Ticker

6/recent/ticker-posts

Ina Mata Masu Neman Jari? Ga Hanyar Samun Kuɗi

Da gaske nake zan taimaka muku.

Amma ba da kuɗi ba dan ni ma nema nakeYanzu ma neman su zan fita. Ba kuma sisina zan ba ku ba.

Amma maganar gaskiya zan ba ku sirrin neman kuɗi ne wanda yake kawo kuɗi cikin sauƙi.

Kin san kargo?🌳 Ke ba kargo kawai ba, duk wata bishiya da kika sani da ba za ta cutar da mutane ba, to kina iya amfani da ita, domin magani ce.

Ki sa yara su sassaƙo miki, ki ɓare ki shanya, ya bushe.

Kin san mata da kwaɗayi sai ki saka zuma na nera ɗari da hamsin (#15) a ciki. Ki ɗan yayyafa a kai yadda zai yi ɗan zaƙi. 😋

Sai ki daka, ki tankaɗe, ki ɗaɗɗaura a takarda ba a leda ba, irin yadda bokaye ke ba da magani 👌

Ke kuma sai ki ce daga Maraɗi ake kawo miki ko daga Agadas. A iya baƙi, kada ki kai hakan zuciya.

Sai ki ce musu yana gyara mace sannan yana maganin mallakar miji da jan hankalin mai gida 🤕

Ki ce ba a sha sai an yi brush kuma ki ce maganin ba ya aiki sai mutum ya sa a zuciyarsa kuma yƙudurce maganin zai yi masa aiki 🙏

Wallahi summa tallahi za ku sha mamaki idan kuka gwada 👌 ba na son ganin mutanenmu na zaman banza yasin😔

In dai kin cire tsoro za ki iya 💪na san ba ki taɓa jin an dawo da magani an ce a ba da kuɗi ba.

Akwai wasu ma bayan wannan🙏

Wata kila gobe in koya muku barbaɗe da ake yi wa mai gida, amma na masu kishiyoyi ne 🧐

Allah na tuba ba, wace rana ce jemage bai gani ba?

Daga Taskar: 

https://barkwanci.blogspot.com


Post a Comment

0 Comments