Ticker

6/recent/ticker-posts

Labarin Wata Waliyyiya (Barkwanci)

Tana kwance a kan shimfiɗar ajali ta ce: “Habibina, in na mutu zuwa yaushe za ka sake wani auren?”

Yana kuka ya ce: “Zuwa lokacin da ƙasar kabarinki za ta bushe.” Ta yi murmushi ta ce: “Ka yi alƙawari?” Ya ce: “Ƙwarai ma kuwa.”

Bayan ta rasu sai da ya shafe fiye da shekaru 5 yana zuwa maƙabarta amma abin mamaki kabarin bai bushe ba.

Allahu Akbar! Ya yi mamaki sosai kuma ya ƙudurce a ransa matarsa waliyyiya ce.

Wata rana ya yi sammako don ziyarar kabarinta, sai ya ci karo da ɗan uwanta, suka gaisa. Ya ce: “Ka zo ziyarar ‘yar uwarka ke nan?”

Sai ya ce:

“Na dai zo don cika wasiyyar da ta mutu ta bar mini. Ta yi mini wasiyyar kullum da sassafe na zo na jiƙƙasar kabarinta, hakan zai sanya ta kwanta cikin nutsuwa. Shekara da shekaru ke nan ina wannan aikin.”

Wani aikin sai mata...

Labarin Wata Waliyyiya

Post a Comment

0 Comments