunnan iya wanka ne, da gyaran jiki, ba wai halittar fuska ba ce kadai, kowa sheda ne mutum na da kyakkyawar a gida amma ka ga yana kula wace ba ta kai ta komai ba a waje, kenan akwai wani kyawun wanda idon mutane bai gani sai shi wanda ake yi dominsa.

A taqaice kawai duk kyawun da mace ke da shi dole sai ta qara da wanka, idan ma a fuska ba za a iya jayayya da wata ba sai ta bar fuskar ta koma wani wuri, a matsayin uwargida na tsohuwar hannu ta san abubuwa da dama wadanda maigida na buqatarsu sosai, sai ta koma can a yi  ta yi, in an yi mata tsiyar fuskar sai ta yi dariya ta watsar. Da haka kuma za ta sami biyar buqata ba boka ba malam, sai dai a yi ta zarginta da cewa sihiri ta yi masa, wannan ma ya ishe ta, amma in ta koma kwaikwayo ai an fado.

Anan Zan Dakata Sai Mun Haɗu a Rubutu Na Gaba,

**************************
Daga:  Baban Manar Alƙasim
**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin rubuce-rubuce da ke cike da faɗakarwa da ilimantarwa, waɗanda ake samarwa daga Zauren Markazus Sunnah. Ku bibiye su a kafafensu na sada zumunta domin samun ƙarin bayani. Amsoshi ba ta da haƙƙin mallakar waɗannan rubuce-rubuce, amma tana ɗora su ne da izinin Baban Manar Alƙasim.

Kishi Rahama Ne Ko Azaba


Post a Comment

0 Comments