Ticker

6/recent/ticker-posts

8.6 Wandara A Sha Maganin Ƙaba - Daga Littafin WASANNI A ƘASAR HAUSA (Page - 414)

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.

8.6 Wandara A Sha Maganin Ƙaba 

Wannan wasa ne na manya da ke cikin jerin wasannin tashe. Yawanci akan gudanar da shi da dare bayan an sha ruwa. Sannan akan bi wuraren da mutane ke taruwa ne domin gabatar da wasan. Adadin masu gudanarwa sakan kai mutane uku zuwa sama da haka. Sannan yana buƙatar kayan aiki.

8.6.1 Kayan Aiki

i. Igiya

ii. Butar duma ko wani abu da za a yi amfani da shi maimakon wannan

iii. Babbar riga/malum-malum

iv. Sanda

v. Hula da rawani

8.6.2 Yadda Ake Wasa

Ɗaya daga cikin masu wasa zai sanya babbar riga da hula da rawani, sannan ya riƙe sandar dogarawa. Wanda ya yi wannan shiga akan kira shi ‘baba.’ Za kuma a samu gorar duma a ɗaure saman da igiya, a rataya masa a wuya. Gorar dumar za ta kasance ta cikin babbar rigarsa. Za a sanya igiyarta mai ɗan tsayi yadda gorar za ta kasance daidai kunkuminsa na gaba. Da ka kale shi, za ka ga gorar duman ta ɗago babbar rigar da ya sanya daga ciki. Wato ana ganin tulu da ta yi.

Yayin da aka je wurin wasa, baba zai riƙa tafiya yana buga gorar dumar da guiwowinsa. Wannan zai sa ta riƙa yawo zuwa gefe da gefe. Ga masu wasa, wai hakan duk ƙaba ce. Baba zai fara ba da waƙa, saura kuwa suna amsawa. Ga yadda waƙar take:

Baba: Tumbulum-bulum,

Amshi: Wandara a Sha Maganin ƙaba.

 

Baba: Na yi na gaji,

Amshi: Wandara a Sha Maganin ƙaba.

 

Baba: Asibiti goma sha bakwai,

Amshi: Wandara a Sha Maganin ƙaba.

 

Baba: To za ta kai ni ƙas,

Amshi: A’a ba za ta kai ka can ƙas ba.

 

Baba: To ni za ta kai ni ƙas,

Amshi: A’a ba za ta kai ka can ƙas ba.

 

Baba: Ni za ta ka da ni,

Amshi: A’a ba za ta kai ka can ƙas ba.

 

Baba: To ai za ta ka da ni,

Amshi: A’a ba za ta kai ka can ƙas ba.

8.6.3 Tsokaci

Wannan wasa yana samar da nishaɗi musamman ga masu kallo. Yana kuma nuna hoton wani yanayi da ɗa namiji ke shiga yayin da irin wannan lalura ta same shi, wato ƙaba.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Post a Comment

0 Comments