Ticker

6/recent/ticker-posts

5.8 Matsayin Almajirai Ga Sauran Jama’a.

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

5.8 Matsayin Almajirai Ga Sauran Jama’a.

Waƙoƙin da ake amfani da su wajen bara na baka suna bayyanar da matsayin almajirai da sauran mabarata ga jama’a. Kamar yadda aka ambata can baya a babi na uku cewa wasu mutane suna ganin bara yana da wata daraja wadda har idan mai neman ilmin addini bai yi shi ba to karatunsa ba zai yi albarka ba. Wannan tunani ya sa ake dubin almajiri da daraja a al’adance kuma ya sa masu bara ke ambaton haka a cikin waƙoƙinsu na bara. Kodayake Khalid (2006) da Jibril (2010) suna ganin yara waɗanda iyayensu ke aika su birane wajen almajirci yara ne masu ‘yar daraja a idon jama’a, kasancewar iyayensu talakawa ne, kamar yadda shike a matakin ƙasa na tsanin tattalin arziki. Shi almajirin bai ɗauki kansa koma-baya ba, shi a ganinsa har ma yana da wata darajar da kowa ke son ya samu. Ga misalin haka a waƙar “Da Bara Da Bara Ɗan Malam” mai cewa:

Almajiri tsuntsu ne,

Da ya ji motsin tsaba,

Sai ya yi firingi da kunne,

Kama da mataccen kusu,

Amma ba kusu ne ba,

Mutum ne ɗan aljanna.

(Almajiri tsuntsu ne)

Ɗiyan waƙar da suka gabata suna faɗi tare da nuna Amajiri mutum ne mai tsananin bukata musamman ta abinci, saboda tsananin bukatarsa ne ya sa ko da motsin tsaba ya ji sai duk hankalinsa ya koma can wajen da ya ji motsin saboda tsananin bukatarsa ga abinci. Sai ya ci gaba da nuna cewa wannan halin tsanani da yake ciki bai mayar da shi koma bayan al’umma ba, shi ma mutum ne kamar sauran jama’a. Ba ma mutum kawai ba, a’a mutum ne mafifi ci a cikin alumma domin ɗan Aljanna ne shi kamar yadda layi na ƙarshe na ɗan waƙar da ya gabata ke ambatawa. Wannan yana nuna yadda mabarata da wasu daga cikin al’umma ke dubin rayuwar bara. Wato duk yadda aka ga mai bara a cikin wahala da wulakanci to ba haka yake ba, shi mutum ne mai daraja a wajen Allah wanda sakamakonsa gidan Aljanna idan aka je Lahira. Wannan ita ce falsafar da ke cikin waɗɗannan ɗiya da suka gabata, masu nuna rayuwar bara rayuwa ce ta bautar ubangiji mai babban sakamako a Lahira. Ƙila wannan tunani ya samo asali ne daga ayoyin Ƙur’ani masu nuna sakamakon wanda ya jure wa wahalar da ya sami kansa a ciki (2:155). A wannan waƙar ake iya fahimtar matsayin mabarata ƙarara ta yadda za a iya gane yadda suke ba yadda ake ɗaukarsu ba.


Post a Comment

0 Comments