Ticker

6/recent/ticker-posts

ƘaiƘayin Zuci: Juyayi Da Nuna Tausayi A Cikin Wasu Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Cite this article as: Lawal, G. (2023). ƘaiƘayin Zuci: Juyayi Da Nuna Tausayi A Cikin Wasu Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture, (2)2, 210-213. www.doi.org/10.36349/tjllc.2023.v02i02.025.

NA

Garba LAWAL
Email: garbalawal195@gmail.com
08032787160/09137303797

Tsakure

Wannan takarda ta ƙunshi tsokaci ne ko bayani kan yadda Aminu Ladan Abubakar (ALA) ya sarrafa wasu zantuttuka masu jiɓi da sosuwar zuci a waoƙoƙinsa domin nuna tausayi da juyayin faruwar wasu abubuwa marasa daɗin ji, da suka faru ga wasu mutane. Wato dai duk batutuwan da hankalinsu yake bayyanawa a waƙoƙin suna da alaƙa da ban tausayi ko juyayi da alhinin faruwarsu. Ya sarrafa ire-iren waɗannan zantuttuka ne sakamakon yadda batututuwan suke sosa masa zuciya a duk lokacin da ya tuna da faruwarsu. Sa’annan kuma sukan sanya masa ɓacin rai da damuwa a duk lokacin da tuna da su Har wa yau kuma mawaƙin ya yi amfani da waɗannan zantuttuka ne a waƙoƙinsa domin nuna tausayi ga mutanen da ibtila’in ya faɗa musu

Fitilun Kalmomi: Waƙoƙi, Tausayi, Juyayi, Ƙaiƙayin Zuci

Gabatarwa

Waƙa zance ne mai tsari da yake tafiya cikin hikima da basira wanda wasu mutane masu fasaha da balaga da azanci suke aiwatarwa cikin sautin murya mai zaƙi da jan hankali. sa’annan kuma a isar da wasu muhimman saƙonni da za su amfanar da jama’a wajen ganin sun gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum. Wato dai mawaƙa wasu mutane ne da Allah (SWT) ya hore masu wata baiwa ta hikiimar iya sarrafa wasu zantuttuka ko kalmomi cikin waƙa da nufin faɗakarwa ko ilmantarwa ko wa’azantarwa ga jama’a. A fanen ilimi akan nazarci ire-iren waɗannan waƙoƙi ne domin a fito da wasu muhimman abubuwa masu amfani da ke iya taimakawa wajen inganta rayuwar al’umma. Mafiya yawa daga cikin mutane masu sauraron waƙa sun fi mayar da hankalinsu ne ga daɗin kiɗan da aka haɗa da waƙa ko kuma zaƙin muryar mawaƙi. Wato babu ruwansu da saƙonnin  dake ƙunshe a cikin waƙar. Saboda haka, manufar wannan takarda ita ce tsokaci kan wasu waƙoƙi da Aminu Ladan Abubakar (ALA) ya rera a inda ya sarrafa wasu zantuttuka masu jiɓi da sosuwar zuci masu nuna tausayi da juyayi kan abubuwan da suka faru ga wasu mutane. Mawaƙin ya yi amfani da zantuttuka da kalmomi mabambanta domin nuna damuwa da alhini da juyayi dangane da faruwar wasu abubuwan takaici da suka faru ga wasu mutane.

Taƙaitaccen Tarihin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Masana da manazarta irin su Imran (2008) da Umar (2011) da Hamza (2011) da Isa (2013) da Muhammad (2014) da Yakasai da Sani (2021) DA Sani & Suleiman (2022). duk sun yi tarayya a kan cewa an haifi Aminu Ladan Abubakar (ALA) a ranar Talata 2 ga watan 10 shekara ta 1973 cikin shekarar hijira ta 1394 a Unguwar Yakasai, Ƙaramar Hukumar Birni da kewayen Jihar Kano. Sai dai kuma an yaye shi a wata unguwa ta daban, wato a unguwar Ƙofar Wambai a hannun kakanninsa. Daga baya sai iyayensa suka yi ƙaura zuwa ƙaramar Hukumar Nasarawa inda suka zauna a unguwar Tudun Murtala.

Aminu Ladan Abubakar (ALA) ya fara karatu da koyon karatun addini a ƙarƙashin Malam Muhammad Sani wanda ake yi wa laƙabi da Malam Ɗan-Sakkwato wanda a wurinsa ne ya haddace izifi biyar daga cikin Alƙur’ani mai Girma. Baya ga nan kuma ya yi karatu a wata makarantar Islamiyya mai suna Zaharaddeeni Islamiyya ta Tudun Murtala ƙarƙashin kulawar Malam Usman Tudun Wada, inda ya fara tun daga rabin aji har zuwa aji shida, wanda daga baya kuma ya zama ɗaya daga cikin alaman makarantar.

Aminu Ladan Abubakar (ALA) ya fara karatun boko a wata makarantar Firamare mai suna Tudun Murtala Primary School, inda ya yi karatu a tsakanin shekarar 1980 zuwa 1986. Daga nan kuma sai ya halarci makarantar Sakandare ta Dakata Kawaji wato (Goɓernment Senior Secondary School, Dakata Kawaji), daga shekara ta 1986 zuwa 1992. Bayan ya kammala karatunsa na sakandire a shekara ta 1992, sai ya dakatar da ci gaba da karatun sakamakon matsaloli na rayuwar yau da kullum har tsawon shekaru goma sha biyu (12). Daga baya ya koma makarantar gaba da sakandare a shekara ta 2000 inda ya shiga makarantar fasaha ta Kano wato (School of Technology, Kano) inda ya yi karatu a fannin zane-zane wato (Department of Arts and Industrial Design) a wannan makaranta, ya samu shedar difiloma ta ƙasa a shekarar (2003).

Sosuwar Zuci Mai Nuna Tausayi

Zantuttuka ko kalmomi masu jiɓi da sosuwar zuci masu nuna tausayi kan zo ne sakamakon jin kai ko nuna damuwa game da faruwar wani abu maras kyau ga wani mutum ko wata al’umma. Mawaƙa kan yi amfani da ire-iren waɗannan zantuttuka ko kalmomi domin nuna tausayinsu ga wani abin takaici da ya faru ga wata al’umma ko wani mutum. Wato dai kamar yadda Aminu Abubakar (ALA) ya nuna tausayinsa ga al’ummar Arewacin Nijeriya dangane da rashin haziƙin shugaba kuma jagora wanda waɗansu marasa imani suka yi masa kisan gilla saboda ƙabilanci da ɓangaranci, kamar dai yadda mawaƙin yake bayyanawa a cikin waƙarsa inda yake cewa:

Jagora: Ya jama’ar Arewa!

Ga ta’aziyyar Sardauna,

Shi da firaministansa,

Abubakar da Sardauna,

Sun tafi ba magandansu,

Yanzu muna cikin ƙuna,

Ba makwafi na halinsu,

Ga shi Arewa sai kuka.

 

‘Y/Amshi: Gamji maza abin koyi,

Ahmadu Bello Sardauna,

In na tuno wafatinsa,

Sai ya saka ni in kuka,

 

Jagora:Ni abin da ka ban tausai,

Nai marinafin idanuna,

Ƙwalla na tuttuɗo guna,

Tay yo gare kumatuna,

Sardauna bai magaji ba,

Ko da ka ji da Sardauna,

Amma iyakaci su na.

(Waƙar Gamji Maza)

 

Waɗannan baituka da suka gabata daga wannan waƙa ƙunshe suke da zantuka masu jiɓi da sosuwar zuci masu nuna tausayawa da takaici da nuna damuwa na irin wannan babban rashin da mutanen Arewa suka yi. Mawaƙin ya nuna tausayawarsa na rashin magajin Sardauna a ɓangaren halin ƙwarai da jarunta, inda ya ce ko da ka ji ana kiran wani da Sardauna to iyakacinsa suna amma babu hali irin na Sardauna.

Har wa yau kuma mawaƙin ya ci gaba da sarrafa ire-iren waɗannan zantuttuka da kalmomi masu jiɓi da sosuwar zuci domin nuna tausayawarsa ga al’ummar Arewa, inda yake cewa:

Jagora:Daga kashe su Sardauna,

Anka yi decreen ƙarya,

Sun ka yi thirty four decree,

Dokoki na hamayya,

Anka rugurguje aikin,

Amadu babu alkunya,

Northern sation policy,

Anka baje su ba ƙarya.

‘Y/Amshi:

 

Jagora:An izini a ƙasar Hausa,

Hausa ta zam harshen aiki,

Daga kashe su Sardauna,

Anka baje wannan aiki,

Wani abu na ban haushi,

Sanda akai kisan haƙƙi,

Sai Ibo sun ka hau fati,

Sun kashe Gamji Hamshaƙi.

 

‘Y/Amshi:Hawayena suna ta zuba,

Ga juyayin gudun hijira.

 

Haƙiƙa duk waɗannan zantuttuka ne da ke nuna tausayi da juyayi na abubuwan da suka faru ga al’ummar Arewa na rashin gwarzon shugaba wanda kuma a dalilin hakan aka rugurguje duk wasu tsare-tsare na ci gaba da ya kawo wa al’ummar Arewacin Nijeriya. Saboda a dalilin rashinsa aka wargaje tsarin yin amfani da harshen Hausa a duk wata mu’amala da ta shafi harkokin gwamnati, wato dai wannan wata Hasara ce babba ga al’ummar Arewa na rashin yin amfani da harshen Hausa a harkokin gwamnati da ma sauran al’amura da suka shafi rayuwar yau da kullum. Saboda haka, lallai wannan abin tausayi ne da juyayi ga duk wata al’umma da ta tsinci kanta a irin wannan yanayi, ba ma al’ummar Arewacin Nijeriya kaɗai ba.

Sosuwar Zuci Domin Nuna Juyayi

Zantuttuka ko kalmomi masu nuna juyayi ko alhini kan samu ne sakamakon faruwar wasu lamurra marasa daɗin ji da suka faru a baya ga wasu mutane fitattu ko wata al’umma da sauran su. Akan nuna juyayi ko alhini ne ga wani lamari da ya faru wanda ka iya tayar da hankali ko kawo firgici ko sanya damuwa a zukatan al’umma. Aminu Ladan Abubakar (ALA) ya nuna juyayinsa da alhini ga al’ummar garin Maiduguri da maƙwabta, mawaƙin ya bayyana batutuwa da dama waɗanda ya ji ko ya gani da idonsa game da lamarin rikicin, wanda ya sanya wasu mazauna garin yin hijira domin tsira da rayukansu da dukiyoyinsu. Kamar dai yadda yake ambatawa a waƙarsa inda yake cewa:

Jagora:Ina zaune  na hangi mutum,

Da matatai suna ta bara,

Da hange nai alamu nai fa,

Babu kama da masu bara,

Da ‘yan ‘ya’ya maza, mata,

A gunsu da dama masu jira,

Alamomi na mai gajiya,

A tare da su suna ta bara,

Da sun ka iso gare ni,

Na tambaye shi ya ce “gudun hijira.”

 

Amshi:Hawayena suna ta zuba,

Ga juyayin gudun hijira.

 

Jagora:Ya ce mani “By Profession,”

A aiki na fi fo hijira,

Ya ce mani “malami ne ni,

Na koyarwa a gwanin fiira,

Ya ce mani ga iyalaina,

Waɗanda da su mukai hijira,

Amaryata da yaranta,

Babu amonsu ko nai kira,

Suna mace, ko suna raye,

Allah masani Sarkin ƙudura

 

Duk waɗannan baituka da suka gabata na daga ƙunshe suke da zantuttuka ko bayanai masu jiɓi da sosuwar zuci masu nuna juyayi da alhini ga wani bawan Allah da ya tsinci kansa daga cikin masu gudun hijira a sanadiyyar yaƙe-yaƙen boko haram da ya faru a garin Maiduguri.

Mawaƙin ya nuna juyayi da alhininsa game da yadda wasu suka yi gudun hijira daga garin Maiduguri zuwa ƙasashen maƙwabta domin samun tserewa. Wato dai yadda yake nuna tausayi da juyayi ko alhini ga mutanen da abin ya shafa, musamman ga waɗanda suka yi gudun hijira suka baro gidajensu da dukiyoyinsu da iyalansu da sauran ‘yan uwa. Wasu kuma suka baro sana’o’insu suka koma mabarata sakamakon gudun hijira a sanadiyyar rashin kwanciyar hankali da ke faruwa a garuruwansu. Haƙiƙa duk waɗannan batutuwa da mawaƙin ya zayyano a waƙar, abubuwa ne na ban tausayi da sanya juyayi ko alhini ga duk wanda hakan ta faru gare shi. Aminu Ladan Abubakar (ALA) ya ci gaba da nuna alhininsa da juyayi ko tausayawa ga wani magidanci da ya tsinci kansa a cikin masu gudun hijira kamar dai yadda yake cewa:

Jagora:Ya ce mani kalli ‘ya’yana,

Ƙanana ne mukai hijira,

Manya a cikinsu mata ne,

Na bar su gida na zo ni bara,

Idan da akwai sukuni,

In yi gadi sai na ɗau ƙadara,

Wurinmu abin mu kai baki,

Mu bauta ciraku mai ƙuduri,

Ko ɗan aiki, ko ko aike,

Ko dai masinja mai shara.

 

Jagora:Nan take jiki ya ɗau rawa,

Na kasa tsayi na kasa zama

Cikin sa’a a motata,

Ina da tufa ta alfarma,

Na ba su tufa, na ba su kuɗi,

Ya karɓa kau yana kyarma,

Ya sake fasa mani kuka,

Na jin daɗi da alfarma,

Na rarrashe su, sunka tafi

Na kasa tsayi, na kasa zama (Waƙar Juyayi).

 

Tabbas waɗannan baituka da suka gabata ƙunshe suke da zantuttuka masu jiɓi da sosuwar zuci, waɗanda ke nuna tausayi da alhini. Aminu Ladan Abubakar (ALA) ya bayyana yadda zantawarsu ta kasance a tsakaninsa da wani bawan Allah wanda ya tsinci kansa a yanayin gudun hijira. Mawaƙin ya nuna kaɗuwarsa matuƙa na ganin yadda wannan bawan Allah da iyalansa, ga ‘yan yara ƙanana a cikin yanayi na ƙasƙanci, tare da yawon bara domin samun abin da za su sanya a bakin salati. Sa’annan kuma akwai ‘ya’yansa mata manya wanda bai san halin da suke ciki ba. Shi dai buƙatarsa ya samu wani aikin yi kamar gadi ko masinja ko share-share ko ɗan aike da sauransu. Duk da cewa mutumin babban malami ne a garinsu amma a sanadiyyar gudun hijira ya zama ƙasƙantacce. Waɗannan batutuwa sun tayar da hankalin mawaƙin matuƙa da har ta kai ga na sosa masa zuciya, musamman ma a duk lokacin da ya tuna da abin a cikin ransa.

Haƙiƙa waɗannan abubuwan da mawaƙin ya bayyanaw a waƙarsa, wasu batutuwa ne da suke nuna tausayi ko juyayi ga bayin Allah da suka tsinci kansu a yanayi na gudun hijira. musamman ma ga wannan bawan Allah da mawaƙin ya samu zantawa da shi a yanayi na ƙasƙanci sanadiyyar gudun hijira da ya tsinci kansa a ciki.

Kammalawa

An nazarci waɗannan waƙoƙi ne domin yin tsokaci game da yadda Aminu Ladan Abubakar (ALA) ya sarrafa wasu zantuka ko kalmomi masu jiɓi da sosuwar zuci a waƙoƙinsa. Mawaƙin ya sarrafa ire-iren waɗannan zantuttuka da kalmomi domin nuna tausayi da juyayi na wasu abubuwa marasa daɗin ji da takaici da suka faru ga al’umma mazauna rewacin Nijeriya. Sai kuma yadda ya nuna yadda wasu bayin Allah suka tsinci kansu a yanayi na gudun hijira. Haƙiƙa mawaƙin ya yi amfani da fasaharsa ta waƙa wajen nuna tausayi da alhini ga waɗannan lamura da suka faru. Saboda haka, ya yi amfani da wannan hanya wajen bayyana abubuwan da suka sosa masa rai game da al’ummar Arewa wato dai ya bayyana abubuwan da suke cikin zuciyarsa da nufin zaburar da al’ummar arewacin Nijeriya da su farka daga barci domin kare mutunci da ‘yancin Arewa tare da ƙoƙarin zaburar da manyan yankin Arewa wajen farfaɗo da martaba da mutuncin Arewa. Wato dai waƙoƙi ne da aka rera domin nuna juyayi da alhini tare da tausayin yadda wasu abubuwa marasa kyau suka faru ga wasu mutane da al’ummar wani yanki.

Manazarta

1.       Barista, M.L. (2011). Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar ALA. Kano: Iya Ruwa Publishers.

2.       Bashir, R. (2021). Hotoncin Zuci A Waƙoƙin Baka Na Hausa: Tsokaci A Kan Wasu Waƙoƙin Maza Da Na Fada. Kundin Digiri Na Uku. Sashen Harsuna da Al’adun Afirka. Zariya: Jami’ar Ahmadu Bello.

3.       Daniel, G. (1995). Emotion Intelligence. London: Bantom Books.

4.       Gusau, S.M. (2008). Waƙoƙin Baka A Ƙasar Hausa: Yanaye-Yanayensu Da Sigoginsu. Kano: Benchmark Publishers Limited.

5.       Izard, C.E. (1977). Human Emotion. New York: Plenum.

6.       Lawal, G. (2022). Sosuwar Zuci A Waƙoƙin Hausa Na Zamani: Nazari A Wasu Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kundin Digiri Na Uku. Sashen Harsuna da Al’adun Afirka. Zariya: Jami’ar Ahmadu Bello.

7.       Sani, A-U. & Suleiman, M. (2022). Tsattsafin Haliya: Wani Ɗigo Cikin Tafashen Aminu Ladan Abubakar (ALA). In South Asian Research Journal of Arts, Language and Literature, Vol. 4, Issue 2, Pp 77-77. DOI:  www.doi.org/10.36346/sarjall.2022.v04i02.005.

8.       Satatima, G.I. (2009). Waƙoƙin Ɗarsashin Zuciya Na Makaɗan Husa. Kundin Digiri na Uku. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya da Kimiyyar Harshe. Kano: Jami’ar Bayero.

9.       Yakasai, S.A. da Sani, A. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Amal Printing Press.

10.    Yusuf, B. (2017). Zuciya A Tunanin Bahaushe: Nazari Daga Waƙar Baka. Kundin Digirin Farko, Sashen Harsuna Da Al’adun Afirka. Zariya: Jami’ar Ahmadu Bello. 

Post a Comment

0 Comments