Shawarata Ga Ɗalibai
Abin da na fahimta shi ne, mutane a kowane mataki sun rabu zuwa kashi biyu game da abin da ya shafi karatu. Akwai waɗanda suka yi imani da shi. Akwai kuma waɗanda suka ɗauke shi a matsayin abin da a Nigerian English ake cewa "formalities." Sau da dama akan samu abin da ake kira "conflict of interest" tsakanin masu waɗannan ra'ayoyi guda biyu a kowane mataki. Misali:
* Yayin da rukunin farko ke
ganin dole ne a dage a fahimci karatu yadda ya kamata, rukuni na biyu na ganin
wannan ɓata
lokaci ne tsantsa.
* Yayin da rukuni na farko
ke ganin cin mutunci da amanar ilimi ne yin sakaka da harkar karatu yadda za a
kasa bambance tsakanin masu hazaƙa da
ragwaye, rukuni na biyu suna ganin matsa lamba a wannan fuskar ɓata
lokaci ne da tsanani na ba gaira ba dalili.
* Yayin da rukuni na farko
ke ganin cewa fahimtar karatu da tarin ilimi na sauya tunani da halaye tare da
tasiri ga rayuwar mutum a jimlace, rukuni na biyu na ganin cewa karatu wani
shinge ne kawai na katange mutum daga shanawa da walwala.
Da sauransu, da sauransu.
Ko ma a wane rukuni ɗalibi
ya kasance, babban shawarar da zan iya ba shi, shi ne, duk yadda za a yi ya
kare dokokin da aka gindaya game da dukkannin abubuwan da suka shafi ɗalibtarsa
ta kowace fuska. Dokoki da ƙa'idojin
jarabawa na da babban gurbi a wannan bagire!
Ba abin mamaki ba ne a samu ɗalibai
da ke shafe dukkannin shekarunsu a jami'a ba tare da karanta abin da ake kira
"Students Handbook" ba. Za a yi mamaki idan aka ce ba abin mamaki ba
ne cewa waɗansu a tsawon shekarunsu na ɗalibtar
ba su ma san da wannan kundin dokoki ba, duk kuwa da suna da lokacin zaman hira
da abokai, da na kallace-kallace da musayar saƙonni
a kafafen sada zumunta da kuma lokaci na musamman na gulma da tsegumi da hanƙoro irin na waɗanda
ke “son kitson wance alhali ba
su da gashin wance.” Ko waɗanda ke karantawa, ba kowa ne ya san cewa karya doka
kowace iriya da ta kasance amintacciya ga muhallin da mutum ke wanzuwa na nuni
da raunin mutuntaka da dattijantakansa ba.
Ko babu waɗansu alƙaluma da suka tabbatar da haka, ina iya iƙirarin cewa ɗalibai
ɗaiɗaiku ne suka ɗauki rantsuwa da ake ba su a ranar “Rantsar da Sababbin
Ɗalibai” a matsayin wani abu mai muhimmanci ko tasiri. Ga da dama daga cikin ɗalibai
wannan rana ce ta cancarewa da ɗaukar hotuna... Wannan ya yi kama kai tsaye da
halayyar shuwagabanni da ke ɗaukar rantsuwa da ana iya kwatanta ta da mai bin
hayaƙi. A lokutan tsegumin ɗalibai, suna iya tattauna ire-iren rantsuwar da
shuwagabannin ke ɗauka tare da take su alƙawarurrukan ba kunya ba tsoron
Mahalicci, ba tare da su sun tuna nasu rantsuwa da suka ɗauka ba. Ko da yake,
shi ya sa Bahaushe ke cewa “laifi tudu ne...”
Abin da nake so ɗalibai su fahimta shi ne, duk yadda ake tunanin yanayi ya
lalace, akwai waɗanda ba sa fitar da rai – waɗanda sun ji sun gani cewa dole
sai sun tabbatar da gaskiya bakin rai bakin fama. Za mu iya cewa suna cikin
rukuni na farko. Sun san da cewa alƙawarin aikinsu ba mai bin shanun sarki ba
ne, face abin tambaya ne a gare su ranar gobe. Suna da ra’ayin cewa karya ƙa’idar
aiki cin amanar alƙawari ne. Sannan sun san da cewa “Sanya ido ga ɓarnar ɓata-gari,
mataki ne na naƙasawa da kassara ƙwazon mutane nagari.” Misali shi ne yadda
wanda ya sha wahalar karatu ka iya samun sakamako guda da mashiririta yayin da
aka yi riƙon sakainar kashi ga lamarin jarabawa!
Wani babban malamin falsafa ya ce: “Karatun babban mataki na waɗanda za su
iya ne, kuma suke da tabbacin za su iya ɗin.” Wanda ya yarda ya shiga
makaranta, to ya yarda da dokoki da ƙa’idojin da ke cikinta. Waɗannan dokoki
kuwa sun shafi ɗalibai da sauran ma’aikata baki ɗaya.
Babban rashin adalci ne da son kai da zon zuciya da rashin sanin ya-kamata
ga ɗalibi ya yi tunanin an zalunce shi yayin da doka ta yi aiki a kansa bayan
ya karya ƙa’ida bisa ganganci da ha’inci. Wanda ya goya masa baya kan wannan,
shi ne azzalumi ba wanda ya yi yunƙurin dakatar da ba daidai ba. A sauƙaƙe
yadda abin yake shi ne, idan aka kau da ido kan ɓata-gari:
* An karya alƙawarin aiki kai tsaye
* An ci amanar dokoki da ƙa’idojin aiki
* An ci amanar al’umma da ƙasa baki ɗaya yayin da ake gina gurɓatacciyar al’umma
mara bin ƙa’ida da sanin ya-kamata
* Ana rage ƙwarin guiwa ga masu hazaƙa
* Ana wofantar da ƙwazo da zaƙaƙuranci da jajircewa da riƙo da gaskiya
* Ana ƙoƙarin samar da al’umma mai rayuwa irin ta dabbobi da babu
ingantacciyar doka da oda
Da sauransu, da sauransu.
Yana da kyau mutum ya san ‘yancinsa sannan ya san ‘yancin waninsa. Yana da
kyau mutum ya san mene ne adalci, mene ne kuma zalunci, ya iya bambance adali
da azzalumi daga aikin adalci ko zaluncin da zai aiwatar bisa hujja ta ilimi na
hankalin tuwo da kuma musamman a fahimtar addinin gaskiya.
Ɗaya daga cikin hadisan da ake fara koyarwa a makarantun isalamiyoyi da dama
na ɗauke da bayanin cewa: “Gaskiya (halal) a bayyane take, ƙarya (haram) a
bayyane yake, duk da a tsakaninsu akwai abubuwa masu ruɗani...”
A bisa wannan, da sauran bayanai da ban zayyano ba nakan ce: “A riƙe
gaskiya da amana da zaƙaƙuranci da aikata daidai” yayin da duk aka tambaye ni SHAWARATA GA
ƊALIBAI.
Abu-Ubaida Sani
07/07/2023
2 Comments
Allah ya ba mu ikon yin riko da gaskiya. Allah kuma ya saka wa Malam da alheri. Ameen.
ReplyDeleteSani Adamu Faskari
Allah ya ba mu ikon yin aiki da gaskiya da rikon amana, muna godiya da irin wadannan shawarwari da ake ba mu.
ReplyDeleteENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.