Ticker

6/recent/ticker-posts

Gudummawar Gwamnatin Nijeriya Ta Arewa Ga Daidaita Rubutun Hausa

Duk da kasancewar akwai ƙa’idojin rubuta Hausa da Gwamnati ta aminta a yi amfani da su, akan samu bambace-bambance wajen yadda wasu ke rubuta Hausa, musamman a fagen haɗa wasu kalmomi da raba su. Ga kuma kullun safiya harshen sai daɗa bunƙasa yake ta hanyar sababbin kalmomin Turanci da ke shiga cikin harshen Hausa ba kama hannun yaro. Don a hanzarta shawo kan waɗannan matsalolin da ke barazana ga rubutun Hausar boko, sai wani ɗan Majalisar Wakilai ta Jahar Arewa da ke Kaduna, da ke wakiltar Lardin Bauchi mai suna Malam Bawa Bulkacuwa ya gabatar da shawarar cewa, “ya kamata a ba Mai Girma Gwamna shawarar a kafa wata hukuma da za a kira Hukumar Harshen Hausa.

Gwamnatin ta karɓi kiran, ta kuma kafa hukumar da aka kira da suna Hausa Language Board wato Hukumar Harshen Hausa, a shekarar 1955 domin daidaita ƙa’idojin rubutun Hausa. Hukumar ta yi ƙoƙarin tace kalmomin da harshen Hausa ya aro daga wasu harsuna kamar Larabci da Turanci. Ta kuma gudanar da wasu ayyukan da suka taimaka wajen kyautatuwar rubutun harshen Hausa.

Hukumar ta ɗauki ma’aikata da dama, shahararru daga cikinsu sun haɗa da Alhaji Isa Kaita da Alhaji Aliyu Makaman Bida da Alhaji Tukur Sarkin Yawuri da Alhaji Abubakar Imam da Mr. C. Sanderson da Alhaji Abubakar Dokaji da Alhaji Abdulmalik Mani da Malam Maigari Yusuf da Mr. J. W. Court a matsayin sakataren hukumar.

Daga cikin ayyukan da hukumar ta aiwatar sun haɗa da:

1. Tabbatar da littafin ƙa’idojin rubutun Hausa mai suna, Rules For Hausa Spelling, tare da yi masa wasu gyare-gyaren da suka shafi haɗa kalmomi da raba su. Misali, a riƙa raba lamirin mutum da na lokaci kamar a irin waɗannan jumlolin:

a)      Abin da su ke so  ba Abin da suke so ba

b)     Sa’ar da ya ke zuwa ba Sa’ar da yake zuwa ba.

Kalmomi irin su saboda da kalmomin jama’u irin su koyaushe da kowane da ko’ina sun raba su kamar haka:

a)      Ko yaushe ba koyaushe ba

b)     Ko wane ba kowane ba

c)      Ko ina ba ko’ina ba

d)     Sabo da ba saboda ba

Haka sun zartar da hukuncin harrufa za su daina sajewa a cikin kalmomi irin waɗannan:

a)      duk da haka ba dud da haka ba

b)     ya fitar da mu ba ya fitad da mu  ba                                

Kamar yadda Kirk-Green (1964 p. 194) ya nuna. An ma buga gyare-gyaren da hukumar ta aiwatar game da ƙa’idojin rubuta Hausa a Mujallar Gwamnatin Jahar Arewa, wato Northern Nigeria Gazette, Northern Reginal Notice No.31 ta ranar 22 ga watan Janairu, shekarar 1957, kamar yadda Yahaya, (1988 p. 129) ya bayyana.

1.      An cimma matsayar yin amfani da wasu kalmomin bayanin nahawun Hausa kamar:

·         Ismi    ya koma         suna

·         Fi’ili    ya koma         abin da za a yi

2.      An tsara littafi wanda ya ƙunshi jerin kalmomin da harshen Hausa ya ara fiye da ɗari biyu da hamsin (250) waɗanda aka kira da suna Alphabetical List of Words Impoted into Hausa. Kamfanin ɗab’i mai suna: Baraka Press ta buga a shekarar 1958, kamar yadda Yahaya (1988 p. 129) ya nuna.

3.   An tsara littafin keɓaɓɓun kalmomin Hausa, da aka kira da suna Glosseries of Technical Terms. Wannan littafin yana ɗauke da kalmomi dubu ɗaya da ɗari ɗaya (1100) da suka danganci keɓaɓɓun kalmomin da ake amfani da su a sassan ma’aikatu daban-daban.

Wannan ba ƙaramar gudummawa ba ce ga harshen Hausa da su kansu al’ummar Hausa.

Domin irin wannan rawar da Turawa suka taka ta taimaka gaya wajen taskace tarihi da fasahohin magabatanmu tare da ƙara wa harshen Hausa ƙima a idon duniya, har al’ummomi daban-daban sun duƙufa a fagen nazarinsa.

Dr. Adamu Rabi'u Bakura
Department of Languages and Cultures
Federal University Gusau, Zamfara State, Nigeria
08064893336

Post a Comment

0 Comments