Ticker

6/recent/ticker-posts

Danlele

6.39 Ɗanlele

Wannan wasa ne na yara mata. Yana ɗaya daga cikin wasannin da ke ƙarƙashin rukunin tashe. Saboda haka, an fi yin sa da dare, kuma cikin watan azumin Ramalana. Kimanin yara shida zuwa sama ne suke gudanar da wannan wasa.

6.39.1 Kayan Aiki

i. Kwanukan abinci

ii. Kayan maza irin su malum-malum da hula da makamantansu

iii. Tabarma

6.39.2 Yadda Ake Wasa

Yara sukan zaɓi ɗaya daga cikinsu, wadda ta kasance tana da wayo sosai. Sai su yi mata shigar maza tsaf. Ita ce za ta kasance ɗan gata. Wato dai za ta kasance tamkar mai gida. Daga nan za a ɗebi kwanukan abinci da kuma tabarma.

Da zarar kayan aiki sun samu, sai yara su ɗunguma zuwa wurin tashe. Za su riƙa shiga gida-gida. Duk gidan da suka shiga, za su baje tabarma. Ɗanlele zai hau bisa tabarmar ya harɗe, tamkar maigidan da aka ɓata wa rai.

Ɗaya daga cikin yaran kuwa za ta kasance matar Ɗangata. Za ta zo da kwanukan abinci daban-daban. Daga nan za ta fara waƙa tare da miƙo masa kwanukan abincin ɗaya bayan ɗaya. Shi kuwa zai riƙa nuna ba zai ci abincin ba. Sauran masu tashe za su riƙa amsa mata waƙar. Haka za su yi ta yi, har sai an ba su abin sawa a baka ko kuma an sallame su.

6.39.3 Waƙar Wasa

Bayarwa: Ka ga ruwa nan ka sha,

Amshi: Gajere.

 

Bayarwa: Ka ga ga fura nan ka sha,

Amshi: Gajere.

 

Bayarwa: Ka ga ga kunu nan ka sha,

Amshi: Gajere.

 

Bayarwa: Ka ga ga fate nan ka ci,

Amshi: Gajere.

 

Bayarwa: Ka ga ga tuwo nan ka ci,

Amshi: Gajere.

 

Bayarwa: Ɗanlele mijina,

Amshi: Gajere.

 

Bayarwa: In ko ba ka so ka faɗa mini,

Amshi: Gajere.

 

Bayarwa: Gobe gidanmu za ni da safe.

Amshi: Gajere.

6.39.4 Tsokaci

Wannan wasa yana nishaɗantar da masu kallonsa. Sannan yana nuna dabarun matan gida na shawokan mazajensu yayin da suka ɓata musu rai. Baya ga haka, wasan hanya ce ta samun abin masarufi ga masu gudanarwa.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments