Ticker

6/recent/ticker-posts

8.3.1 Zakkar Gida - Daga Littafin WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA (Page - 152)

Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.

8.3.1 Zakkar Gida

Hannunta ba shi tashi ga daka,

Ga cin tuwo yaka tashi.

 

Tasa uku hitarta faɗuwarta,

Ɗauki mai laƙaƙƙe-laƙaƙƙe.

 

Mai laƙaƙƙen hannu,

Da ba shi tashi ga daka,

Ga cin tuwo yaka tashi.

 

Malmala taka loma da ita,

Gidauniya kurɓi ukku takai mata.

 

Ban kula ba, ban sa kai ba,

Ban kula ba da marin ƙato,

Balle na ɗan jariri.

 

Ɗauki-ɗauki in tanye ki,

In ba ki so in ɗebo.

 

Zama daka tanyo ne,

Ido ka tsoron aiki,

Hannu na faɗin a kawo mu gani.

 

Maccen kurku maccen banza,

Maccen da ba ta wa namiji isa.

 

Idan aka lura da waƙar da ke sama, za a ga bambanci tsakanin adadin ɗangwaye da ke cikin ɗiyoyin waƙar.

WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Post a Comment

0 Comments