Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa. Ahmadu Bello University Press Limited.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
5.6.1 Laƙad raliyal Lahu
Jagora: Laƙada raliyallahu anal muminina.
Amshi: To.
Jagora: Angal lahu angaruhin mu’asha.
Amshi: To.
Jagora: An aiko mu inda malam mu
gan shi.
Amshi: To.
Jagora: Ga shi biki gare shi mi
zamu ba shi.
Amshi: To.
Jagora: Kai ka mukai mu samu lada cikakka.
Amshi: To.
(Laƙada Raliyallahu)
A cikin wannan
waƙa akwai wata jumla a ɗa na byu mai cewa “Angal lahu angaruhin mu’asha”.
Wannan ɗan waƙa ba ya da wata ma’ana, amma idan mai sauraro ba mai ilmi
ba ne sai ya ji kamar wata aya ce ake karantowa. Wannan wani surkulle ne da
mabarata ke amfani da shi a cikin waƙoƙinsu domin su nuna wa mai sauraro kamar su masu ilmi ne
suna cirato ayoyi suna sakawa a cikin waƙensu.
Haka ma “Lanzika inna Lanzika” a cikin waƙar “mata dangin Fatsima” shi ma surkulle ne mai kama da ana karanto wani
abu mai wata ma’ana da ta danganci karatu na addini kamar dai yadda wani mutum
kan ce “Waman takanahu illa awaya”.
Da sauransu.
0 Comments
Post your comment or ask a question.