Alibawa wani jinsin Fulani ne dake da asalin su a wani wuri dake cikin Jamhuriyar Nijar ta yau. Sun shigo yankin Masarautar /Daular Katsina a cikin ƙarni na 18 har ma suka zauni Dajin Rugu tare da Dabbobin su da iznin Sarakunan Katsina na wancan lokacin, daga bisani suka zo inda wasu itatuwa na Zurmawa /Zurmi kenan ta Jihar Zamfara ta yau. Suna a nan ne labarin bayyanar Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi ya riske su har ma suka yi masa mubayi'a a daidai inda garin Dauran ya ke a yanzu a ƙarƙashin jagorancin Shugabannin su, watau su Malam Abu Amil da Malam Muhammad Namoda da Aliyu Ɗanyab'i da Malam Mahmuda. Wasu daga cikin su ne suka bi Mujaddadi a lokacin Hijirar tsakanin Ɗegel da Gudu bayan fitowar su daga Gida kafin zaman su a Dajin Rugu. Waɗan ne suka samar da gidan Magajin garin Sakkwato na farko ta hannun Malam Abubakar Haruna Ɗanjada (zuriyar sa ce ke ci gaba da sarautar Magajin garin Sakkwato da Hakimcin Gundumar Gumbi a Jihar Sakkwato ya zuwa yau).
Sun samu Tutoci guda biyu na Jihadin jaddada addinin musulunci na Daular Usmaniya na cikin gida da ake kira Internal Flags a Turance waɗan da aka baiwa Malam Abu Amil da Malam Muhammad Namoda. Abu Amil ya zauna a Zurmi, Malam Namoda ya zo ya ƙirƙiri Ƙauran Namoda a shekarar 1807. Malam Ummaru Ɗanjeka ya zo daga Zurmi ya ƙirƙiri Moriki a cikin 1850s. Wannan jinsin Fulanin dai ne suka ƙirƙiri garuruwan Kware da Kuryad Dambo dake cikin Masarautar Shinkafi ta yau ta hannun Gatari da Ƙanensa Makauru. Daga jinsin su dai ne waɗan da suka fita daga Ƙungurki dake Ƙauran Namoda ta yanzu suka je yamma sai da suka zauni garin Shagari har ma suka zamo sarakan wurin, watau zuriyar su Marigayi Mai Girma Tsohon Shugaban Ƙasar Tarayyar Nijeriya, Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari GCFR, Turakin Sakkwato watau kenan akwai su a gundumar Yabo ta Jihar Sakkwato ta yau. A takaice abun da zan iya cewa kenan game da wannan tambaya, dafatar idan manyan masananmu suka leƙo zamu samu cikakken bayani.
Lambar Waya: 08149388452, 08027484815
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.